TAKUN SAAKA 14

Jikinsa ta faɗa dai-dai maigadi ya buɗe masa gate ya shigo, dan Hibbah wayarsa ta kira saboda shine na ƙarahe da ya kira Ummi yaji yaya jikinta? Dan ya kwana biyu baizo gidan ba. Duk yanda yaso ganin ya janyeta a jikin nasa hakan ya gagara, sai sake ruƙunƙumesa takeyi jikinta na rawa, yayinda taketa faman son ɓoye fuskarta a ƙirjinsa duk da tsahon nata gaba ɗaya iya ƙirjin nasa ta tsaya.
Cikin zafi-zafi ya shiga tureta yana girgizata. “K Muhibbat nutsu, muje inga Ummin gani nazo”.
Jin muryar da bata yayunta ba ya sata saurin ja da baya tabar jikinsa. Isma’il da ya samu ta rabu da jikin nasa da sassarfa yay gaba abinsa zuwa sashensu har yana haɗawa da ɗan gudu-gudu. kusan cin karo sukai da Abbah da ya koma ya ɗakko kayansa saboda ihun da Hibbah tayi ya farga da halin da yake a ciki. Duk da ya kuma ga Ummi a yashe a ƙasa sai kawai firgici biyu ya kamashi. Na farko kar wani yazo ya gansa a yanda yake sakamakon ihun Hibbah a zata wani abu yaso mata har Ummi ta shiga halin da take ciki a yanzu. Dan haka ya fito dan ya gudu salin alin, idan Hibbah ta sako sunansa a ciki kuwa yasan ta yanda zai kare kansa ai.
Haka kawai zuciyar Isma’il ta raya masa irin abinda Abban ke gudu. Dan haka yasa ƙafa ya taɗesa sai gashi a ƙasa tim. Takan kafafun Abba yabi da shaggun takalman ƙafarsa, ji kake ƙasss ƙashi na bada sautin karyewa ko tsagewa. Wata iriyar wahalalliyar ƙara Abba ya saki tare da ɗaukewar numfashi na wucin gadi. Ko waiwayensa Isma’il baiyiba ya ida afkawa cikin falon inda ya hango Ummi a ƙasa itama babu alamar rai tattare da ita.
“Ummi!… Ummi! Ummi!!” ya shiga ƙwala mata kira da kama hannunta yana girgizawa. Sai dai babu alamar motsi tare da ita sam. Mikewa yay da sauri ya ciro wayarsa yay kiran Yaya Umar da yasan shine mafi kusanci da gida. Sai dai bai ɗaga ba. Tunawa ana sallar la’asar yanzu haka ya sakashi cije lip ɗinsa na ƙasa ya cusa wayar a aljihu. Batare da tunanin komai ba ya ciccibi Ummi gaba ɗayanta yay waje. Sai lokacin Hibbah ta nufo falon sabida hango abinda Isma’il ɗin yay ma Abba.
“Muje asibiti” yace mata kawai yana nufar hanyar gate. Babu musu ta bisa tana kuka da riƙe hannun Ummi ɗin da ya ɗakko. Sai lokacin kuma Hajiya mama ke fitowa da ga sashensu itama. Ta bisu da wani irin kallo mai ma’anoni da yawa saboda ganin baƙon fuska ɗauke da Ummi ɗin. Dan duk zuwan da Isma’il ɗin keyi gidan ba taɓa haɗuwa sukai ba. Wahalallen ihun da Abba ya saki ne ya fargar da ita halin da yake a ciki, babu shiri ta runtuma a guje kansa tana ƙwala kiran sunansa…….
★★★★_____★_____★★★
Tun kan su ƙarasa asibitin Isma’il yay ƙoƙarin kiran doctor Bilal. Cikin sa’a kuwa ya ɗaga dan mutuminsa ne. Bayani yay masa cewar gasu a hanya tare da mara lafiya su zam cikin shiri. Dr bilal yace babu damuwa sai sunzo.
Cikin mintuna kalilan kuwa suka iso asibitin saboda uban gudu da yake zugawa a hanya. Kamar yanda yay fata sun sami su Dr Bilal na dakon isowarsu. Babu ɓata lokaci aka shiga da Ummi ciki.
Kuka sosai Hibbah keyi da son binsu, badan yaso ba ya riƙo hannunta yana ƙoƙarin dakatar da ita. Sai dai taƙi ta nutsu, dole yay mata yanda yasan zata nutsun, ya jawota jikinsa ya rungume. Da ƙarfi ya rumtse idanunsa zuciyarsa na wani irin bahagon gudu.
Itako Hibbah tuni ta ƙara lafewa tana wani irin kuka mai ban tausayi, dan gaba ɗaya ma ta mance a jikin wa take. Sai da ƴar nutsuwa ta fara zo mata ne sakamakon kiran wayarsa da akayi tai azamar janye jikinta. Komai baiceba shima. Sai ƙoƙarin ciro wayarsa da yay a aljihun wandonsa. Ita kuma ta koma kan kujera ta zauna tana cigaba da kukanta da add’ur ALLAH ya bama Umminsu lafiya.
Yaya Umar da yaga miss call ɗinsa bayan fitowarsu massallaci ne ya kirasa. Dan haka yay masa bayanin da bazai ruɗar da shi ba. Koda ya yanke kiran sai ya shiga kiran sauran suma.
★★
Cikin mintuna kalilan yaran Ummi suka gama hallara a asibitin. Gaba ɗaya hankalinsu a tashe yake. Sai dai sunata ƙoƙarin lallashin Hibbah da ke kuka sosai har yanzu. Harda su amai. Ga zazzaɓi mai zafi ya gama lulluɓeta matuƙa.
Fitowar Dr bilal ya sasu maida hankalinau garesa. Cikin son kawar da damuwarsu yace, “Ku kwantar da hankalinku babu wata matsala mai yawa insha ALLAH. Dan yayi ƙoƙarin kawota asibiti akan lokaci. Sai dai ku kiyaye dan ALLAH kar yazam muna tufƙa ana warwarewa.”
A take nutsuwa ta saukar musu. suka shiga jerama Isma’il godiya tamkar zasu ɗaukesa su goya. Shi dai ransa a dagule yake da takaicin Abbansu, dan shi baisan ba mahaifinsu bane.
Sun cigaba da dakon jiran farkawar Ummi da aka sakama ƙarin ruwa a asibitin har wajen sha biyu na dare da aka basu sallama saboda Alhmdllhi komai normal, amma sai Dr Bilal yace su barta anan ta ƙara hutawa har sai gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma. Duk sun gamsu da bayanin nasa. Dan haka sukai masa godiya da fitowa dan su tafi gida Hibbah da zata kwana da ita tare da Nurse tayo musu rakkiya.
Har sannan Isma’il na tare da su. Karan farko a tarihi da Hibbah ta dubesa cike da girmamawa da idanunta kumburarru. “Yaya Isma’il mun gode sosai. ALLAH ya bada ladan zuminci. Yanda ka jikan Ummin mu, kaima ALLAH ya baka ƴaƴa da zasu jiƙanka. Ya ƙarama Abbanka lafiya da tsahon rai mai amfani, ya jiƙan Umma”.
Ba karamin ratsa zuciyarsa addu’ar tata tayi ba. Ya kafeta da ido har sai da Yaya Umar ya zunguresa sannan ya sauke ajiyar numfashi da sakin murmushi. “Nagode sosai auta. ALLAH ya karama Ummi lafiya ya albarkaci rayuwarki. ALLAH ya baki miji na gari”.
Cikin jin daɗi yayunta suka amsa masa da amin. Itama tattausan murmushi da bata taɓa masaba a yanzu ta saki tana juya baya alamar taji kunya da addu’arsa ta ƙarshe. Su Yaya Usman suka ƙyalƙyale da dariya Ammar na tsokanarta. Bata kulashi ba dan yau batajin yin faɗa Ummi bata da lafiya.
Tun a asibitin suka rabu da Isma’il. Shi yay gida suma suka wuce gida. Inda tunkan su shiga sukaji labari a bakin maigadi cewar Abba ma na asibiti. Ya fadi ne a bakin ƙofa da alama yaji ciwo a kafafunsa. Hakama goshinsa da bakinsa sun fashe yanata zubar da jini ma.
Kasancewar da ga Hibbah har Isma’il basuyi musu bayani ba sai basu kawo komai a ransu ba suka ɗauka tsautsyine kawai. Addau’ar samun lafiya sukai masa suka shige. Dan ba’ai musu tarbiyyar son ganin lalacewar wani ba koda ace maƙiyinsu ne.
*________________________________*
A ɓangaren Abba kam da ƙyar aka iya ɗagasa da ga inda Isma’il ya taɗesa. Bakinsa duk ya fashe da goshinsa daya daushi kwalliyar tsitstsigen baranda. Hakama kafafunsa da alamar yayi karaya ko targaɗe. Dan ko takasu baya iyayi ma. Hasalima a sume aka ɗaukesa da ga gidan zuwa asibiti saboda jinin da yayta kwararwa kafin Junaid yazo da mota su fita da shi zuwa asibiti.
Su hajiya mama babu wanda yasan ainahin abinda ya faru da Abban suma. sai dai kansu ya ɗaure matuƙa ganin da ga shi sai boxer kayan da ya fito da su a hannu sabida ihun Hibbah yashe a gefe. Sunma rasa yaya zasu fasalta al’amarin musamman da likita ya tabbatar musu kafarsa ɗaya ta samu karaya da hannunsa. Ɗayar kuma tsagewar ƙashi ce ga ciwon goshinsa dana bakinsa da yay wanu zundun-dun uwa an saki shantu.