SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fitowa tai daga daki tana cewa
“Lapia kira da Sassafen nan”
Huci yake kaman Zaki Yana k’allanta
“Ina Kika kai min Y’a tah”
Mama ta tabe baki tace
“Ina Kuwa zan Kaita nifah Rabona da ita tun jiya da Daddare”
Cikeda masifa Yace
“Idan bakisan inda taje bah ya akai kikasan bata gidan”
Sai a sannan Mama ta K’alleshi itama rai Bace
“Mallan kullum magana tah daya ce gareka ka rinka jin tsoron Allah, Duka yaran nan Y’ayanka neh. Ka daina nuna banbanci, ni tunda nake ban taba ganin Irin Wannan Abin naka bah, Haba M…”

Saurin Katseta Yayi da Cewa
“Bah Wannan Na tambayeki bah maganan Y’ata make miki”
Murnushin Takaici Mama tai
“Ameenatu takai Sulthana Chemist jiya da Daddare rai a Hannun Allah, A Chan suka kwana”
Zaro ido Mallan Yayi Yana K’allan Mama
“Da Izini Wah?”
Bata bashi amsa bah Tabar Wajan ta shiga Kicin Abinta..

Basu suka K’araso gida bah Sai Wuraren K’arfe Tara da Rabi, Da Sallama suka Shigo cikin Gidan, Baffa suka Samu zaune a bakin Kofar dakinshi da Alamar su Yake jira dan yana ganinsu ya mik’e dasauri. Ameenatu ya Kalla yana cewa
“Daga ina kike”
Cikeda tsoro tace
“Daga Chemist muke nakai Sulthana neh”
Da Izinin Wah?” cewar Baffa

Dan Dagowa Ameenatu tai ta Kalleshi sannan ta duk’ar dakai
“Bah Kowa, Anma Baffa gani nai tana cikin Wani Hali datake Bukatar Taimako”
Nuna Ameenatu Baffa yayi da Yatsa
“Idan Na K’ara gani ko naji makamancin Haka a gidan nan Wallahi saina mugun Saba miki, ki rubuta ki ajiye”
Bai jira mai zatace bah Ya fice daga gidan.. Jin ya Fita Yasa Mama ta Leko Suka shiga Dakinta, Abin karyawa ta Basu Suka ci Sannan Taba Sulthana Magani. Dakinsu Ameenatu ta Koma ta kwanta dan tadan K’ara Kwanciya, Lumshe ido tai ta Bude Dasauri a Fili tace
“Dr Fareed mai yasa kakemin Gizo a Idona, Mai yasa nake tunaninka tun Sanda muka Rabu”

Niko Ummy Abduol nace ki jira Readers su baki amsa nidai baza’aji mutuwar sarki a bakina bah…

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 66 to 70*

   Dedicated dis page to *Summayya Danfulotie* Sakonki Ya iso Gareni, Nagoda da Addu'a Allah yabar K'auna.. da Kuma Sahiba *Aysha Zagi* I beg make uh no hug transformer uh knw I lurv uh..

Kwance Yake kan katafaren gadonshi Yana Latse latse a Waya, Bude kofan Dakin Akai koba’a fada mishi bah yasa Yasir neh dan Shi kadai ke shigo mai daki bah Tareda izini bah. Kan gadon Yasir ya zauna yana k’allan Masroor da yayi kamar bai Ganshi bah
“Morning Shagwababbe”
Hade rai Masroor yayi yana cigaba da abinda Yakeyi, fuzge Wayan Yasir yayi a aje a Bedside din dake kusa dashi
“Ina ma magana kayi banxa dani”
Tsaki Masroor Yayi tareda Mik’ewa Yana cewa
“Yasir Wallahi ka kiyayeni da kirana da Wannan Sunan”

Dariya Yasir yayi harda Rik’e ciki
“Kaga Yanda kake da baki kamar wani k’aramin Yaro”
Tsaki Masroor yayi ya kauda kai
“Pls banasan Damuwa Yasir meh kuma ya kawoka”
Tsagaitawa da Dariyan yayi Yana cewa
“Dan Allah d’an Rakani zakai”
Zaro ido Masroor yana K’allan Yasir
“Tab! Allah ya kiyaye na K’ara raka kah, Jiya da naraka kah ka Kaini kauye.”
Dariya Yasir ya K’ara Fashewa dashi
“Kuma kaman Kasani Wallahi Chan nakeso muje cox Inasan nasamu wasu informations ne wajan Mallan din nan, Pls Frend”
Shiru Masroor yayi yana Yatsine Fuska
“Shiknan bah Damuwa anjima sai muje”

Murmushi Yasir Yayi
“Dats y I lv uh Friend”
Shima murmushin yayi dai dai nan aka turo kofar dakin, daga kai Masroor yayi yana k’allan kofan. Ganin Mahnoor ce yasa ya rike Kugu Yana K’allanta
“Any problem”
Itama K’ugun ta rike tana Y’ar dariya tace
“Any problem”
Kanta yayo rai bace dan ya Tsani yayi abu a kwaikwayeshi, dasauri ta ruga bayan Yasir ta Labbe tana cewa
“Pls Bro Yasir karka bari ya dakeni”
K’areta Yasir yayi yana k’aftama Masroor ido
“Meye Haka kaifa kanada Matsala”
Kwafa Masroor Yayi har zai juya ya hango tana mai dariya, Duka yakai mata ta goce sai a Fuskan Yasir. Dafe wurin yayi yana K’allan Masroor
“Nagode Dukan naka ya rasa inda zai tsaya sai a Fuska nah”

Dariya Masroor yayi
“Sorry wallahi Mistake neh”
Mahnoor na Ganin Haka ta runtuma a guje, Saida ta fita Sannan ta Lek’o tana Murguda baki
“Daddy yace ka Sameshi a Study room”
Bata jira mai zaice bah Tabar wajan dasauri dan tasan halinshi yanzu yana iya Kai mata duka. Yasir ya K’alla yana cewa
“Au b ryt back”
Gyada mai kai yayi batare dayace komae bah..

Study room din ya nufa Ya murda kofan tareda Sallama, Daddy a Amsa Yana Murmushi
“Shigo have a Seat”
Zata Masroor Yayi
“Daddy ance Kana Kirana”
Medicated glass din dake idonshi ya Cire Yana K’allan dan nashi
“Ya kamata tunda yanzu kana Final year dinka neh ace ka nemi matar aure, Kaga daka gama dai kawai ai aure”
Turo baki Masroor Yayi
“Haba Daddy Aure kuma, I’m still young Banfa isa aure bah”
Dan Murmushi Daddy yayi
“Son Look at uh, Uh a Matured Enough ace ka Aje Iyali, Na Tsufa and I Want to see my grandchildren kafin na Tafi”
K’ara Cuno baki Masroor yayi yana gungunai
“Nidai Daddy dan Allah kabar Maganan nan banaso”
Kai daddy ya gyada
“Shiknan bbu damuwa, Yanzu dai idan kagama Kasani Company na Dake Lagos Nakeso ka Rik’e Har abada Na Barmaka”
Dago kai Masroor Yayi dasauri yana K’allan Daddy
“Daddy Are you serious”

Kamin Daddy yayi Magana Mami ta shigo Da Sallama, Tana Y’ar murmushi
“Kana Mamaki neh” cewar Mami
Kasa magana Masroor yayi saboda Farinciki, Dasauri ya Rungume Daddy yana Dariya
“Thank uh! Thank uh!! Daddy, U’re the best dad evr”
Dariya Mami da Daddy Sukai a tare. Barin dakin Yayi dasauri ya nufi dakinshi, Yasir dake Latse Latse a Laptop ya dago jin Yanda Ya banko Kofan dak’in, Rungume Yasir Yayi Yana Dariyar Farinciki
“Friend am now the Owner of MasMah Company”
Xaro ido Yasir yayi da Mamaki
“Are uh Serious”
Kai ya Gyada mai Yana murmushi, Rungume juna suk’a kara yi Cikeda Farin Ciki Yasir Yace
“I’m Very Happy for you Yasir”
Dagowa yayi ya K’alli Yasir din
“Friend Barinyi Wanka Na Fito Yau akwai Chilling”
Dariya Sukasa a Tare Masroor ya nufi Bathroom dasauri…

Bayan Kwana Biyu

Ameenatu Kullum Cikin Tunanin Likitan nan take, Duk ta Chanza ta koma Shiru shiru, Duk sanda Mama ta tambayeta sai tace bah Komai. Sulthana Ta Warke Ras ta cigaba da T’allanta Kamar yanda ta saba.

Yau Ta Dau T’allanta kamar yanda ta saba ta Fito, Yanke Shawara tai kawai ta Nufi Tashan dake garin dan a nan take tunanin Zatafi yin Ciniki, Tashan ta nufa duk da nisan dake Tsakani da Cikin Kauyen su. A haka har ta isa Tashan ta nemi guri ta zauna, Ciniki ta Fara Kadan kadan harta Siyar, da murna tadau Tray’nta Tana Fadin
“Alhamdulillah na Gode Allah yau Baffa bazai zaneni bah”
Gida ta Nufa Tana Tafiya Dak’yar saboda Yunwan dake Damunta. Layi ta Fara a Hanya tana Rik’e da Cikinta daketa Kukan Yunwa. A guje Suka taho dan Yau Masroor ne ke driving din, Bai ankara bah Yaga Mutum a Gabanshi tana Layi dasauri ya Taka burki Motar ta Tsaya Daidai Inda Sulthana Tak’e Tsaye Rik’e da Cikinta..

Jin K’arar taka Burki da K’uran daya tashi Yasa ta K’walla ihu Ta Matsa dasauri har saida ta Fadi, Kudin Dake Hannunta suka Watse iska ya soma Tafiya dasu. Masroor ne Ya fito dasauri Rai Bace Yana K’allanta
“Keh Wacce irin Dabba ce, Bakya Gani neh. So kike na bugeki ku samu abin Fada Koh”
Dafa Kafadanshi Yasir Yayi
“Haba Masroor Cool down mana Bakasan meye Dalilinta na Tsayawan bah”
Mik’ewa Tsaye Tai Dasauri Ta fashe da Kuka mai Sauti, Sai a Sannan Sukaga Fuskanta. Kudin dah suka watse ta soma bi tana kuka sosai Tana Harhadawa. Wasu Har sun Mata nisan da bazata iya daukowa bah”
Dawowa tai tadau Tray’n tana Cigaba da kuka sosai, Sai a Sannan Yasir Yayi Magana
“Friend Itace Yarinyan nan na Rannan da Mukagani a Kusada Motan mu”
Kurrrri Masroor ya mata ko Kiftawa bayayi, Yasir neh Yayi K’arfin Halin k’arasaw inda Take yana K’allanta
“Its ok Nawane kudin na biyaki”
Dago Manyan idanunta tai daya rune Zuwa ja Ta K’alleshi har ta bude baki zatai Magana wani Kukan Yazo mata Ta k’ara Fashewa da Sabon Kuka..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button