Uncategorized

TAKUN SAKA 28

           “Dattijo Isma’il ya riga yasan da wannan tun ba yanzu ba, dan haka a wani dare ya zaunar da mahaifina cikin dauriya ya sanar masa ɗunbin dukiyarsa daya tattare ya killace batare da sanin masu jiran ya wuce su hau kai ba. Gaba ɗaya ya mallakama mahaifina wanann dukiya, sannan yay masa umarni da ya bar ƙasar bayan ya damƙa masa fuskokin jabu (Facemask) guda uku yace koda ya dawo ƙasar haihuwarsa ya cigaba da amfani dasu shi da mamy na da ni dan yasa ƴan uwansa zasu bibiyesa bazasu barsa ba. Mahaifina yayi kuka sosai a wanann dare, kuka irin wanda ɗa ke yi yayin rasa mahaifa ko yin nesa da su. Shidai dattijo Isma’il nasiha yayta masa da addu’oin fatan alkairi da gamawa da rayuwa lafiya. ALLAH sarki rayuwa ashe nasihar ƙarshe ce, dan kuwa a safiyar wannan ranar aka wayi gari da rashin dattijo Isma’il. Abbana ya shiga ɗimuwa matuƙa harma ya rasa ina zai saka kansa. Yayinda tsoro ya kamashi ganin yanda matan dattijo da danginsa tun kan akai gawarsa harsun fara rigima akan dukiyar da suke tsammanin ya bari. Ana kai gawar dattijo Abbana ya silale ya baro ƙasar da dukiyar daya mallaka masa bisa umarninsa. Inda yabar baya da ƙura. Dan kuwa dattijo kashi uku ya raba dukiya yabar musu kashi guda kawai. Wannan dalilin yasasu farga da rashin Abbana da wuri saboda sunce a nemosa yay musu bayanin ina sauran dukiyar take.”

       “Abbana ya dawo ƙasarsa ta haihuwa cikin zuri’arsa, sai dai kuma anyi rashin sa’a dangin dattijo nacan na bincike a kansa har suka gano inda yake. A nan kuma ɓangaren Abbana koda ya dawo ni kaɗai suke sakama Facemask idan za’a kaini makaranta ko zan fita waje. Su mutane a tunaninsu baƙon yaro mukai, shiyyasa basu taɓa kawo hankalinsu a kaina ba. komai ya sake canjawa. hankalin iyayena ya kwanta, sunan mahaifina ya sake yin shura musamman akan harkar kasuwanci. A ƙanƙanin lokaci ya zama bashi da abokan mu’amula sai manyan mutane, a ƴan uwa kuwa dama zuwa yanzun iyayensu duk sun rasu, babu wasu shaƙiƙai na jini dan shima tamkar Mamyna shi ɗaya aka haifa a gidansu, baima san mamansa ba.”

     “Lokacin da cikin Mamy na ya shiga watan haihuwa a lokacin komai ya sake canjawa, dan kuwa dai dangin dattijo sun ƙaraso ƙasar nan batare da sanin Abbana ba. Hasalima har sun kammala bincike akansa da inda yake.”. Hannu ya kai ya ɗauke ƙwallar da suka cika masa ido, kafin ya cigaba da faɗin, “Ranar da bazan taɓa mantawa ba. Rana mafi ciwo da zafi, ranar da duk nisan tarihi bazai gogeta ba a gareni itace ranar juma’ar dana rasa iyayena duka. Dan kuwa dangin dattijo da taimakon wasu hatsabibai sukaima gidanmu dirar mikiya. Hankalin mahaifina ya tashi, dan ya tabbatar tamu ta ƙare, amma sai cikin jarumta ya faɗama mahaifiyata duk tsanani karta buɗe ƙofa shi zai fita shi kaɗai, idan kuma zamanta da nawa bazai yuwu ba ta tabbatar ta fita zai janye hankalinsu, ta kuma sakamin facemask ɗin wajen dattijo itama ta saka nata. Mahaifiyata na kuka ta shiga roƙonsa kar yaje amma sai ya lallasheta da bata ƙwarin gwiwa. Ya fita garesu, inda suka zagayesa da mahaukatan makamai tare da basa umarnin fiddo musu dukan dukiyarsa. Gane dangin dattijo da yay ya sakashi yarda zai basu, tare da roƙonsu idan ya basu su barsa da ransa cikin iyalansa. Sun nuna sun amince, dan haka Abbana ya tattara kuɗaɗen ya basu harma da dukkan takardun kaddarori suna kammala amsa ɗaya da ga cikin dangin dattijo cikin bada umarni yace (Master kashe shi). Shigar wannan furuci a cikin kunnena ya sani fashewa da kuka a cikin dakin da muke maƙure ni da Mamy. Na mike a razane da nufin fita Mamy ta hanani. Kuka nake ina fisgewa har na samu damar guduwa na leƙa ta jikin window. A dai-dai wanann lokacin wanda aka kira da Master yasa yaransa suka kama Abbana suka danne yay masa yankan rago cikin rashin tausayi da rashin imani duk da kwata-kwata shekarunsa bazasu gaza ashirin ba a duniya”.

     “Kuka na fasa wanda ya jawo hankalinsu ɗakin da muke. Cikin bada umarnin ɗan uwan dattijo ya ce muma a kashe mu. Hankalin Mamy da ya fara gushewane ya dawo jikinta saboda tuna wasiyyar Abba. Cikin rawar jiki ta kama hannuna muka fita ta ƙofar baya su kuma suna ƙoƙarin buɗe ƙofar. Kasancewar a cikin falo komai ke faruwa muka fice a gidan ina kuka mahaifiyata na kuka jini na zuba a jikinta ga tsohon ciki. Tafiya muke ta ceton rai dan kuwa suna buɗe ƙofa sukaga alamar mun fita ta ɓarauniyar hanya sai suka take mana baya. Fahimtar ana binmu yasa Ummi cikin galabaita ta ce naje kawai. Kaina nake girgiza mata ina kukan ni bazanje ko ina na barta ba. Sanin taurin kaina yasata juriyar cigaba da tafiya batare da mun fahimci inda muke jefa ƙafa ba dan gari yayi shiru kasancewar dare ya tsala. Sosai Mamyna ta sake galabaita, saboda alamar haihuwa data zo mata gadan-gadan, ga jini na zuba mata. Yanke jiki tai ta faɗi, na durƙusa a gabanta ina kuka da kiran sunanta ta tashi, amma ina bazata iya ba. Cikin amincin ALLAH mutumin da muke a ƙofar gidansa yaji kukana ya fito. (Sun kashemin Abbana da Ummina baba sun kashesu) na faɗa cikin kukan daya saka Hankalinsa tashi ya kamani ya muƙar tare da ɗaukar Mamy gaba ɗaya ya shige damu cikin gidan. A daidai lokacin su dangin dattijo da ke binmu suka iso ta ƙofar gidan tare da ƴanta’addan hayarsu. Sai dai rashin tabbatar da muna anan ɗinne ya sasu wucewa dan baban nan daya taimakemu ƙarar tahowarsu ta sakashi sa hannu ya toshen baki. Wucewarsu da kamar mintuna biyar naƙudan mamana ya tsananta. Baba ya rasa yanda zaiyi dan bashi da mata. Haka yanaji yana gani ya sama Mamyna ido harta haihu. A galabaice ta damka amanarmu a hannunsa tare da roƙonsa da cewar ya kaimu gidan marayu dan zama anan gidan bazai bamu tsaro ba tunda ta tabbatar dangin dattijo Isma’il sun gama sanin komai a kammu da kamanina na gaskiya tun kan suzo garemu. Tana gama faɗar haka ta bar duniya.”

        “Na ɗanɗana raɗaɗi biyu na zafin rashi a dare ɗaya a kusan lokaci ɗaya. Ga kuma ƙani Ummi ta haifamin. A taƙaice dai a ɓoye dattijo ya samo maƙwafta sukai jana’izar mamyna a washe gari da safe, bayan wata tsohuwa ta suturtata. Bani da wayo sosai dan shekarata tara kacal. Amma na shiga damuwa sosai. Dan ma kallon jaririn Mamy na ɗan ragen jin zafi. Wasiyyar Mamyna tasa baba ɗaukarmu a washe garin da Mamy ta cika kwana uku mu da shi duka muka koma gidan marayu gudun kar makasan su gano inda muke. Ashe shima bai taɓa haihuwa bane shiyyasa matansa duk suka gujesa.”

         “Mun koma gidan marayu da zama inda baba ya tambayeni sunan da zai sama jaririn Mamy na ce Habib. Babu musu baba yay masa huɗuba da suna Habib. Nine na cigaba da rainon Habib a gidan marayu, tare da matar da ke kula da mu da baba wanda a yanzu shine tamkar mahaifina. Karku manta inada facemask ɗin da dattijo Isma’il ya bama Abbana. Kuma ni kaɗai nake sakawa su basa amfani da ita. A kuma lokacin da zamu fito Mamyna ta ɗauka ta sakamin ita. Kuma koda muka zo gidan marayu ban cire ba na cigaba da amfani da kayana batare da kowa yasan ainahin fuskata ba”……………✍

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button