Uncategorized

TAKUN SAKA 28

      Ummi da gaba ɗaya zuciyarta ta gagara gaskata abinda Master ya faɗa ta gyaɗa masa kai cikin sanyi da rauninta. Sai kuma ta duba su Yaya Muhammad da ke ta ƙyalli cikin shaddoji na zuwa ga amarensu. Da idanu tai musu umarni.

        Ita ba abar wasansu bace, dan haka babu wanda ya nuna alamar musawa suka ƙarasa ga kujerun falon duk suka zauna.

      Master ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana jingina bayansa da kujerar da ya zauna tare da lumshe idanunsa. Tsahon minti ɗaya da wasu sakanni ya buɗesu a hankali yana tasowa zaune sosai ya fuskanci Ummi.

      “Da farko zan fara da neman gafararki Ummi, matsayinki na uwa da nake kallo da kima da daraja bayan mahaifiyata. Tabbas kin bama Isma’il gata da kulawa irin wanda a kowane dare yake kukan kishirwar rashin samu tun daga ƙuruciya. Na shigo jikinku a dalilin kutse da Muhibbat taima rayuwata. Kafin isowa ta gareku da nufin yaudararku na hukuntata nazo, sai dai labarin ya canja tun a ranar farko, awannin farko, mintunan farko, sakannin farko. Ummi kece kika canja komai, a lokacin da zuciya batai tunanin sauyawar ba. Dan da ga lokacin da wanann hannun naki mai albarka da daraja ya sauka saman tsakkiyar kaina yayin da kike a gadon asibiti, kika furta kalma mai matuƙar tsada da girma a gareni komai ya canja.”

      (Na gode ɗana. ALLAH yay maka albarka. Ya tsare rayuwarka da imaninka). “Wannan addu’a ce da kika ambata a gareni wadda zuciya ta daɗe tana ƙishirwa da bege”. Yay murmushi mai ciwo tare da kai yatsa ya ɗauke wasu guntun hawaye da suka ciko idanunsa suka taru a gefe.

    Gaba ɗaya jikin su Yaya Muhammad yay sanyi. Duk sun tsaresa da ido.

    Ya cigaba da faɗin, “Naji matuƙar fargaba da tsoro a lokacin da su Yaya Muhammad sukace bazasu amshi kuɗin aikin nan ba, dan ina tare da su batare da sun san ni ɗin wanene ba. Tabbas da basu amsaba Ummi bazan yafema kaina ba. A yau a kuma yanzu zan sanar daku wanene *_Master_*. Na zaɓi wannan lokacinne domin samarwa ƴan uwana kwanciyar hankalin shiga sabuwar rayuwa. Amma kafin sannan zan sake tabbatar muku Muhibbat tana hannuna”.

     Duk da dama shi suke zargi maganar ta dake su matuƙa. Musamman da labarin ya canja salo zuwa Isma’il da Shuraim da Master duk abu guda ne.

       “Kuyi haƙuri, badan na ƙuntataku na ɗauketa ba. Nayi hakane domin kuɓutar da ita”. 

     Wata nannauyar ajiyar zukata suka sauke kusan a tare. Ummi ta kai hannu ta share hawayen da suka ziraro mata har cikin ranta tanajin nutsuwa da ƙaguwar son jin wanene shi?.

         “Aliyu Ibrahim Hikima shine sunan mahaifina. Shahararren ɗan kasuwa da sunansa yay shura matuƙa a wasu shekaru da suka shuɗa. Sunan mahaifiyata Maryam. Auren soyayya sukai da mahaifina duk da dangin mahaifiyata basa so sam. Ba komai yasa basa son auren ba sai dan mahaifina bashi da komai a lokacin. Su kuma mutanene masu dukiya. Dagewar da mahaifiyata tayi akan sai shi ne yasa babanta yarda ya bashi aurenta. sai dai ya tabbatar masa babu shi babu ita.”

        Ya saki ɗan murmushi da cigaba da faɗin, “Ko’a jikinta ta amince da sharaɗin, saboda son da takema mahaifina bashi da iyaka. Anyi aurensu babu wani shagali aka mikama mahaifina. Dukansu basu damuba, dan su dai burinsu ya cika kawai. A farkon zama sun fara rayuwa mai cike da ƙuncin talauci da fatara, amma sai soyayyar da sukema juna tai matuƙar tasiri wajen mantar da su hakan. Shekararsu biyu a wannan hali na matsi da kakana ya sakasu batare da sun sani ba. Dan kuwa duk wata hanya da mahaifina zai samu kakana ke tosheta wai duk dan mahaifiyata ta magantu. Amma sai akai rashin sa’a ko’a jikinta. Sai ma shi Abbana ne kan damu musamman idan yay dubi da ga gidan data fito. Dan ƴar gata ce sosai Mamy na a gidansu, sannan ita kaɗai iyayenta suka haifa. Rayuwa ta musu tsanani sosai, gashi babu ciki babu alamar samuwarsa. Fahimtar komai zai iya lalacewa yasa mahaifina ɗauke Mamy na suka bar garin. Wannan tafiya itace sanadin canjawar komai.”

        “A yayin tafiyarsu sukai gamo da wani dattijo wanda alamu suka tabbatar da ba ɗan ƙasar nan bane. Dattijon nan shine ya fahimci akwai damuwa da talauci tare da su, dan ko kuɗin mota ma basu da isashe. Shine ya biya musu kuɗin mota na inda zaije, dan ya fahimci su kansu basu san ina suka dosa ba. Tafiya mai nisan zango ta kaisu wani gari dake akan gaɓar barin ƙasa. A garin suka kwana wajen dattijon nan daya hanasu matsawa ko nan da can, washe gari da safe ya sake basu umarnin su bishi. Mahaifina bashi da wata mafita banda ya bisan, da yake lokacin duniya na bacci azzaluman basuyi yawaitar yanzun ba. Sun sake yada zango a ƙasar Niger. Inda sukai kwanaki biyu anan dattijo ya kammala harkokinsa. Koda ya sake tabbatar musu gaba zasuyi basu damu ba, suka nuna masa amincewarsu. Yaji matuƙar daɗin yanda suka aminta da shi babu bincike ko nuna shakku”.

        “Bara dai karna jaku da nisa. Daga ƙarshe Iyayena sun tsinci kansu ne a ƙasar haihuwa ta wannan dattijon. Tun a tarbar da akai musu suka fahimci dattijon nan da ko sunansa bai sanar musu ba ƙasurgumin mai arziƙi ne. Yayinda suka isa katafariyar daular sa kuwa sai mamaki ya kamasu na dalilin zuwansa ƙasarsu, dan kuwa dai ya fito ne da ga gidan sarauta mai faɗa a ji da tarihi. Dattijo yasa an karrama rayuwarsu da basu muhallin zama mai tsafta. Bayan kwana biyu sun huta ya nema jin labarinsu. Mamana taso a ɓoye. amma sai babana yace su faɗa masa gaskiya kodan karamcin da yay garesu. Wannan dalilinne ya sakasu fayyace masa komai na rayuwarsu har barowarsu gida. Ya nuna tausayawa a garesu da ga ƙarshe ya ɗauka mahaifina ya ɗaura akan dukiyarsa. Amana da jarumtar da Abbana ya nuna wajen tsare dukiyar da nuna gaskiya yasa Dattijo yarda da shi, harya maidashi babban yaronsa makusanci, komai ya koma hannunsa. Wannan abu ya baƙanta ran ƴan masarautarsu ƙwarai da gaske. Harma da sauran yaransa da ke hidima ma dukiyar kafin zuwan su Abbana. Ƙiri-ƙiri suka ɗauka karan tsana suka ɗorama Abbana, kullum cikin masa gorin shi din baƙon haurene suke.”

        Rayuwa ta sauyama iyayena. Dan cikin ƙanƙanin lokaci dukiya ta bunƙasa garesu. Basu da wata matsala sai ta rashin haihuwa da tsangwamar mutane. Haka suka cigaba da haƙuri da juriya na tsahon shekaru har ALLAH ya azurtasu da samun cikina. Sunyi matuƙar farin ciki, irin wanda baki bazai misalta ba. Hakama Dattijo Isma’il yayi farin ciki tamkar shi za’aima haihuwar, dan shima bai taɓa haihuwa ba. Bayan cikina ya cika watanni tara aka haifoni, inda naci sunan dattijon nan wato Isma’il. Sai dai kallon mahaifi da babana ke masa yasa sukemin alkunya da suna Muhammad Shuraim.”

      Na tashi ɗan gata a wajen dattijo Isma’il da mahaifana. Yayinda tsiraru a cikin jama’ar masaruta ke sona. Wasu ko yanda suka tsani mahaifana haka suka tsaneni duk da ƙanƙantar shekaru na. Shekarata uku a duniya Abbana ya maido mamana ƙasarmu ta haihuwa saboda bazai juri tsangwamar da ake musu nima aimin ba. Dangi sunyi murna, sun kuma sha mamakin ganin ya kuɗance lokaci ƙanƙani. Dan yama take kakana ya shanye dukiyar da suke ƙinsa a dalilinta. Koda ya ajiyemu komawa yay ya cigaba da lura da dukiyar dattijo. Daga ni iyayena basu sake samun wani cikin ba har na kai tsahon shekaru takwas, kafin mamana ta wayi gari da ciki. Nanma sunyi murna, hakama ƴan uwa, musamman ma ni. Cikin mamana na watanni uku ciwo ya kai dattijo Isma’il ƙasa, wanda ake zargin sammu akai masa. Mahaifina shine ya koma jinyarsa, dan ƴan uwansa kowa ya noƙe, burinsu kawai ya bar duniya suhau kan dukiyarsa har matansa.”

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button