Uncategorized

TAKUN SAKA 27

         Dara-daran idanunsa ya zuba a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta, tare da ɗago hannunsa na dama ya ɗaura saman cikinta. A bazata Hibbah taji wannan al’amari. Babu shiri ta zabura ƙafarta na gocewa tai baya. Cikin zafin nama ya taro ƙugunta ta dawo saman ƙirjinsa, sannan kuma ya tura hannunsa da ke kan cikinta ƙasan rigarta.

        A matuƙar firgice Hibbah da taji saukar lallausan tafin hannunsa saman fatar cikinta daya tura cikin zaninta  ta ce, “Na shiga uku Ummi”.

         Shima da ƙarfi ya cije lip ɗinsa yana zaro wayar baba Saude da ta soke a zani da sakinta ya matsa saboda fitowar baba saude da ga kitchen tana faɗin, “Ƴar nan lafiya? Badai faɗuwa kikai ba?”.

        Ina Hibbah bama taji baba Saude ba. Dan yana sakinta ta zame ƙasa saboda wani irin rawa da jikinta keyi. Shi ko tini ya fara taka steps ɗin tamkar bai aikata komai ba. Dan ko tanka maganar baba Sauden baiyiba harya ƙarasa sakkowa ƙasan.

      “Babana kamarfa ihun yarinyar nan naji”. Baba Saude ta faɗa aɗan rikice. 

          Cike da basarwa ya ɗan dubi Baba Sauden ya janye idonsa. “Kunnenki ne kawai baba”. Yay maganar yana nufar hanyar fita abinsa.

      Cikin shakku baba Saude ta bisa da kallo, sai kuma ta kaɗa kai kawai ta juya kitchen tunda taga da ga saman ya ke. Maybe kunnen nata ne kamar yanda ya faɗa.    

        kuka sosai Hibbah ta saki jikinta a ƙanƙame. Dan wannan sabon abune wanda a tsayin rayuwarta bata taɓa fuskanta ba ga wani ɗa namiji. Ga baƙin ciki da takaicin wayar da ya amsa. Sosai takejin kewa da tsoron kar wani abu ya sami ahalinta. Dan babu abinda ta gano a tsakkiyar idanun Master sai ɗunbin hatsabibanci da mugunta. Tabbas zai iya aikata duk abinda zuciyarta take tunani. Anya bazata janye kalamanta ba kodan ceton ahalinta?, Ummi tana da ciwon da bata buƙatar damuwa, rashinta a gida kuma babbar damuwace ga Ummin da yayyenta. A yanzu haka ALLAH kaɗai yasan halin da suke ciki na rashin ganinta.

       Cikin Kuka ta ke faɗin,, “Wlhy Ummi zan iya sadaukar da komai domin ke, na haƙura da *takun saƙar* da shi zan roƙesa ya dawo dani wajenki”. Tana maganar tana miƙewa a wajen, ɗaki ta koma ta faɗa saman gadon da jan bargo ta ƙudindine har saman kanta. Dan harga ALLAH wani irin zazzaɓi-zazzaɓi ma takeji. Ummi tasha gargaɗinta da tsoratar da ita akan illar sakarma namiji jiki harya iya kai hannu wani sashe naka. Sai gashi tsohon najadun nan yau ya tura ƙazamin hanunsa har kan mararta.

★★★★★

             A ɓangaren Abba suna fita daga gidan A.G gidan shakatawar Alhaji Sallau suka nufa. Sun samesu kusan su biyar da alama zaman jiransu suke suma. Da ido R.D yay ma A.G alamar miya kawo Abba cikinsu?, dan gaba dayansu manyan masu faɗa aji ne a ƙasa da mukamai ke hannunsu. Sannan a shekaru duk sun girmi Abban, hasalima sune suka ɓata rayuwar Abban dan lokacin da Alhaji Balele ya sakoshi a harkar wajensu yake kawosa kasancewar su ubannin gida a garesa. kai A.G ya gyaɗa masa da masa alamar cool down.

     Cikin kaɗa kai R.D ya janye idanunsa yana gyara zamansa cike da isa. Kasancewar duk ubannin gida suke a wajen su Abban cikin girmamawa ya gaidasu. Kafin ya kai zaune inda A.G ya nuna masa.

         Alhajin Mande ya dubi Abban da faɗin, “Lallai Halilu idonka kenan?”.

     Ƙasa Abba yayi da kai a girmamame. “Ayi hakuri ranka ya daɗe na samu raunine a ƙafa, amma Alhmdllh zuwa yanzun na fara fita kaɗan-kaɗan”.

       Alhajin Mande ya gyaɗa kansa da faɗin, “Eh A.G ya sanar mana ai randa ya kawo mana invitation ɗin auren yaran wajenka. Sai dai kuma muna baka haƙuri bamu samu zuwa ba bisa wasu dalilai”.

       “Babu komai ranka ya daɗe dan auren ma ba’a ɗaura ba”.

       “Tofa miya faru aka fasa?”. 

Cewar Engineer Zailani Ginger.

      “Engineer matsala aka samu, wadda a dalilintane ma muka zo nan ni da A.G”.

       Gaba ɗaya dattijan ala kwankwan ɗin suka maida dubansu ga A.G. 

      A.G ya gyara zamansa yana dubansu shima. “Hatsabibin yaron nanne ya ɓata masa aiki”.

     Kai tsaye R.D yace, “Kana nufin Master?”.

       “Shi kuwa”.

Kusan a tare suka haɗa baki wajen faɗin, “Ya akai yasan Master shi?”.

        A.G yay ɗan tiri-tiri da faɗin, “E..e eh ya sanshi ne sakamakon yarinyar nan data hari Master ɗin kwanaki ƴar yayansa ce. To da mukai bincike ta office akan yarinyar ne na fahimci haka. Shine na nemesa danjin wani abu akanta. Daga nanne ya roƙeni muyi masa wani aiki akan yayun yarinyar da uwarta shima zai taimakemu ta yanda zamu amfani da basirar yarinyar. Shine fa na saka Master akan aikin dan nasan zai iya, gashi kuma yarinyar dama ta shiga gonarsa. Hakan yasa muka yanke shawarar ya aureta………..”

         “Aure fa kace?”. 

Dr Sufi ya faɗa da mamaki.

      “Eh Doctor, dan aurenne kawai zai iya bashi damar ɗaukar yarinyar cikin sauƙi saboda ƙanwar shegen jami’in nanne Abubakar Aliyu Hamza Gwarzo. Kasan kuma shima hatsabibin kansa ne mai faɗa aji wajen I.G”.

      Lokaci ɗaya ruɗani ya bayyana a kan fuskarsu. Engineer Zailani yay saurin tare numfashin A.G da faɗin, “To yanzu dai yaya akai?”.

       Carab Abba ya karɓe zancen. “Ya auri shegiyar yarinyar, sai dai ni ya wargazamin nawa aikin na hana yayun yarinyar auren nawa ƴaƴan. Yanzu hakama ya ɓoyesu inda ban sani ba”.

         “Alhaji Halilu kabi a hankali, na tabbata master bazai aikata hakanba sai da manufa”. A.G ya faɗa cikin jin haushi. Kafin Abbah ya ce wani Abu Alhajin Mande ya karbe da faɗin, “Master kam banajin zai ɓata lokacinsa akan wanann shiriritar, amma ku jira na san yana gab da zuwa nan”.

        Cike da zalama Abbah yace, “Yauwa Alhmdllhi. Gara yazo naji yaya aka faɗi a ragaya ranka ya daɗe”.

       Komai babu wanda ya sake ce masa. Dan ama kusan dai-dai rufe bakinsa maigadi ya shigo yana sanar dasu isowar Master ɗin.

      Da hanzari R.D ya bada damar shigo da shi, dan sun rasa miyasa baya yarda ya shigo musu kai tsaye a duk sanda suka buƙaci ganinsa. Koda waya ya gama da su sai ya nema iso yake shigowa.

        Cikin izzarsa da ƙasaita ya shigo falon da sallama ciki-ciki. A kusan tare suka amsa suna zuba masa ido tamkar tsoffin mayu. Yana matuƙar birgesu da tafiya da imaninsu. Sai dai sam sun kasa samun kansa domin biyan bukatar zukatansu. Ya dai amince yay musu sauran ayyuka, hatta kisan kai idan sukace sunaso ayima wani yakan amshi aikin, amma sanin yaya yake aikin har yanzu basu da tabbas. Kuma bai basu wata ƙofar masa tambaya ba, dan duk da karancin shekarunsa a cikinsu baya ɗaukar raini koda na kallon bamza ne.

         Zaune ya kai bisa kujera yana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cike da ƙasaita. Kafin ya kai hannu bisa glass ɗin fuskarsa ya gyara masa zama da ƙyau yana kare musu kallo ta ciki. “Barkan ku”. 

     Ya fada a taƙaice yana zuƙar iska da fesarwa. Sosai sukejin takaici na salon iskancinsa da izza. Sai dai basu da damar tankawa dan duk sun kasance a tafin hannunsa, saboda sirrikansu da yawan gaske ya gama sani.

        Bakuna suka shiga washewa. Kowanne na ƙoƙarin tambayarsa yaya yake. Nanma a takaice ya amsa musu da cewar, 

      “Normal”. 

  Ya tsuke bakinsa.

          A.G ya nuna masa Abba. “Ina fatan ka gane wannan ko Master?”.

      Cikin ɗan yamuste fuskar boginsa ya ce, “Kamar..”

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button