TAKUN SAKA 27

Haushi ya kama Abba. Ya zuba masa harara da faɗin, “Kai saurayi miye kuma Kamar? Ni nasan ka ganeni kodan maƙudan kuɗaɗen dana sauke maka kafin karɓar aiki na”.
Mai makon ya amsa Abbah sai ya duba A.G da faɗin, “Wanann shine dalilin kiran?”.
“A’a ina” R.D yay azamar faɗa saboda sanin wulaƙancin Mastern. Kaɗan da ga aikinsa ya karta musu rashin m ya tashi yay tafiyarsa.
Abba da ya fahimci gadara bazatai ba sai ya kwantar da murya. “Kai ko saurayi dan ALLAH ka saurareni. Wlhy ina cikin matsala fiye da zatonka. Kuma ba kowa bane ya sani wabilahillazi sai kai. Miyasa munyi maganar ka auri yarinya kawai sai ka wargaza auren nawa ƴaƴan kuma? Bayan kuma duk na sanar maka ƙudirina akansu”.
Nan ma banza yay masa bai tanka ba, sai ma agogon hanunsa da ya kalla. Da sauri A.G da ya fahimci ma’anar kallon agogon ya ce, “Ayi haƙuri a sauraresa Master. Rashin tabbatar wannan aikin zai iya saka masa ciwon zuciya wlhy. Nasanka kuma baka karya alƙawari, ga shi bamu san dalilinka na hana auren yaran nasa ba”.
Kamar bazai tanka ba kuma sai ya dubi Abban. “Mi kake buƙata yanzun?”.
Baki Abba ya washe yana gyara zama. “Yauwa ɗan albarka. Su yaran da ka wargaza auren yaran nawa da su nakeson sanin inda suke su da uwarsu. Idan da hali kuma a karminsu ɗaya bayan ɗaya dan ALLAH kamar yanda mukai da kai a farko, ni yanzu ma basai sun auri yaran nawa su wani sami ciki ba. Sanann akwai dukiyarsu da ke a hannuna da kaddarori duk sunayensu ubansu ya saka matsayin masu gadarsa, dole sai sun saka hannu su da lauyan baban koda zan iya amfana da su. To shi kuma lauyan ya ɓata ɓat tsahon shekaru shegen shine nakeson a kwashe kuɗaɗen a maidosu accaunt ɗina. Takardun kaddarorin kuma a maida sunana. Amma inason a fara kashemin ita yarinyar da aka ɗaura aurenku da itan sannan, dan wlhy da baka ɗauketa ba a jiya ni da kaina da zan kasheta”.
“Zamu sake sabon ciniki. Dan baka sanarmin gaskiya ba a wancan aikin shiyyasa na wargaza auren ƴaƴanka. Ni idan za’a bani aiki bana son ƙarya bana son munafinci. Yanzu ma idan ka ƙara zakaga ba dai-dai ba. Ka tattara dukan bayanai da accaunt no. Ɗin da kuɗin suke da takardun kaddarorin ka bama A.G tare da kuɗin aikina”.
Yawu Abba ya haɗiye da ƙyar, dan awancan aikin fa 5mil ya bashi. Amma dan tsabar wulaƙanci ace wai sun ciwu batare da an masa aikin ba. Shikam ya fahimci yaron nan zigidir yake son masa. To amma ai yanzu kuɗaɗene masu nauyi zai samu. Dan haka ya sake gyara zama. “Na yarda zan sake biya. Amma nawane to? Dan ALLAH amin ragi”.
Cike da shan ƙamshi Master ya ɗan dubesa ta cikin glass ɗin idonsa ya ɗauke kai. “Zaka fara bada 10mil yanzun nan, bayan naga takardu da nauyin kuɗaɗen asusun zan faɗi farashi”.
“Bantan uba kana nufin 10mil ɗin ma ba farashi bane?”.
“Kuɗin saka data and transport ne”. Master ya faɗa a gadarance.
Abbah zai kara magana A.G ya zunguresa. Kallonsa yay a marairaice tamkar zaiyi kuka. Amma sai ya girgiza masa kai alamar karya sake cewa komai. Dole Abbah yay ƙasa da kansa. A zuciyarsa kuwa sai jama Master kwando-kwandon tsinuwa yakeyi.
Da ido Alhajin Mande yay ma A.G alamar ya sallami Abba. Kansa ya gyaɗa yana duban Abban. “Alhaji Halilu kaje ka tattara abinda ya ce idan na fito zan biyo ta gidanka na amsa”.
Miƙewa Abba yay yana faɗin, “To. To bara naje ɗin, amma dan ALLAH ka ɗan sake nemamin ragi kuɗin yayi yawa wlhy, dan ya zabtare kaso biyu bisa ukun abinda na mallaka idan aka haɗa da biyan farko. Gashi nayi hidimar kamawa shegun yaran can gidajen haya babu gaira babu sabar”.
“Babu damuwa kaje. Zamuyi magana da shi”. A.G ya faɗa cikin ƙosawa.
Sai da sukaji fitar motar Abba a gidan suka maida hankalinsu ga Master da ya lafe cikin kujera idanunsa da ke cikin glass a lumshe. Dr Sufi ya fara magana yana ɓalle murfin robar ruwa. “Master taruwarmu anan tana da nasaba da wani babban aiki da ya sake taso mana. Amma kafin mukai maganarsa nakega ya kamata ace kuɗaɗen hannunka daketa taruwa kusan shekara biyu mizai hana a ɗan raba wasu a ciki kar asusun ya cika da yawa har wani yay mana ƙafar angulu. Kaga tunda aka fara aikin nan biyanka kawai muke kuɗin aiki amma kuɗaɗen ko nera bata shiga aljihun ɗaya da ga cikinmu ba, sabanin da da kayi aikin kake bamu abunmu”.
Miƙewa yay zaune sosai tare da zare glass ɗin idonsa. Ya zubamasa razanannun idanunsa masu kama dana Zaki. “Likita kasan bana magana biyu, shiyyasa tun farko na sanar muku sai na kammala muku wannan aiki zan baku sakamako. Ko kana tunanin da kuɗaɗen nan nake harkar rayuwata ne?”.
Da sauri Alhajin Mande ya ce, “Haba karma ka kawo hakan a ranka Master. Mu da kake gani anan mun matuƙar yarda da kai shiyyasa muke iya fasa maka sirrin cikinmu, karka manta tun kana ƙaramin ɗan jagaliya kake tare damu. Sam ba haka Dr Sufi ke nufi ba. Amma nima sai nake ganin ko kaso ɗaya bisa uku ne na kuɗin aɗan raba mu farfaɗo koda bayan ka gama wannan aikinne na yanzu da zamuyi magana. Dan shima asusun manyan gwasake ne”
Komawa yay jikin kujerar ya kwanta yana maida glasess ɗinsa cike da salonsa na izza. “Zaku bani accaunt numbers naku na sirri. Bayan aikin nan ya kammala zakuji billions ɗari-ɗari”.
Wani irin kallon zazzaro idanun mamakin jin nauyi kuɗaɗen da kawai tsakurowa zaiyi ga abinda ya tara musu sukai. Atake bakunansu duk suka washe. Alhaji Sallau yace, “Kace abin na gaske ne Master mu ƙara ƙaimi”.
Wani ɗan salo kawai yay masa da yatsunsa???????? ba tare da ya bashi amsa ba.
Wani irin shegen daɗi ya baibayesu. R.D ya jawo takardun gefensa yana faɗin, “Waɗan nan sune jadawalin sunayen waɗanda za’a wawashe ma asusu. Uku da ga ciki munason a fallasasu wa duniya bisa handamar da suka shuka akan kuɗaɗe. Na farko I.G na ƴan sanda. Sai ministern man fetur. Da shegen can Barau na ALLAH shaharren ɗan kasuwa a zahiri a baɗini kuwa kuɗin kwangilar gwamnati ne yake handama da ga aminansa da suka ɗaure masa ƙugu a gwamnatin. Sai gwamnan jihar gabas damu.”
Wani shegen murmushi Master ya saki yana miƙewa. ga accaunt no ɗina nan naji alert. Da ga safiyar jibi idan ALLAH ya kaimu zakuji sakamakon aiki.”
Dariya suka shiga ƙyalƙyalewa da shi suna tafawa. R.D ya miƙa masa takardun sunayen duk waɗanda suka lissafo da bayanai akansu yana faɗin, “Master muna son rayuwar shegen I.G ɗin can ta salwanta fiye data kowa. Kaima dai kasan yanda yake tsaye kullum akan son damƙoka da gurfanar da kai harma da alwashin da yake ɗauka na tabbatar da hakan. Ko nera kartai saura a asusunsa. Akwai bayanai shiryayyu akansa da fitarsu sai ta saka zuciyarsa bugawa kafin ma hukumar daƙile ta’annati da kayan gwamnati ta fara bincike a kansa. Kaga sai muga da wane taurin kan nasa zai cigaba da bibiyarka balle ya gano sunanmu da ke manne da naka a baɗini”.
Komai Master bai ce ba. Sai amsar takardun da yay ya nufi hanyar fita yana ɗaga musu hannu alamar bye.
Yana gama ficewa kusan dukansu sukaja tsaki. Dr Sufi yace, “Shegen yaro mun ɗorasa akan samu amma yana neman fin ƙarfin yanzu ɗan banza hatsabibin aljani”.