SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Saida Sukai Tafiya Mai Tsayi Sannan Suka K’arasawa Wajan, Koda Sukaje sun Tadda Mutane Sosai a Wajan, Sauke Sulthanan Ameenatu Tai Mama Ta Rungumeta a jikinta ita Kuma ta k’utsa Cikin Mutanen
“Dan Allah Ku Taimaka, Yarinya ce Bata Numfashi ina Likitan”
Mutanen da Suk’a bi Layi Kowa Ya Tsaya Suka Shiga da Ita Cikin Dakin Maganin, Kwantar da ita akai a irin Gadon Marasa Lapaia dake Dakin, mutumin Ya dauko Sthethoscope Yasa a K’irjinta Cikeda Fargaba, jin Zuciyarta Na Harbawa Yasa Ya Sauk’e ajiyan Zuciya. Ameenatu daketa K’allanshi Hankali Tashe Tace
“Likita ta mutu koh?”
Kai Ya Girgixa mata Sannan Yace
“Bata Mutu bah tanada rai, Anma maiya Sameta”
Itama Ajiyan Zuciyan tai Tana K’allan Sulthanan
“Ruwa neh ya mata duka dazu shine ta dawo gida tana numfashi Sama Sama”

Baice Komai bah Sai Gani datai ya Hado wasu Allurai Guda Biyu Ya mata Sannan Ya Dauko wani ya mata a Hannu. Ganin Abubuwan Dayake Yasa Ameenatu Tai Saurin Cewa
“Likita Wallahi Bamuda kudi Dari biyar ce a Hannun mu ka taba magani K’awai”
Juyowa yayi ya K’alleta tareda Murmushi
“Karki damu, ni Likita ne nazo Kauyen nan dan Taimaka ma Alumma kuma Kyauta nakeyi”
Murmushi ne Ya subuce mata har saida Fararen Haqoranta Suka Baiyana. Cigaba Yayi da Abinda Yakeyi Har drip yasa mata Sannan Ya maida dubanshi da Mama Dak’e Tsaye
“Mama Samu Guri ki Zauna Dan Bah Yanzu Zaku tafi bah Har sai Ruwan dana Sah mata ya K’are Sannan kuma ta Farfado”

Wuri yaba Mama Ta zauna tana mai Godiya, Baice komai bah Sai Murmushin dayakeyi. Ameenatu ta matso inda Mama take Zaune Ta sadda kai Kasa tana cewa
“Mama ki koma gida, Banasan Abinda zaije ya dawo, karki Damu Insha Allahu komai zai daidaita. Kada Baffa ya fito bakya nan”
Tho Mama tace Tareda Mik’ewa tai Musu Sallama Ta Wuce Gida. Har Likitan ya Gama Bah duban Mutanen Dake waje Magani Anma Sulthana Bata Farka bah, Dak’in ya Shigo Tareda Cire Lapcoat din dake Jikinshi. K’allanshi Ameenatu tai
“Likita Har yanzu bata Farka bah”
Juyowa yayi ya K’alleta Yana Y’ar Murmushi
“Karki damu Zata Farko koda xuwa Safe neh”

Ameenatu Batace Komai bah ta Maida Dubanta ga Sulthana Dak’e Kwance.
Wayoyinshi Dake kan Table ya dauka Tareda Briefcase dinshi Sannan Yace
“Yan Mata Zan Tafi Masaukina”
Key din Chemist din ya Mik’a Mata Yana cewa
“Nasan Sai nah dawo ruwan zai k’are dan Haka Ga Key ki rufe Kofan Karki bude har sai idan nine nace miki nazo”
Hannu bibiyu ta Amsa tamai Godiya, Torchlight ya Mik’a mata Sannan ya Fita Ita kuma ta Tashi ta Rufe Kofan Ta dawo ta zauna…

Bacci ne Ya kwasheta a Wajan bata farka bah Saida Dataji Ana Kiran Sallan Asubah, Mik’ewa tai dasauri Sai a Sannan ta tuna Bah Gida tak’e bah, Sulthana ta k’alla taga ta juya Kwanciya. Murmushi tai ta tabata
“Alhamdulillahi, Allah Ya baki lapia”
Dube dube ta soma yi koh zata samu ruwan Alwala, Anma bata samu bah. Haka ta zauna har Gari yayi Haske Tangaran har ta soma jin hayaniyar mutane Bakin Shagon Alamar Magani sukazo Amsa, Jin Ana dukar kofan Yasa Tace
“Waye”
Muryan Likitan Ta jiyo yana cewa
“Bude Nine”
Bah Musu ta Bude kofan Ya Shigo Yana K’allan Sulthana. Gaidashi Ameenatu tai Ya Amsa Da Y’ar Murmushi a Fuskarshi
“Ya Jikinta”
Dasauki Ameenatu Tace K’anta a K’asa, Karasawa yayi inda Sulthanan keh Kwance Ya soma Dubata, A Hankali ta bude ido ta daura su akan Kyakyawan Saurayin Dake Tsaye a Kanta
Mik’ewa Tai dasauri tana K’allanshi Shima ita Yak’e Kallo. Kauda kai tai tareda Bin dakin da K’allo, Ameenatu ta Gani zaune tana K’allanta ta mik’e Tana kokarin Sauka daga Gadon, Saurin Rikota Ameenatu tai tana cewa
“Ina zaki bayan Bakida Lapia”
Sai a sannan Taji zafi a Hannunta, Duba Takai Wajan tana Hannunta da Allura Ruwa na Bi. Tabe Baki tai Ta zauna Tana Yatsine Fuska. Tunda Ta bude ido bah Abinda Likitan nan keyi sai K’allanta Kamar zai Cinyeta. Ganin Irin Kallan Da yak’ema Sulthana Yasa Ran Ameenatu ya baci Zuciyarta Tahau Mata zafi…

Tho! Kunjimin Wannan Ameenatun, Tho me Take Nufi

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 61 to 65*

         Gareki *Hafsat Hassan* Sakonki ya Iso Gareni, ina Godiya da Soyaiyyarki Gareni. Wannan Shafin Naki neh..

Ganin irin K’allan da Yakema Sulthana Yasa Ran Ameenatu ya baci Zuciyarta tahau mata zafi, Kauda kai tai Tareda Jan Guntun Tsaki.
“Likita Yaushe Ruwan zai K’arene Inaso mutafi Gida”
Sai a Sannan Yadawo daga Duniyar Tunani ya K’alli Ameenatu yana cewa
“Nan da Y’an mintina, ai ya kusa Karewa”
Batace komai bah Ta juya fuska tana k’allan wani wajan..

Sulthana ya K’alla yana mata Murmushi
“Ya jikin naki”
Turo baki tai ta kauda kai gefe
“Ni Bah abinda ke damuna”
Murmushi Yayi yabar wajan ya koma inda Jama’a ke tsaitsaye Suna jiranshi. Sai a Sannan Ameenatu tace
“Sulthana ya Jikin”
Murmushi tai Kanta a kasa
“Dasauki”
Shiru neh yabiyo baya Har na Wasu yan Mintina, Ganin Ruwan ya k’are Yasa Ameenatu ta mik’e taje ta Gayama Likitan Fuska bah Walwala, dakanshi yazo ya Cire mats tareda Hada mata magunguna Suka amsa Tareda mai godiya…

Har zasu fita Yadan Sosa Sumar Kanshi Yana Cewa
“Ummm ji mana”
Ameenatu ta Tsaya batareda ta Juyo bah, Karasawa Yayi inda Tak’e tsaye yace
“Gashi zaku tafi bansan Sunayenku bah, n Inason idan bah damuwa mu K’ulla zumunci da Ku”
Murmushi Ameenatu har Fararen Hakoranta Suka baiyana
“Bah Damuwa Sunana Ameena, Ita kuma Sunanta Sulthana kuma muna Unguwar Taro tari gidan Mallan Jamilu mai Almajirai
Sunan Ya maimaita a Hankali tareda Lumshe ido Sannan Yace
“Ni kuma Sunana Dr Fareed, ni dan Cikin Garin Kano neh”
Murmushi Ameenatu tai
“Mun gode Sosai Dr Allah ya saka da Alheri”
Kai Ya daga mata Yana K’allanta har tah fita daga shagon, Already dama Sulthana ta fita..

A Gida Kuwa, da Asubahi Kiran Sallan Farko Baffa ya fito ya Nufi Zaure dan Tada Sulthana kamar Yanda ya saba, Ganin Bata nan Yasa ya Dawo ya buga Dakin Mama, Budewa tai tana Bata Fuska
“Dama na Fada miki, Yanzu je ki gani da Idonki Yarinyan nan Ashe ba’a gida take Kwana yawon karuwancinta take tafiya sai asubah tayi take dawowa. Tho yanzu dai gashi yanzu tah Makara”
Tabe Baki Mama tai Tareda Kauda kai
“Tho indai Sulthana bata gidan nan tah Tafi Yawon karuwancin neh kamar yanda ka fada tho tareda Y’arka Suka Tafi”
Da Mamaki Ya K’alli Mama rai bace
“Ni kike Gayama Wannan Maganan, Yanzu na K’ara tabbatar da bakida Hankali da Tarbiya Saratu. Da bakinki Kike ai banta Y’arki”
Guntun Tsaki Mama tai dan Baffa ya mugun Kaita Mak’ura Yau

“Aibanta Y’a ai a wurinka na koya, Sannan Maganan Tarbiya Rainonka neh. Idan kuma baka Yarda bah sai kaje ka duba ka gani”
Bata jira mai zaice bah ta rufe kofan dakinta Bam!
Jiki na Rawa Baffa ya nufi dakinsu Ameenatu yana Duka, Hafsatu dake Barci ta Mik’e xaune Cikeda Masifa
“Wai Wayene”
A Harzuk’e Baffa Yace
“Budemin Kofa”
Jin muyan Baffa Yasa ta Bude dasauri ta fito, Ido yasa yana jiran Fitowa Ameenatu jin Shiru Yasa ya K’walla mata k’ira
“Keh Ameeenatu bazaki Fito bah”
Hafsatu tace
“Ai ba’a dakin tah kwana bah”
A rude Baffa Yace
“Ina Taje?”

Girgiza Kai Hafsatu tai tana cewa
“Bansan inda taje bah, bata dai kwana dakin bah”
Tamkar Mahaukaci Baffa ya koma a cikin gidan, Bai damu da Sulthana bah Burinshi Kawai Yaga Ameenatu, Fita Yayi ya nufi masallaci. Yana dawowa ya soma Kwallama Mama kira..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button