Uncategorized

TAKUN SAKA 26

      Baba saude da ba fahimtar ina Hibban ta dosa tai ba tai ƴar dariya da faɗin, “Taɓ. Ai indai waɗan canne komai yi suke har girki. Babana ya musu horon tarbiya mai ƙyau ai. Sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi”.

        Ɗan kallonta Hibbah tayi danjin abinda ta faɗa. Sai kuma ta saki guntun murmushi. “Mama iyayensu dai, shi da ya samesu da ga sama ai ba’ace tarbiyyarsa ba”.

       “To ƴar nan ai shine iyayen nasu. Dan dukansu da kike gani nan shi yay wahala da su tun daga gidan marayu, yawancinsu ma tun suna jarirai. Tarbiyarsa ce, horansa ne. Shine uwa a garesu shine kuma uba. Shine dangi. Ai samun mutum irin babana a wannan zamanin abune mai matuƙar wahalar gaske. ALLAH dai ya saka masa da alkairi ya cigaba da dafama rayuwarsa.”

        Karon farko da Hibbah tai sagade tana kallon Mama Sauden. Dan ba karamin dukan zuciyarta zancen yayi ba. Sai kuma tunawa da fasikancin da su Abba ke aikatawa da shi da tai yasata juyawa tana taɓe baki. A ranta tace (dan ya taimakesu shine kuma ya ajiyesu yana ɓata musu rayuwa kenan. ALLAH ya saka musu).

        Baba Saude da bata fahimci abinda Hibbah tai ba ta cigaba da bata labarin ƙoƙarin Master da jarumtarsa akan su Khalid na tsayama rayuwarsu har suka sami ingantaccen karatu a fanin islama da boko. Hibbah dai gyaɗa kai kawai take, dan zancen wani na shiga wani na fitane kawai. Ita duk wannan tarin alkairin nasa bawai gani take ba sam. Tsiyar da suke aikatawa da su Abba ta goge mata duk wannan farin nasa baƙi ya maye gurbinsa. 

      Sai dai cikin son bugar cikin Baba Sauden sai catai “Uhm lallai yaci sunan nasa Muhammad Shuraim”.

         Baba Saude tai ƴar dariya da faɗin, “Wai ƴar nan kinko iya faɗar sunan. Ni wlhy wahala yake min sunan nan nasa na larabawa. Shiyyasa nafi ganema kiransa da baba na saboda asalin sunan sa”.

      Gaban Hibbah ne ya faɗi. Kenan sunansa ne Muhammad Shuraim ɗin? Da sauri ta juyo tana duban baba Saude. “Oh mama bayan Muhammad Shuraim ɗin yana da wani sunan yanka ashe?”.

        Baki Baba Saude ta buɗe zata bama Hibbah amsa Habib ya shigo kitchen ɗin wuff tamkar an jehoshi. Waya ya mikama Baba Sauden. “Baba Master na magana”.

         Cike da farin ciki Baba Saude ta amsa wayar takai kunnenta da faɗin, “Alo babana”.

     Batare da Hibbah tasan mi ake faɗa da ga can ba taga Baba Saude na gyaɗa kai da faɗin, “To to babu matsala babana sai a dafa maka. ALLAH ya dawo dakai lafiya”. Da ga haka ta mikama Habib wayar. A dai-dai nan kuma su Salis suka shigo ɗauke da kwanikan da sukaci abinci.

    Ganin Hibbah ke wanke-wanke suka zaro idanu waje. “Aunty da kanki? Rufa asirinmu kar boss yay mana walmakalufatu”.

     Cikin bata fuskar haushi biyu Hibbah ta juyo tana dubansu. “Malami kubar wani kirana da Aunty niba auntynku bace.”

         Dariya kawai sukayi batare da sunce mata komai ba. Sai ma Habib da ya sake faɗin, “Aunty kibar wanke-wanken zamuyi Please”.

     Harara ta dallara masa. Yay saurin ɗora hanunsa saman baki yana faɗin, “Na tuba”. 

     Dauke kanta tai batare data tanka ba. Idris ya matsa tacan gefe yana tattare hanun rigarsa. Bara to na miki ɗauraya kawai. Banza tai masa ta cigaba da wanke kwanikan a cikin kumfar data ƙara ganin sun ƙaro kwanikan. Wannan taruwar tasu a kitchen ɗin ya hanata jin ɗayan sunan na Master. Hakan kuma ba karamin takaici ya sakata ba shiyyasa ta haɗe fuska har suka kammala wanke-wanken bata sake kulasu ba. Sai sauraren hirarsu da Baba Saude da takeyi. A ranta kuwa sai gulmarsu take wai sun cika surutu.

         Suna kammala wanke-wanken Baba Saude tace taje ta huta zata ɗaura girkin rana. Cike da jin daɗin hakan Hibbah tace zata tayata. Duk yanda Baba Saude ta lallaɓata akan tabari sai ta ƙara jin sauƙi ta dage zatayi. Fahimtar yarinyar babu ruwanta akwai sauƙin kai yasa baba Saude barinta sukai girkin tare. Kusanma Hibbahr ce tayi komai kaɗan baba sauden ta tayata. 

      Har sukai girkin suka ƙare tas Habib na nane dasu a kitchen ɗin yaƙi fita. Hakan ya ƙarama Hibbah takaici matuƙa dan bata samu yanda take so ba. 

        Sai dai cikin sa’a Baba Sauden ta fita jera abinci dining dai-dai Habib ɗin yana fita a kitchen ɗin saboda lokacin salla yayi zasuje massallaci.

         Harara ta raka bayansa da shi tana sauke numfashi, dan duk surutunta da rawar kai ta kula waɗan nan samarin sun damata sun shanye. Sauran kayan da suka rage ta ɗakko ta fito zuwa dining ɗin itama. Tana tsaka da taya baba Saude shirya kwanikan taji ƙarar waya nokia. Da sauri baba Saude ta nufi falon tana faɗin, “Tofa wake kirana ni Saudatu?”.

        Wani ɗan tsalle Hibbah tayi dadi kamar zai karta. Sai kuma tai saurin kama kanta ganin baba saudan ta dawo dining ɗin tana faɗin, “To nidai Bara’u banajinka sam. Nasan dai so kake kayi magana da Zaituna gashi kuma bana gida ina wajen aiki. Ka kira wayar Habu mai shago sai ya bata dan nasan yanzu ta dawo gida”. Da ga haka ta cire wayar a kunnenta tana mita.

        “Kai samarin zamani dai babu kunya. Kigafa wanann ja’irin ɗan makwafcinane. Akwai ƴar maƙwaftanmu da yake so bata da waya kullum sai ya kira a wayata sunyi wayar dare. Yau kuma bansan wace fitina tasashi kira da ranar ALLAH ba”.

      Hibbah da ke cikin jin daɗi tai ƴar dariya kawai.

        Baba sauden ma sai bata sake cewa komai ba ta ajiye wayar a dining ɗin ta cigaba da aikinta. Aiko wani sanyi ya sake sauka a zuciyar Hibbah. Cikin dabara da wayon da ALLAH ya bata ta shiga gyara zaman kayan dining ɗin harta iso ga wayar. Cikin dabara ta ɗauka tai ƙasa da ita tasa a silent. Kafin ta faki idon Baba Saude ta tura a cikin zani.

       A dai-dai wanann lokacin Master ya turo ƙofar falon ya shigo da sallama ciki-ciki. Cike da mutuntawa a garesa baba Saude ta washe baki tana faɗin, “Babana sannu da dawowa”

        Saurin juyowa Hibbah da sam ba jin sallamarsa tai ba tayi, idonta ya sauka akansa dai-dai yana gyaɗa ma Baba Saude kansa. “Baba ya gidan?”. Ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin wuce Hibbah da ya nuna tamkar ma bai ganta a falon ba.

      “Gida Alhmdllh babana. Dan yau na ƙara samun ƴar tayen hira”.

    Sarai ya fahimci Hibbah take nufi, dan haka ya fara hawa steps ɗin kawai batare da ya sake cewa komai ba. 

      Harara Hibbah ta raka bayansa da ita. Wani sashe na zuciyarta najin tsananin takaicinsa da kallonsa mutum mai tsananin girman kai da wulaƙanci. Sai da ya ɓacema ganinta ta ɗauke kanta da duban Baba Saude, “Uhm Mama tunda mun gama nima bara naje nai salla”. 

     Juyowa baba saude da ke nufar kitchen tai ta dubeta. “Eh ɗiyata kin fini gaskiya kam. jeki kiyi nima bara na haɗa ma Babana abinci da Habibu sun dawo sai ya kai masa saman”.

        “To mama”. Hibbah ta faɗa tana nufar upstairs. Harta hau step na biyu baba Saude ta dakatar da ita. “Kinga yi haƙuri ko zaki dawo ki tafi masa ma da abincin ma kawai, a saman nan ake shirya masa shi. Dan tunda kikaga ya dawo to yunwa yake ji”.

     Hibbah dai da yake neman hanyar kuɓuta take kafin baba Saude ta farga da rashin wayarta da sauri tace, “To baba ki bari kawai su dawo sai sukai masa kamar yanda kuka saba. Kar kuma kaiwar tawa yasa hakan bai masa ba”.

       Gamsuwa da zancen nata da kuma sanin halinsa yasa baba Saude faɗin, “Eh gaskiyarki kuma, dan dama inba Habibu ba babu ma mai yawan hawan saman kai tsaye sai inshi ya bukaci ganin wani a cikinsu. Jeki kawai”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button