Uncategorized

TAKUN SAKA 32

 *_Typing????_*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_Chapter Thirty Two_*

……….A ɗan firgice Hibba ta farka da ga gajeran barcin da Master ya sakata na dole. Waige-waige ta shigayi cikin ruɗanin ganinta a sabon waje. Yayinda wani irin tsoro da tsantsar firgici ke bayyana akan fuskarta. “Na shiga uku wa kuma ya kawoni nan?”.

      Ta faɗa muryarta na rawa alamar son yin kuka……..

      “Hi aunty queen!”.

Da sauri ta juyo tana kallon Habib mai maganar da maɗaukakin mamaki, sai kuma ta ɗan sauke ajiyar zuciya koba komai taga wanda ta sani, duk da suma ɗin ba wai abin yarda bane. 

       “Barka da yamma aunty queen”. Aka sake faɗa ta ɗayan gefenta. Khalid ne yay maganar dan haka ta ɗan hararesa. Ta buɗe baki zatai magana Master ya fito ta wata ƙofa waya manne a kunnensa. Ga kofin baƙin shayi a hannunsa. Baiko kalli kowa a cikinsu ba ya kai zaune bisa kujerar dake kallonsu yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

      Yayinda yake amsa wayar cikin rashin sakewa da ƙasaita. Hararar gefen ido Hibbah tai masa tana gulmarsa a cikin rai. Ta dubi su Habib da suka nutsu a tsaye. “Ni ku bani abinci yunwa nakeji aka satoni nan”.

      Cikin gumtse dariya Khalid yace, “Mi zaki ci to?”.

       “Komai ma”. 

   Barin wajen yayi. Babu jimawa sai gashi ya dawo da damammiyar madara da kwalin cornflakes. Yaja ƙaramin stool gabanta yana faɗin, “Gashi auntynmu”.

       Komai batace ba. Sai dai babu musu ta zuba cornflakes ɗin batare data kalli inda Master yake ba, har zata kai baki kuma sai ta dakata. Ta ɗan saci kallonsa tana faɗin, “Khalid inji dai ba’a saka ka barbaɗa wani abun mutuwa ba ko?”.

       Idanu ya ɗan waro waje. “Abin mutuwa kuma Aunty Queen? Wazai saka miki abin mutuwa?”.

       “To na sani, tunda agabana ranar akace a bani maganin feshin ƙwari nasha”.

         Habib da Khalid suka dubi juna suna satar kallon Master daya gama wayar yana daƙilarta ne kawai alamar akwai abinda yakeyi, duk da yana jinsu yayi kamar baisan dasu a wajen ba. Cikin danne abinda ke taso musu Khalid yace, “A’a babu abinda aka saka miki aunty. D……”

        “Zaku wuce abinda ke gabanku ne? Ko zaku zauna surutu?”.

     Ya faɗa batare da ya ɗago ya dubesu ba. Kafinma ya rufe baki sun bar wajen. Hibbah ta taɓe baki da cigaba da shan cornflakes nata dan yunwar takeji da gaske. Cigaba da abinda yakeyi yayi harta kammala bai dubeta ba. Sai da ta mike tana ɗan dafe kai ne ya bita da kallo.

      “Ina ne kitchen?”.

  Ta tambaya cikin kwantar da murya dan ita tayi alƙawarin daina tsiwa har sai ta gano wanene shi.

       Da yatsa ya nuna mata yana miƙewa. Ficewa yay da ga falon yana sake ɗaura wayar a kunnemsa alamar wani kiran yayi. Gaba Hibbah tai itama inda ya nuna mata. Bata wani jima ba ta fito tana gyara hijjab ɗin jikinta da batasan ta yanda akai ta sakashi ba, balle inda ta samoshi. Sake komawa tai kan doguwar kujerar ta kwanta ranta fal tunanin dalilin da yasa aka kawota nan ɗin kuma?. Harga ALLAH hatsabibancinsa na bata mamaki. Mutum ne da sam baka taɓa gane ina ya dosa balle manufarsa. A ɗan zaman da tai da su sosai ta fahimci wasu halaye na mutanen kirki tattare da shi. Sai hakan ke yawan raba mata hankali daga ɗabi’unsa na zahiri da kowa ya sani. (Zan dai sake nutsuwa na fahimci guy ɗin nan).

     Ta ayyana a zuciyarta cikin yarda da kai. Cigaba tai da tunane-tunanenta har ta fara jiyo hayaniyar su Adam da batasan ta ina suka fita ba. Jin hayaniyar tasu na cigaba da tashi sama-sama ya sata miƙewa dan zaman shirun baya mata daɗi, ga jikinta duk babu ƙarfi kanta kuma na mata ciwo kaɗan-kaɗan. Ta riga ta saba da baba Saude acan da Sharifat. Duk da ba sanin ko’ina tai ba haka ta fito compound inda take jiyosu. Girman gidan ya bata matuƙar mamaki, an wadatashi kuma da abubuwa kai kace ba a cikin gurguwar ƙasarnan tamu bane ba. 

       Tsaye tai tana kallon su Habib da ke faman buga basket ball. Haka kawai taji wani nishaɗi har fuskarta na bayyana murmushi. Ta shagala sosai a kallonsu ta hango wata ƙyaƙyƙyawar mage na fitowa da ga ɗakin maigadi. Tana son mage, tsoronta da yaya Usman keyi a gida ya saka Ummi ta hanata ajiyewa. Magen ta nufa tana faɗin, “Woow Cutie”. Tai maganar tana kaiwa duƙe ta ɗauka magen. 

       Master da ke kallonta da ga can inda yake ta gaban ruwan da aka ƙawata na swimming pool ya ɗan yamutse fuska ganin ta ɗaga magen ta rungume a jikinta tana murmushi tamkar ta samu ɗa. Sam shi bai wani damu da mage ba amma ba tsoronta yake ba, baya son dai sam ta taɓa masa jiki. Ɗauke kansa yay ya cigaba da  danna wayarsa.

      Hibbah ba lura da Master tayi ba, dan haka ta cigaba da hidimarta da mage cikin nishaɗi. Lokaci-lokaci takan ɗaga kai ta kalli su Salis. Wani ɗan zare ta ɗauka tana ɗagawa sama magen na tsalle zata kamo. Hakan yasaka Hibbah ƙyalƙyalewa da dariya tana tafiya da baya-baya magen na binta da son kama zaren.

     Tana gab da isa inda Master yake Idris ya farga. Zungurin Musbahu da ke kusa da shi yayi. Musbahu ya ɗan waro ido dan ganin abinda ke shirin faruwa. Yay saurin ɗaga hannu zai fargar da Hibbah da ke gab da zuwa inda Master yake Idris ya rufe masa baki.

        “Kai malam waye ya saka. Barta dan ALLAH, wlhy ni so nake babban yaya ya amsheta matsayin matar gaske bawai ta wucin gadi ba. Dan sun matuƙar dacewa.”

     Musbahu da ya gamsu da bayanin Idris ya jinjina kansa yana janye hannunsa. “Ashe bani kaɗai nake da fatan nan ba.”

    “Sosai kuwa”

Cewar Idris cikin bada tabbaci.

            A ɓangaren Hibbah kam gab take da kaiwa ga Master da gaba ɗaya hankalinsa nakan wayar dan abu mai muhimmanci yakeyi a ciki. Khalid da sai yanzu idanunsa ya kai shima ya ɗan zaro ido. Da sauri ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Aunty Queen bayanki”.

       Tsorata Hibbah tayi, dan duk zatonta wani abun cutarwa ne, musamman ganin yanda Khalid ɗin yayi maganar. Tai ƙoƙarin juyawa da sauri sai dai ta rigada tazo gab da shi, ga magen ta ɗane ƙafarta saboda kama zaren da tasamu damar yi. Uban tsalle ta doka da ƴar ƙarar tsoratan data fargar da Master. Cikin zafin nama ya riƙo hannunta ganin tayi baya zata kai ƙasa, sai ko gata gaba ɗaya a kansa.

       Hawar masa ƙafa da magen tayi ne shima ya sakashi saurin ɗaga ƙafarsa, ga Hibbah ɗare-ɗare a cinyarsa. Yanda yayi ɗinne kuma ya sake firgitata ta duƙunƙunesa gaba ɗaya har yana sakin wayarsa a ƙasa babu shiri. Cikin sauri su Idris suka shiga jan hannun juna suna barin wajen ransu fari tas..

     Master ya sake rumtse idanunsa da ƙarfi jin yanda Hibbah keta sake cusa kanta a ƙirjinsa da dabaibayesa. Ga mage da kamar ance ta nane musu sai tsale-tsallenta take. Dole ya miƙe gaba ɗayansa dan bayason magen na taɓa masa jiki. Hibbah ta fasa ƙara da son sake ruƙosa jin zata faɗi ƙasa, sai dai abisa tsautsayi ta riga tayi baya da yawa, idan kuma takai ƙasa tabbas zata cutu. Magen ya yakice a jikinsa yana ƙoƙarin kai ɗayan hannunsa ya riƙo nata ganin gaba ɗayanta zata sulmiya cikin ruwan ne.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button