TAKUN SAAKA 45

*_Chapter Forty Five_* ………..Tunda suka fara tafiya duk sanda Hibbah zata ɗago sai taga idon Master a kanta. Dole ta tilastama kanta daina kallon nasa ta koma sauraren hirarsa shi da Abdull dan wata sabuwar kunya yake sake haddasa mata. Sai idan Abdull ɗin ya ɗan tsokaneta ne takanyi murmushi kawai.
Ba wata tafiya sukai mai nisa ba. Koda Abdull yay fakin bata fito ba sai da ta bari suka fara fita sannan ta fito a ƙarshe. Ɗan duban Master dake kallon agogon tsintsiyar hannunsa tayi, dan suna gab da shiga gidan ya saka mask a fuskarsa. Dai-dai ya ɗago shima suka haɗa ido. Saurin yin ƙasa tai da nata tana ɗan murza yatsun hannunta waje guda.
Abdull dake fiddo ledoji a booth yay ƴar dariya yana kallonsu. “Mutanen nan kuna lafiya kuwa? Sai wani abu kuke tamkar wasu budurwa da saurayi”.
Harararsa Master yayi da faɗin, “To kai banda sa ido miya kawo idanunka nan?”.
“Ikon ALLAH, sai na rufe idanu saboda karnaga masoya”. Abdull ɗin ya faɗa yana ɗan kallon Hibbah da tai kamar bata a gurin, sai dai sarai tana jinsu. Gaba ɗaya dai hankalinta na’a kallon gidan daya gama ƙyau da haɗuwa sashe-sashe kamar wani ƙaramin estate. A kallo guda zaka fahimci sabone ko tarewa cikinsa ba’ayiba, dan wasu wajejen ma ba’a kammala ginin ba.
Ƴan sandan dake a cikin gidan tako ina kusan su ashirin suka nufosu fuskokinsu da fara’a. Cike da girmamawa suka shiga ƙame jikinsu suna gaidasu. A yanda sukeyi ɗin zai baka tabbacin suɗin suna ƙasa da master ɗinne.
Ɗaya da ga cikinsu ne ya kwashi ledojin da sukazo da shi suka nufi sashen dake can ƙarshe da alamu suka nuna an ɗan jima da kamalashi. Suna shiga cikin falon Hibbah da ke a bayan Master kirjinta yay wani irin bugawa saboda tozali da tai da Yaya Ammar ya fito da ga kitchen ɗauke da kofi yana faman danna waya dake a hannunsa. Jin takun mutane da yawa ya sashi ɗagowa duk da yasan zagaye suke da ƴan sanda a gidan tun randa aka kawosu. Shima ya wani waro idanunsa waje lokacin da idanunsa ke sauka akan Hibbahn da Master daya cire mask ya koma Isma’il ɗinsa bayan sun shigo cikin falon. Da wani uban gudu ta kwasa har tana ɗan ture Master ta nufi Ammar. Babu wani tunani a ranta ta daka tsalle ta ɗanesa da sakin wani kuka mai ban tausayi.
Har cikin rai sai da Master yaji wani abu mai kama da kishi ya soki maƙoshinsa. Amma sai yay saurin kaudawa a ransa dan yasan dai Ammar ɗan uwanta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Fitowar Ummi dake magana cikin ɗan faɗa akan kiran da Ammar yake ƙwala mata yasaka Hibbah saurin sakin Ammar ta nufi Ummin. Itama ɗanetan tayi tamkar zata tsaga jikinta ta koma har Ummi na neman faɗuwa.
Da masifar ƙarfi Ammar ya shiga ƙwalama su yaya Umar kira su da matansu. Suma sai gasu ko suna sakkowa da ɗaɗɗaya daga saman Upstairs. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya harmutse. Har Hibbah tama rasa jikinwa zata kasance dan farin ciki. Sosai Master yaji tausayinta ya kamashi, dan shi kansa ya sake tabbatar da ɗunbin soyayyar dake tsakanin wannan ahali. Dan yanda Hibbah ke kuka haka su Yaya Muhammad ke faman sharar hawayen kewarta da ƙaunarta.
Da ƙyar Ummi ta samu suka lafa dan lura da su master ɗin da tayi. wanda su kansu su Yaya Abubakar sai yanzu suka gansa. Sosai mamakin ganinsa ya kamasu, dan kewar Hibbah ya mantar da su mamakin ganinta anan ɗin duk da basusan wanene yasa aka kawosu nan ɗin ba tsahon kwanki huɗu kenan.
“Isma’il yaya akai kuka san nan?”.
Ummi ta tambaya cikin tsaresa da idanu. A karon farko ya saki murmushi kansa a ƙasa.
Kafin ya samu damar cewa wani abu Yaya Abubakar daya kafesa da idanu ya kira sunansa cikin alamar kowanto. Guntun murmushi kawai master yayi yana ɗauke kansa. Ganin kallon da suke masa da fahimci sauran wasiwasi a ransu ya ɗan duba Hibbah da ke naniƙe da Ummi da alamar magana ce fal bakinta, hakan yayi dai-dai da satar kallonsa datai niyyar yi batasan shima ita yake kallo ba suka haɗa ido. gargaɗi yay mata da idanu alamar ta kiyayi bakinta. Baki taɗan tura gaba da ɗauke kanta tana sake nanuƙe Ummi da ɓata fuska.
Master ma ɗauke nasa idon yay ya maida ga duban Yaya Abubakar dake kallonsa har yanzu yana wani ƙayataccen murmushi dake tafe da ma’anoni da yawa. Murmushin shima Master yayi ya ɗauke kansa kawai. A karon farko yay ƙaramar dariya har haƙoransa na bayyana sosai. Ya kai hannu yana shafa fuskarsa da duban Ummi cikin haɗe hannayensa waje guda????????.
“A gafarceni Ummi, ni a haka labarin nawa yazone, nima bada son raina na ɓoye miki hakan ba. Dan kallo nake miki na uwa bayan mahaifiyata. Tun asali haka na tashi cikin ɓoyayyar rayuwa saboda samun cikar burina, sai kum yanayi ya sake ɓoyeni saboda neman martabata. Kuma Yaya Muhammad ku gafarceni yau ga auta nan na kawo muku, insha ALLAH kuma zuwa yanzu babu wani tasiri dake tare ga masu burin cutar da ita ko ku kanku. Nagode da halaccinku gareni. Nasan kunada tambayoyi fal bakinku akan kawoku da akai nan aka ajiye, karku damu insha ALLAH daga yau zuwa gobe zaku fahimci komai, dan haka a yanzu dan ALLAH kuyi haƙuri karku tambayeni komai”
Ya riga ya gama ɗauresu tunma kafin suce komai, dan haka bakunansu suka gagara ce masa koman domin tuhuma. Sai ajiyar zuciya kawai da suke faman saukewa a jajjere. Master ya maida dubansa ga Yaya Abubakar. “Ayi haƙuri babban Yaya, inaga ya kamata ka bimu mu maidaka wajen aiki yanzun dan kafi kowa buƙatar komawar a wannan gaɓar. Yana gama faɗa ya miƙe da ɗan duban Hibbah ya ɗauke kansa yana kallon agogo.
Dole yaya Abubakar ya miƙe shima ya fita domin kimtsawa batare da ya iya cewa komai ba tunda Master yace karsu tambayesa komai dan ALLAH. Sai dai kuma a ransa ya gama yarda Isma’il jami’in tsarone tabbas.
A nan suka bar Hibbah da hakan yay matuƙar sakawa cikin farin ciki, hakama sauran yayunta da su Zahidah. Sai dai duk bugun cikin da suke mata akan son jin wani abu game da Isma’il tayi mirsisi. Sai ma ita dataita musu ciwon baki akan dama sun san Isma’il ne ya saceta shiyyasa sukaƙi nemanta balle damuwa da rashin ganinta. Lallaahinta su Yaya Muhammad suka dingayi. Daga ƙarshe Ammar ya bata labarin komai daya shafi Master, wanda zuwa yanzu itama duk tasan wannan harma da abinda su basu sani ba na kasancewarsa jami’in tsaro. Tana da matuƙar wayo, dan haka taki yarda tayi maganar Abba Halilu a gaban su Zahidah da abinda taji har sai da suka shiga salla ɗakin Ummi su kuma suka tafi sashensu. Wayar Ummi ta ɗauka ta turama su Yaya Muhammad massege akan idan sun dawo salla zatai magana da su a sashen Ummi.
Suna idarwa kuwa koda suka shigo gidan kai tsaye sashen Ummin suka nufa, inda suka isketa naniƙe da Ummi tanata bata labarin su Habib da baba Saude. Ummi sai dariya take da jin daɗin autarta batai rayuwar ƙunci da damuwa ba ashe. Sai take sake ganin girma da mutuncin master a cikin idanunta da jin kaunarsa a ranta fiye da da can. Zama sukai suma suna sauraren surutun na Hibbah suna dariya, idan Ammar ya musa mata magana idan tayi yace bai yardaba su hau faɗa yana dariya da daɗa tunzurata. Sai Yaya Muhammad ya hararesa sannan ya bata haƙuri.