TAKUN SAKA 31

*_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
_________________________
*_Chapter Thirty one_*
………..Tab ɗinsa data yasar a ƙasa ya ɗauka ya bar wajen batare da yako kalleta ba. Hakan yasa taɗan sauke ajiyar zuciya tana fitowa da ga bayan Baba Saude data ɓuya. Kallonta baba Saude da ke murmushi tayi. Cikin son tsokanarta tace, “Anya baza’ai ƴar gida ba anan ɗiyata?”.
Cikin rashin fahimta Hibba tai ƴar dariya tana zama. “Baba Saude ina kwana”. “Lafiya lau”. Ta amsa mata da kulawa. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Ke da baki da isashen lafiya ya kamata kizo ki karya”.
Kallon su Habib da suke tattare plates ɗin da suka gama tayi. “Baba nifa lafiyata lau ALLAH. Waya ce miki banda lafiya ne?”.
Da sauri gudun karta ɓaro musu aiki Khalid ya ce, “Baba saude yau dama tuwon rana akai mana miyan ɗanyen kuɓewa”. Hankalinta ta maida garesa da faɗin, “To shikenan Khalid inhar suma duk suna so ai sai ayi.”
A mamakin Hibbah da ke kallonsu sai gani tai sun hau murna harda rawa. Baki ta ɗan taɓe tana mikewa, a ranta ko tana ayyana taɓararsu.
Duk yanda Hibba take dojema su Habib a wannan yini sai da ta saki jikinta da su ƙarfi da yaji, saboda yanda suke shiga lamarinta. Da ga ƙarshe sai gashi sun baje a falo suna hira tare cikin nutsuwa. Dan idan taso nutsuwar bazaka taɓa ɗauka ita bace. Ita kanta Baba Saude tayi mamaki. Takuma fahimci cewar gata ne kawai ke ɗawainiya da Hibbar.
Tare suka shiga kitchen ita da baba Saude sukai girkin rana. Bayan sun kammala ta fito ta koma sama. Salla tayi tai kwanciyarta sai barci. Da ga haka babu wanda ya sake jin ɗuriyarta har bayan la’asar. Dan koda ta tashi tai salla sai tai zaman shan kukan kewar ahalinta. Sai kusan biyar ta fito falon.
Kowa bata samu ba sai motsin baba saude a kitchen. Ta leƙa ta gaisheta tana tambayarta su Idris. Computers room ɗinsu baba sauden ta nuna mata. “Suna cikin can, suna dawowa da ga sallar la’asar babana ya kaɗasu can kinsan su ƙwararrune na na’ura mai ƙwaƙwalwa anan suke wasu ayyuka nasu da nima bansan kona minene ba”.
“Na satar kuɗaɗen mutane mana”. Hibbah ta faɗa a hankali batare da baba Saude tajita ba. Ɗakin ta nufa, ganinsa a buɗe yasa ta danna kai da sallama. Shi kaɗai da ke tsaye a kansu ya ɗago ya kalleta. Su Salis kam duk sun duƙufa aikin gabansu. Haɗa idon da sukai yasata janye nata ta maida kansu Adam. Yanda suke sarrafa kwamfitocin sun matuƙar birgeta. Dan sai ka ɗauka bada hannu suke sarrafa keyboards ɗin ba tsabar ƙwarewa da yawan dannawar da suke a koda yaushe.
“Guys are you ready?”.
Musbahu ya faɗa da ɗan ƙarfi. A tare suka haɗa baki wajen faɗin yes. Sosai Hibbah ta nutsu wajen kallonsu matuƙa, suko sunata aikinsu cikin maida hankali garesa har aka kira sallar magrib. Ganin ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa da faɗin, “Lokacin salla yayi” ya sakata juyawa zata fita.
“Hii Auntynmu”.
Salis ya faɗa yana ɗaga mata hannu. Juyowa tai tai wani ɗan yaƙe tana ɗaga masa hannu sai kuma ta gimtse fuska da hararsa. Ya haɗe hannayensa alamar tuba fuskarsa ɗauke da murmushi kamar yanda suma sauran sukeyi mata. Sake tsuke fuska tai ta fice batare data sake tankawa ba.
Tunda Hibbah ta koma ɗakinta taketa faman kai kawo na mamaki. Gashi takadari shu’umi, amma a ɗan kwanan da tai a gidan biyu ta fahimci sam baya wasa da salla baya barin su suma suyi wasa da ita. Anya bazata amshi tayin yimasa aikin na wata guda ba kodan ta yo leƙen asirinsa. Dan bata da wani babban burin da ya wuce ganin ta damƙa su Abba da dukkan mabiyansu ga hukuma kodan kuɓutar da kanta da ahalinta garesu.
Wannan shawarar da ta yankema zuciyarta ne ya sata fitowa bayan sallar isha’i. Cikin sa’a kuwa ta samesa a falon saman shi kaɗai zaune yana aiki a system. Gefe kuma yana shan baƙin shayin da keta tashin ƙamshi. Sarai ya ganta ta gefen ido, sai dai a ransa yana mamakin ganin yanda ta fito a nutse tamkar ba ita ba. Mamaki bai karasa kasheshi a zaune ba sai da ta zauna a ƙasa tana faɗin, “Yaya Master barka da aiki”.
Duk yanda yaso shareta sai ya kasa. Batare da ya kalleta ba yace, “Kina buƙatar wani abu ne?”.
Duk da ta ɗanji haushin yanda yay ɗin sai ta danne. Cikin sanyin murya da kwantar da kai tace, “Dama zance maka ne na amince zanyi maka aikin. Amma dan ALLAH nima ka cikamin alƙawarin barina naje ga ahalina bayan na kammala. Sai dai ina roƙonka abu biyu. Ka haɗani dasu ko waya muyi dan su sami nutsuwa nima na samu. Sannan dan ALLAH karka sakani aikata abinda ba dai-dai ba. Kaga ni ɗin marainiya ce, sannan kuma mace. Ɓacin sunana ko fitar tambarin fuskata da sunana ga al’umma tamkar daƙile wata ƙofar mutunta sunan gidanmu ne. Sannan zaiyi wuya ace na sami mijin aure bayan wannan shine fatan kowacce ɗiya. Abu na ƙarshe bana fatan a tada mahaifina a nuna masa ni matsayin ƴar ta’adda bayan ban nema masa mutunci da addu’a ba. Sai kuma dan ALLAH ka zamemin garkuwa na mutuncina a gidan nan duk da tunda na shigo babu wanda ya nufeni da ko maganar banza a cikin yaran ka da ya shafi iskanci. Kaima ka ɗan rage kusancin da kake son haifarwa a tsakaninmu kodan gujema sharrin shaiɗan”.
Tunda ta fara magana ya gagara cigaba da danna system ɗin. Karo na farko a rayuwarsa da ya sakata a jerin masu hankali da nutsuwa. Ko sanda yake zuwa gidansu da farko kallon miskila yake mata sangartacciya. Sai daga baya ya fahimci kawai gatane data tashi a ciki ya sata zama kamar wata sakalya ga shegen baki……..
“Dan ALLAH”.
Ta faɗa cikin katse masa tunani. Numfashi yaja ya fesar tare da janye idanunsa a kanta. Kujerar gefensa ya nuna mata alamar tazo ta zauna. Babu musu ta mike ta zauna kanta a ƙasa dan batason kallon idanunsa tsoro suke bata.
“Muhibbat!”.
Ya kira sunanta a karo na farko tun shigowarta gidan.
Ta amsa masa da “Na’am” a nutse kai kace ba ita ɗin bace ba.
“Shekararki nawa ne?”.
“Sha tara”.
Ya gyara zamansa yana fuskantarta sosai. “A shekarun nan naki nasan dai kinsan minene aure tunda har kika ambacesa, sannan kina zuwa islamiyya kinsan minene addininki”.
Kanta ta jinjina masa, tana wasa da yatsun hannunta.
“To Alhmdllh. Da farko dai naji duk bayaninki da amincewarki. Na biyu inason ki kauda duk wani tunani akan waɗan nan yaran da kike gani a gidan nan. Duk da nasan zuciya bata da ƙashi bana fatan wata rana da wani a cikinsu zai miki kallo irin wanda kike tsoro. Dan kasantuwar hakan na nufin tabbas zan iya halaka yaro kona nakasashi.” Ɗagowa tai ta ɗan kallesa saboda jin abinda ya ce. Sai dai ganin shima ita yake kallo ne yasata maida kanta ta duƙar.
Cikin halin ko in kula da yanayin nata ya cigaba da faɗin, “Bazance miki na amince da kowa a cikinsu ɗari bisa ɗari ba, sai dai ina musu ƙyaƙyƙyawan zato kasancewar su ɗin tarbiyyata ne. Nasan su ba muharramanki bane ba, hasalima bai dace na kawoki cikinsu ki zauna ba. Sai dai nayi hakanne bisa ga lalura da kuma sanin nan ɗin shine kawai yafi tsaro a gareki. Abu na ƙarshe inason ki sani ni ɗin mijinki ne”.