TAKUN SAKA 26

*_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
_________________________
*_Chapter Twenty Six_*
………..Kai tsaye gidan A.G Abba ya nufa. Dan yasan yau ranar hutu ce baya a Station. Kasancewar basu cika haɗuwa a gidajensu ba yasa da ƙyar maigadin gidan A.G ya yarda yay masa sallama da shi. Dan ya kira wayarsa yafi a ƙirga amma bata shiga.
Cikin takaici A.G ya fito, dan yayi zaman yin breakfast ne maigadi ya sanar masa zuwan baƙo. Turus yayi na ganin Abba. Sai dai tunda ya gansa babu damar komawa. Dole ya karaso inda yake yana faɗin, “Alhaji Halilu wai dama kai ne?”.
Kai kawai Abba ya iya kaɗa masa. Kafin ya ce, “A.G akwai babbar matsala fa”.
Saurin dakatar da shi A.G yay yana ɗan waige-waige. “Alhaji Halilu kayi haƙuri maganar nan bata nan bace. Inaga shigo ciki har motarka”.
Babu musu Abba ya koma mota. Maigadi ya wangale masa gate bisa umarnin uban gidansa. Koda yay fakin ciki suka shige babban falon baƙi na gidan. A.G na niyyar fita domin kawo masa wani abin taɓawa Abban ya dakatar da shi.
“A.G ci ko sha duk bashi bane a gabana yanzu, zo muyi magana.”
“Humm Alhaji Halilu kanada ruɗani kai dai. Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka dan nasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi dai”.
“A.G bazaka gane ba. Kai dai zauna kaji mike tafe da ni kawai.”
Babu musu A.G ya koma ya zauna. Abba da ke a firgice ya fara masa bayani muryarsa har rawa take. “Asiya da ƴaƴanta sunbar gidan a daren jiya. Zuwa yanzu kuma bamusan ina suke ba. Hakan ya sake tabbatarmin yaron nan Master ne ya taimaka musu…….”
Katsesa A.G yay da faɗin, “Master kuma Alhaji Halilu? Wai nikam miyasa duk kake zargin Master ne? Tayaya zai taimakesu miye ribarsa? Bayan kasani na sani akwai jiƙaƙiyar TAKUN SAƘA tsakaninsa da ƴarsu ma. To kai miye ma na damuwa da tafiyar tasu ne? Ba dama ta samu ba na hawa kan dukiyar da kake dako tsahon shekaru kaci karenka babu babbaka”.
“A tunaninka kenan. Amma da ga abinda ya faru zuwa yau ka auna da hankalinka da ka fahimci inda alkiblar yaron nan ta dosa mana. A wannan karon da alama burgar banza kakeyi baya tare da kai. Dukiyar nan kuma da kake ganin zan cita cikin sauƙi bazata ciyu ba, koka manta duk kaddarorinsa sunayen ƴaƴansa ya sa matsayin next of kings. Wasu kuma sunan Asiyar ne ma”.
“Hhhh wannan ganganne Halilu. A yanda na raini Master ni da abokan aikina bai isa zillemana ba ya maidamu abokan TAKUN SAƘAr sa. ai kaima kasan ko a gidan giya akwai babba. Maganar dukiya kuwa shi da kansa ma zai mana aikin”.
“Ni duk ban musa maka kun raini master da wani blaa blaa ɗin zancenka ba. Yanzu so nake ka kirasa ka bigi cikinsa ko zamu san inda su Asiya suke. Sannan duk yanda za’ai inason ka samamin ma’aikacin banki da zaimin aikin sirri kuɗaɗen dake a accaunt ɗin Aliyu su dawo accaunt ɗina baki ɗaya, ka kuma saka shi Master ɗin nemo mana lauyan Aliyu duk inda yake”.
“Maganar kiran Master ba damuwa bane, hakama zancen canja kuɗi zuwa accaunt ɗinka koshi zai iya mana wannan aikin. Matsalar ɗaya ce ka yarda Master bazai zama shashasha akan mace ba. Macen ma ƙaramar yarinya kamar ɗiyar ɗan uwanka”.
“To naji na yarda kirashi”. Abba ya faɗa badan ya yarda ɗin ba har cikin rai. Dan yanaji a jikinsa Hibbah tayi shu’umcin na mata akan Master. Sai dai shi A.G tsananin yardar da ya bama Master ɗinne yasa bai fahimtaba.
“Kiran Master bazai yuwuba a yanzu. Amma zan tura masa saƙo da kansa zai biyo lokacin da yaga ya dace”.
“To ashe kuwa yau a gidanka zan kwana”. Abba ya faɗa kansa tsaye.
“Gidana kuma?”.
“Ƙwarai kuwa. Dan babu inda zanje saina tattauna da Master.
“Humm Alhaji Halilu kai fa sam baka da haƙuri. Maganar zama anan bazai yuwuba. Kaje zan sameka gidan hutawarka. Kokuma mu haɗu wajen su Alhaji Alu”.
“Kawai jeka shirya ina jiranka mu tafi tare”.
Ɗan tsaki A.G yaja dan Abbah ya takura masa. sai dai babu yanda ya iya dole yace ya jirasan to.
★★★★★
A ɓangaren Hibbah kam Shawarar data yankema zuciyarta ne ya sata sauka a gadon ta nufi toilet. Fuskarta ta wanko ta fito. ɗaukar tray ɗin kwanikan da tai breakfast tai ta fita da addu’ar ALLAH yasa yabar gidan. Babu inda ta sani amma tsabar ƙarfin hali yasata yarda zata gane. Taji matuƙar daɗin ganin baya falon, taɗan tsaya yima falon saman kallon tsaf. Sosai tsarinsa ya mata ƙyau. Ga wani ƙamshi mai daɗi da sanya zuciya nutsuwa na tashi duk da mayataccen ƙamshin turarensa na neman dannewa. Tunaninta ya bata baza’a samu kitchen anan ba, dan haka ta nufi downstairs ɗin kai tsaye.
Tunda ta fara tako staps ɗin su Adam dake zaune a dining suna breakfast suka ɗago kusan a tare. Hibbah da ke sakkowa tayi ɗan turus ganin matasan samari kusan bakwai. (Su kuma waɗan nan fa?) tai tambayar a zuciyarta. Kai tsaye zuciyarta ta sake ayyana mata (Kin manta minene aikin mai gidan, ba dole kiga maza ba tare da shi). Tsaki taja a ƙasan maƙoshi tana ɓata fuska. Akan laɓɓanta tace, “Asararru”. Tana cigaba da sakkowa.
Suko su Habib tuni sun maida kawunansu ƙasa tun kallo guda da sukai mata. Tana sakkowa step ɗin ƙarshe suka haɗa baki wajen faɗin, “Barka da safiya aunty”.
“Aunty?!” ta faɗa tana kallonsu cikin ware idanu. Sai kuma ta turo baki, “Kujimin mutane dan ALLAH. Rusa-rusa daku zaku wani kirani aunty wannan ai zagi ne”.
“Tofa ga mai gayya mai aiki, Kunga wata zuƙeƙiyar halitta.
Cewar Salis a hankali.
Zungurinsa Zaidu yayi cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Karkai maganar banza matar babban yaya ce, akwai tazarar taku”.
“A gafarceni wlhy suɓutar baki ce”.
Baba Saude da ke zaune da ga can falo tana murmushi ta ce, “Kinga manta da waɗan nan shaƙiyyan ɗiyata. Keda baki da lafiya ai da baki fitoba kinma barsu zanzo na ɗauka.
Sai da Hibbah ta ɗan harari su Musbahu da murguɗa baki duk da bawai jin mi suke faɗa tayi ba sannan ta maida dubanta ga baba Saude tana sakin murmushi. “A’a babu komai mama. Ai naji sauƙi Alhmdllhi. Inane kitchen ɗin?”
Cikin jin daɗin wayewar kan yarinyar da ko alamar baƙunta babu tattare da ita ta nuna mata hanyar kitchen. Kan Hibbah tsaye ta nufi kitchen ɗin kuwa. Komai ƙal fes tamkar ba girki aka kammala a cikinsa ba. Ganin hakan yasa Hibbah ajiye kwanikan a wajen wanke-wanke ta fara yunƙurin wankewa.
Motsin wanke-wanken natane ya saka Baba Saude shigowa. “Ya ALLAHU ƴar nan inake ina wanke-wanke kina fama da kanki. Ki barsa su Habibu zasuzo su wanke idan sun gama shiritar cin abin nasu”.
(Uhm ai da yake ƴan daudu ne) Hibbah ta ayyana a ranta. A fili kuma sai tai ɗan murmushi. Karki damu mama zan wanke kawai. Ina maza ina wanke-wanke banda dai gidan naku a haguggunce yake”.