TAKUN SAKA 32

Maimakon ta riƙe hannun sai ta damƙe rigarsa gaba ɗayansu suka antaya a cikin ruwan ji kake tanjamm????????.
Yanda ruwan ya bada ƙara yasa su Habib fitowa kusan duk a guje sukayo wajen pool ɗin har maigadi. Sam Master bai iya ruwa ba. Hasalima bai cika son ganin babban ruwa ba, kona swimming pool ɗin idan ya zauna wajen saboda son sanyi baya yarda yay masa kallon daya haura sakanni yake ɗauke ido. Idanko damina tazo duk wani rashin jinsa nutsuwa yake saboda rashin sakewa, ko yaya ruwa ya dakesa sai yaji a jikinsa dan sai yayi ciwo.
Hankalin su Habib ya tashi saboda sanin bai iya ruwaba. Gashi basu da damar cewa zasu shiga ruwan saboda Hibbah dake tare da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci Master ya shaƙi ruwa, sai dai kuma ƙoƙarin son ceto Hibbah yake a zatonsa bata iya ruwanba itama. Duk yanda yaso hakan ta kasance ya gagara, dan harya fara galabaita. Hibbah kuwa tanata ƙoƙarin ganin taje gaɓa dan itama dai bawai ta iya swimming ɗin bane ba, amma ta fisa dan ta kuɓutar da kanta batare data fita hayyacinta ba. Ruɗewar data lura su Zaidu sunyi ne ya sata saurin waigawa bayanta tana ƙoƙarin sharce ruwan fuskarta. Idanu ta zaro matuƙa, dan Master harya fara yin ƙasa.
Da sauri ta koma bayan inda yake. Tasa hannu ta toshe hancinta tai ƙasa wai zata ɗagosa. Ina yafi ƙarfinta, amma tsabar ƙarfin hali tanata kici-kici cikin rawar jiki na tsoro, dan ta fahimci bai iya ruwa ba. Da ƙyar ta samu da taimakon su Habib data miƙoma hannunsa suka kama ta ɗagoshi, sai faman cije baki take dan ya mata nauyi a jiki, tana turawa suna ja har suka ɗagosa gaba ɗaya.
Ganin kamar bashi da rai yasa Hibbah fashe musu da kuka, dan gaba ɗaya kanta ta bama laifin. Ruɗewar da tai yasata fara danna ƙirjinsa kamar yanda taga Musbahu nayi. Amma babu alamar ruwan daya shaƙa zai fita.
Adam yay saurin faɗin, “Aunty Queen taimakon gaggawa ta baki Please”.
Ruɗewa ta sakata ranƙwafawa kansa ta ɗaura bakinta kan nasa, yayinda ta toshe masa hanci da yatsunta biyu, bada wani tunani ba ta shiga bashi taimakon gaggawa. Ganin taja numfashinsa na farko babu wani alama yasata jawowa a karo na biyu da iya ƙarfinta tana matse ido.
Gaba dayansa ya yunƙuro saboda tahowar numfashinsa mai haɗe da tari da ruwan daya shaƙa. Hannayensa duk biyu sukai sama, tana ƙoƙarin dagowa ya sake rungumota ta dawo kan ƙirjinsa. Tsam ya matseta yana cigaba da tarin ruwan daya shaƙa na fita.
Nannauyar ajiyar zuciya su Khalid duka shiga saukewa na godiya ga ALLAH. dan da gaske sun shiga tashin hankali. Sai mutsu-mutsu Hibbah take nason ƙwace jikinta amma ta kasa koda motsi. Sai da tarin ya lafa masa ne ya ɗan janye hanun daya dabaibayeta yana buɗe idanu da ƙyar. Cikin sauri ta miƙe a kansa duk kunya da takaici sun dabaibayeta. Ya ɗan kalleta ya maida idanunsa da sukai jaa ya lumshe.
Ganin ya saki Hibbahr su Salis da duk sukai ƙasa da kai tunda ya kawo numfashi duk sukayo kansa. Sune suka taimaka masa ya tashi zaune. Zasu kamashi ya mike ya girgiza musu kai alamar zai iya. Baya duk sukaja. Shi kuma yabi Hibbah dake jike da ruwa ta nufi hanyar falo da sassarfa da kallo. Mikewa yay da ƙyar yana dafe kansa da ke juya masa. Shima ya nufi falon su Habib suka take masa baya sunata jera masa sannu. Har cikin ransu kuma ganin laifinsu suke dan sun bada gudunmawa a wannan accident ɗin.
A falon suka iske Hibbah sai rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa. Duk tausayi ta basu, tayi tsumu-tsumu tamkar an tsamo ɓera a ruwa????????????. Shi kansa ta bashi tausayi, duk da bayajin ƙarfin nasa jikin shima gabanta ya ƙarasa. Babu zato Hibbah da duk kunya ta dabaibaye saboda yanda kayan suka manne mata a jiki sai ji kawai tai anyi sama da ita.
Da sauri ta harɗo hannayenta a wuyansa saboda wani Masifaffen kunya daya rufeta tashi a karo na farko tun zuwanta gidansa. Ta tura kanta akan ƙirjinsa da riga ta manne shima yanata ɗigar da ruwa.
Ƙin ɗagowa tai har sai da taji ya direta ta ɗan buɗe ido. Da sauri ta kalla inda ya kawotan shima ta kallesa. kafin ta ɗaga baki tai magana ya kammala dai-daita ruwan ɗumin ya saki ruwan shower ɗin ya sauka a kansu. Wani irin bahagon ajiyar zuciya Hibbah ta saki jin ruwan akansu. Ta rumtse idanunta da sauri tana juya masa baya ganin zai cire riga abinsa hankali kwance.
Juyawar tatace ta bashi damar cire duka kayan jikinsa ya bar boxer kawai ruwan na ratsa masa jiki kozai samu nutsuwar abinda yakeji na ƙutsa masa cikin ƙashi. Sai da yaji ya ɗan fara samun nutsuwa ne ya kashe gaba ɗaya, batare da yace komaiba yaja bathrobe ya saka. Tun kafin ya fita a toilet ɗin ya fara sakin atishawa a jajjere.
Ajiyar zuciya Hibbah ta kuma saki jin ya rufe mata ƙofar hawaye na gangaro mata. Gaba ɗaya kallon komai take tamkar a mafarki yau itace a banɗaki daya da namiji.
Jin sanyin na neman dawo mata a jikine ya sata zuwa ta sama ƙofar key ta fara zame nata kayan. Dan dole ne idan tana bukatar zaman lafiya tayi yanda ruwan zai ratsata ta kuma rabu da kayan gaba ɗaya. Hatta da gashin kanta ji take kamar ta kwashe ta yar.
Sai da taji tamkar fatarta zata ɗaye dan saukar ruwan dumin nan sannan ta kashe tana sauke numfashi da atishawa itama. Towel ya rage a toilet ɗin gashi guntu, bata da zaɓin daya wuce ɗauka ta sakama jikinta, ta sake jan karami ta naɗe kanta tana sakin atishawa da kallon facemask ɗin daya cire a fuskarsa. mask ɗin ta ɗauka tana jin takaicin kanta na juyawar da tai da tabbas saita ga face nashi yau. Jin atishawa zata halakata ya sata ajiyewa ta matse kayan data cire da nasa. Gefe kuma tana tunanin yanda za’ai ta fita a toilet ɗin da guntun towel ɗin?.
A ɓangaren Master kam rawar sanyi sosai yakeyi, da kyar ya iya daukar wani mask ɗin ya saka a face nashi. Gadon ɗakin dake a gyare ya haye yaja bargo ya rufa yana sakin atishawa da rawar ɗari.
Hibbah da taji kamar babu motsinsa ta ɗan leƙo kanta. Babu kowa a ɗakin dan haka tai tunanin ya fita dan bata farga da gadon ba. Sai da ta fito tsakkiyar ɗakin ya saki wasu tagwayen atishawa. Da sauri ta duba kan gadon saita ga a lulluɓe yake. Ajiyar zuciya ta sauke da saurin nufar Wadrobe ɗin ɗakin duk da bata tunanin samun kaya. Cikin sa’a taci karo da kayansa. Cikin sauri taja jallabiyar data fara gani ta zura a jikinta duk da ta mata yawa sosai. Tanayi tana juyawa ta dubesa wai ko zai kalleta.
★★
Da ga can falo su Habib nata kai kawon dafa masa ruwan zafi mai kayan kamshi, dan sun tabbatar a yanzu shine yafi bukata bisa taimakon farko. Su duka bakwai sun haɗu a kitchen ɗin abin tausayi da dariya. A haka dai suka haɗa Habib ya ɗakko ya nufo ɗakin nasa. Sai da yay sallama da knocking Hibbah ta amsa sannan ya shigo. Ganin yanda har yanzu a ruɗe yake ya bama Hibbah mamaki. Ta bisa da kallo lokacin da yake kaiwa durƙushe a gaban gadon saitin kan Master. A marairaice yake kiransa kamar zai saki kuka.
Master dake jinsa ya buɗe ido da ƙyar tare da kai hannu ya ɗan ja bargon daga saman kansa. Sosai idanunsa sukai wani irin kaɗawa jazur, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu dan ma mask ya tare abin tausayi da tsoro. Sosai gaban Hibbah ya faɗi ganin cikin kanƙanin lokaci ya fita hayyacinsa. Batare da Hibbah ta sani ba tuni ta karaso gabansu itama har rigar na neman harɗeta zata faɗi ta dai dafe gado.