Uncategorized

TAKUN SAKA 31

       “Miji?”.

Hibbah ta faɗa a kiɗime.

     Kansa ya jinjina mata yana tamke fuska fiye da da saboda sanin halinta. “Kamar yanda naje neman aurenki gidanku ban ɗakkoki nan ba sai da na biya sadaki aka ɗaura da shaidu”. Ya ƙare maganar da ɗakko lap-top ɗinsa dake gefe ya danno mata video. Tabbas taron ɗaurin auren yayinta ne. Dan yana saka play da fuskar Yaya Umar ta fara cin karo, wanda yake sanye cikin kayan da suka saka ranar ɗaurin auren. Yanata waya alamar baima san ana ɗauka ba. Cikin tsumar da jikinta ke mata ta cigaba da kallo har aka gama ɗaura auren duka yayunta dasu Zahidah aka ɗaura nata a ƙarshe ita da ango mai suna Muhammad Shuraim Aliyu. Kuma hakan na nufin shine kenan. Tunda Baba Saude ta tabbatar mata sunansa ne.

     Kanta ta shiga girgizawa hawaye na kwaranyo mata. Ta buɗe baki kamar zatai magana sai kuma ta kasa kuka ya kufce mata. Tashi tai da gudu tabar falon zuwa ɗakinta. Ya bita da kallo harta shige. Baki yaɗan taɓe da ɗauke kansa irin ko’a jikinsa ɗin nan.

★★★★★★★★

          A gidan Ummi kam yau anguna sun gwangwaje daren alkairinsu ga matansu. Inda suka samu ƙyaƙyƙyawan sakamako daga tsare kai ga zina. Basu ɓata rayuwar ƴar kowa ba suma ALLAH ya kare matayensu ya basu cikakku nagartattu.

      Kowanne ka kalla a wannan safiyar zaka fahimci ransa fes yake da shiga sabuwar rayuwa. Ita kanta Ummi farin cikin nasu data gani ya sakata a farin ciki itama. Tasan ko basu faɗaba sunga wani abu na daga sakamakon haƙuri.

        Sun so zama da ita su tattauna akan Isma’il tace karsu damu tana kan nazarine game da shi. Suma ta basu dama kowa yaje yay nazari yazo mata da sakamako. Amma kar suyi gaggawar yanke hukunci akan ƙaddara balle fara TAKUN SAƘA da shi game da sirrin da UBANGIJI ne kawai yaso basu haske shiyyasa ya aiko Isma’il ɗin a cikinsu.

     Badan sun so ba sukai shiru. Dan ita ɗin ba abar rainawa bace a garesu.

★★★★★

       Da ga ɓangaren haji Halilu ma dai sai a hankali. Gaba ɗaya ya maida kansa kiɗimammen ƙarfi da yaji. Ga momy na addabar rayuwarsa akan ciwon Junaid. Ta dage sai an kamo Isma’il an miƙa ga hukuma. Hakama su Ummi.

      Ya yarda da nemo Isma’il dan haka ya bama jami’an tsaro dama. Sai dai damuwar itace babu ko hoton Isma’il bakuma su san ɗan inane ba shi ɗin. Gashi su Ummi da za’a iya samun bayanai da ga garesu an memsu an rasa. Dan haka suka saka aka kama baban hafsat da baban Zahidah da Sheikh Aliy akan sunsan ina su Ummi suke tunda ƴaƴansu aka aurama yaƴan Ummin.

       Su kuma an kaɗa dambu da taliya sunce sam basusan ina Ummi take ba. Batun tarewar yara kuwa wani gida suka nuna akan nan aka kai amaren. Sheikh Aliy dai uffan baima ce musu ba. Kwarjininsa kuma da sanin shi ɗin wanene ya hanasu kausasa harshe garesa. Koda akaje gidajen aka duba sai aka samu gidajen da Abban ya kama musu hayane su zauna da ƴaƴansa.

      A take ƴan sanda suka fahimci wani abu su ummin suka ƙulla shiyyasa sukai ɓaddabami. Sai kawai suka duƙufa neman su ummin suma bayan Isma’il.

★★★★

          Suma su A.G tunda suka mikama Master sunaye da accaunt Numbers nasu suka koma gefe suna jiran sakamakon aikin da suka bashi. Yayinda a zahiri suke tsakkiyar manyan mutane masu kishin ƙasa ana ta tattauna ta ina za’a nemo master da tawagarsa. Ɗari bisa ɗari an yarda da su. Saboda yanda suke nuna kishi da taɓarɓarewan tsaron ƙasar da son ganin an hukunta masu irin halin master. Ta ko ina sun kafa tsun tsare sune dai????????.

★★★★★★★★

       Tun daga wannan ranar Hibbah ta shiga wasan ɓuya da kowa na gidan. Idan ka cire baba Saude da kan ɗan ganta lokaci-lokaci. Master ya share kamar ma ya manta da lamarinta. Dan gaba ɗaya hankalinsa ya tattarune yanzu akan aikin da yasa gaba. Su kansu su Habib abinda ya janye hankalinau kenan ko zaman gidan basayi yanzun. Dan lokuta da dama ma da ga ita sai baba Saude suke yini a gidan. Sai weekend ne Hibbah tahaɗu da yarinyar da baba Saude ke riƙo wadda tsintarta tai ta rena tun tana jinjira gashi har tana da shekaru biyar yanzun. Sosai Hibbah taji daɗin ganin yarinyar, dan gata ƙyaƙyƙyawa da ita ga wayo. cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu harta manta da wasu ababen halitta su Master a gidan. Sai dai kuma a duk minti cikin bin kwaƙwƙwafin komai take na gidan batare da ko baba saude ta farga ba.

     A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai ga Hibbah da sati biyu a gidan Master. Yau tsahon kwanaki goma sha biyu kenan bata sakashi a idonta ba. Ba kuma ta haɗu da su Zaidu ba, dan suma basa ma kwana a gidan, daga baya ne kuma ta fahimci shima uban gayyar baya kwana a gidan kusan sati guda kenan.

        Yau ma kusan la’asar bayan ta gama sharɓar kukanta ta tashi ta gyara fuskarta ta fito wajen Baba Saude. Zamanta baifi da mintuna goma ba ya shigo falon da sallama ciki-ciki. Sam Hibbah bata wani jisa ba saboda ta maida hankalinta gaba ɗaya wa tv ne. Sai da taji baba Saude ta ce, “A’a babaa barka da dawowa”.

      Saurin juyowa tai jin abinda baba Saude ta faɗa. Dai-dai ya ɗago idanu yana gaishe da baba Saude. Haɗuwar idanun nasu waje guda ya saka Hibbah saurin janye nata ta maida ƙasa. Dan gaba ɗaya ta koma cikin yanayin rashin walwala a ƴan kwanakin nan, shiyyasa duk wani rawan kan nan nata da tsiwa kamar an mata ruquyya a kansu. 

     “Ina yini”.

Ta faɗa acan ƙasan maƙoshi batare da tayi tunanin zaima jita ba. Duk da yaji ɗin bai amsa ba. Yana dai cigaba da kallonta dan a kallo guda ya fahimci bata a cikin walwalarta. Cigaba da takowa yay inda suke. Batare da ya janye idanun nasa ba ya ajiye ledar hannunsa a saman centre table tare da janye idanunsa da ga kan ta ya maida ga baba Saude.

       “Baba kuyi haƙuri mun barku gidan shiru”.

     “A’a babu damuwa wlhy babana. Ai da yake inada abokiyar hira dan ma dai kwanakin nan nakega kamar tana da damuwa ne. Ban dai tambayeta ba dan kar na ƙara ɗaga mata hankali”.

      “Karki damu baba baƙunta ke damunta kawai”.

        “Ai yaci ace baƙuntar nan ta tafi babana. Amma zan ƙara dagewa wajen ganin na gusar da ita.”

       Hibbahr ya sake ɗan kalla da janye idanunsa. Batare da yace komai ba ya nufi sama. Sai da ya hau kusan steps biyar sannan ya tanka. “Ki sameni anan”.

    Ya faɗa batare da ya juyo ba.

Ganin bata motsa ba harya gama hayewa ne yasa Baba Saude kallonta. “Muhhibatu tashi kije babana na kira kinji”. Dan ita duk zaton ta ƴana da alaƙa da Hibbahr ne. Tunda ita shaidace a kansu bata taɓa ganinsu da matan banza ba har ƙannen nasa. Dan haka take kyautata masa zato.

        Mikewa Hibbah tai a hankali ta nufi saman hawaye na ciko mata idanu. Babu wanda take muradi da ƙulafucin gani kamar Ummi da su Yaya Muhammad. Tsaye ta samesa a tsakkiyar falon da alama ita yake jira. Ta samu damar ƙarema bayansa kallo tunkan ta ƙaraso saboda da ya juya mata baya. Kaya na masa ƙyau, musamman ƙananun kaya da take ganinsa da su kawai dan bata taɓa ganin yasa manyan kaya irin na hausawa ba. Kullum cikin shigar kananun kaya yake tamkar dangin masu jajayen kunnuwa. 

      Jin idanu a kansa ne ya sashi juyowa. Saurin duƙar da kai Hibbah tayi ƙasa. Cikin dakewarsa yace, “Baki iya gaisuwa bane?”.

      “Ina yini?”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button