TAKUN SAKA 26

Hibbah da batai tsammanin samunsa zaune a falon ba tai ɗan diri-diri. Ƙoƙarin haɗiye abinda ya tsarga matan a maƙoshi tai tana cigaba da takowa ganin baiko nuna alamar yasan da shigowarta ba, kamar barci yake ma a hakan.
Ta ɗan taɓe baki saboda ganin wani zaman ƙasaita da yay a cikin kujera. Hanyar ɗakin data tsinci kanta a ciki ta nufa zuciyarta na tsitstsinkewa saboda shegen sanyin da falon ya ɗauka. Amma shi ko a jikinsa, da alama ma matsanancin daɗi yake masa.
“Kin koma satan waya ne?”.
Ƙasaitacciyar muryarsa mai amo da kamewa ta daki dodon kunnenta. Cak ta tsaya da rumtse idanunta da ƙarfi, dan duk tsiwarta tana shakkar wanda baizo mata da wasa ba. Ko yau da safe takaicin tuno maganarsu Abbah yasata iya maida masa murtani badan bata ganin girmansa a idanunta ba. Ko bai tanka maka ba kwarjininsa da kame kai yasa ma’abocin mu’amulantarsa jin shakkarsa.
Juyowa tai a hankali tana ɓata fuska ranta fal mamakinsa. Ta ɗan saci kallonsa amma sai taga yana a yanda ta shigo ta samesa ido lumshe bai motsa ba. Duk yanda taso yin tsiwar ta gagara koda motsa laɓɓanta tsabar yanda ya cika mata idanu har bata ganin wani fili a falon, dan fuskarsa tamau take babu alamar yasan minene fara’a.
Cikin pretending da shagwaɓar da takema su Yaya Muhammad ta ce, “Ni wlhy ba ɓarauniya bace. Tunda dai ba’a taɓa cewa na ƙwamushe kuɗaɗen bankin mutane b?”. Tai maganar da ɗan murguɗa baki duk da zuciyarta kuwa babu abinda take sai lugude.
Lumsassun idanunsa da suka kaɗa jajur kamar wanda yake cikin ɓacin rai ya buɗe akanta. Sallama Habib ɗauke da tray babba ya hanashi yin maganar da yay niyya..
Itama sai ta juya tana amsa masa sallamar da yay ranta fal murnar samun hanyar kuɓuta. Habib ɗin ya ɗan risinar da kansa cike da girmamawa ya ce, “Sannu Aunty”.
Harara Hibbah ta zuba masa tana sake ɓata fuska. Shi dai yay gaba abinsa yana murmushi. A tunaninta zuwan Habib ɗin zai kuɓutar da ita. Sai taga saɓanin haka dan ko motsi baiyiba, baima amsa gaisuwar Habib ɗin ba, sai mayatattun idanunsa da har yanzu ke a kanta.
Ƙasa tai da kai, ta kasan ido ta gama auna tafiyar da zata kaita ɗakinta. Ta ɗan dago ta sake dubansa. Ganin har yanzu ita ɗin dai yake kallo sai ta ɗan fara taku kamar zata koma wajensa. Hakan da tai ne shi kuma ya sashi ɗauke idanunsa ya maida kan Habib da ke zuba masa abinci.
Tana ganin haka ta zambaɗa da gudu. Sai ƙarar takun gudunta kawai suka jiyo.
Habib yay saurin saka hannu ya danne bakinsa jin dariya zata kufce masa. Shiko gogan wani irin fici-ficin fitina yayi da idanunsa yana sake tsuƙe fuska. Cikin muryar da babu wasa ya dubi Habib.
“A rufemin network ɗin gidan nan na tsahon awa biyu”.
Tamkar Habib zai fasa kuka ya dubesa. “Master awa biyu?”.
Harara ya zuba masa. Habib yay saurin gyaɗa kansa da amsawa da to. Kasancewar ya kammala zuba masa abincin ya nufi hanyar downstairs dan babu damar ƙara yin musu.
Shi ko lip ɗinsa na ƙasa ya dan ciza da jawo abincin gabansa ya fara ci a nutse. Sai dai kuma tun a laumar farko yaji banbancin girkin dana baba Saude. Idanu ya lumshe ya sake buɗewa akan abincin, dan ɗanɗanon sak na wadda a yanzu yakema kallo irin na uwa mai saka zuciyarsa farin ciki da yin rauni.
A hankali saman laɓɓansa ya furta “ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka Ummi”…………✍
Ni dai na ce “Hummm Master wace Ummi?”????????????
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]