TAKUN SAKA 32

Shayin Habib ya miƙa masa kamar zaiyi kuka. Da ƙyar Master ya mike ya jingina da fuskar gadon sai atishawa yake akai-akai. Habib ya zuba shayin a muq ya mika masa. Amsa yay babu musu yana matse idanu dan yasan shine kawai abinda zai taimakeshi a halin yanzun. Sai dai maimakon ya kai baki sai ya miƙawa Hibbah yana mata nuni data zaune a gefen gadon.
A yanayin da yake ne yasata kasa musa masa, dan ita sam bawai ta shiga wani hali bane, shi kansa ta fahimci kamar dai yanada wani ciwone da baya buƙatar shiga ruwa, musamman wannan da yay sanyi sosai, ko kuma halittarsace hakan. Gashi shi kuma ya shagesa da yawa. (Dama akwai mazan da basu iya ruwa ba?). Ta faɗa a zuciyarta tana satar kallonsa ta gefen ido.
Wani shayin Habib ya sake zubawa ya miƙa masa, amsa yay. Habib dake kallonsa cikin damuwa yace, “Salis yaje gida ya ɗakko maka kaya masu kauri. Akwai abinda kake buƙata bayan shayin?”.
Ƙasa yay da idanunsa ya ɗan kalli shayin ya ɗago ya duba agogon dake ɗakin. Ganin lokacin sallar magrib ma yayi sai ya girgiza masa kai kawai.
“Kuje kuyi salla”.
Yay maganar a hankali miryarsa harta canja launi tamkar ba shi ba.
Sannu Habib ya sake masa yana mikewa. ya dubi Hibbah da yake fatan ita babu komai da ga gareta. “Aunty ke bakijin komai ko?”.
Batare da Hibbah ta kallesa ba ta girgiza masa kai. “Alhmdllhi” Habib ɗin ya faɗa da nufar ƙofar fita. Shuru ɗakin ya ɗauka kamar babu kowa, ita dai Hibbah kanta a ƙasa zuciyarta na wasuwasi da saƙe-saƙen mike damunsa haka daga shiga ruwan da kwata-kwata basu gaza 30minutes ba a ciki? Dan gaba ɗaya yanda ya birkice ɗin zaka fahimci akwai damuwa da yake fuskanta game da hakan. To amma kuma a koda yaushe ai cikin warware ac yake kamar goyon larabawa shi baya masa illa kamar haka kenan? Kuma yana wanka, Kenan shima duk basa masa illah?.
Oho shi dai Master baima san tanayi ba. Dan shayin yake sha cike da dauriya, amma lokaci-lokaci yakan ɗan kalleta ya janye idonsa. Duk da alamu ya nuna yanajin sanyi sosai haka ya miƙe dan shan shayin ma ya ɗan bashi nutsuwa. Bayan ya buɗe wadrobe ya ɗauka kaya toilet ya nufa yayo alwala da ruwan zafi sosai ya canjo kaya. Gaba ɗaya yanda yake jinsa bazai iya fita massallaci ba, dan haka yay ma Hibbah nuni alamar taje tayo alwala.
Haka kawai ta tsinta kanta dajin nauyinsa. Dan haka babu musu ta mike tana faman naɗe rigarsa. Batai tunanin jiranta zaiyi zaman yi ba sai da ta fito ta gansa a zaune ya rufa da bargo idonsa a rumtse. Sai atishawa da yake cigaba da jerawa. Motsinta ya sakashi buɗe idon, ya miƙe batare da yayi magana ba yana tunanin abinda zata rufa tai sallar…..
Sallamar Salis ce ta sakashi sauke ajiyar zuciya. Hibbah ta amsa ganin shi muryar tasa tayi ƙasa. Itace ta bama Salis ɗin damar shigowa. Sai ko gashi da sabuwar sallama ɗauke da leda babba. Ya ajiye yanama Master daya koma bakin gadon ya zauna sannu. Kai ya jinjina masa kawai tare da miƙa hannu ya amshi ledar da faɗin, “Kaje kai salla”.
Cikin girmamawa Salis ya amsa. shi kuma ya buɗe ledar sai ga Hijjab da kayan Hibbah a sama. Hijjab ɗin ya miƙa mata yana mikewa. Amsa tayi ta saka. A karan farko ya ja musu sallar magrib, koda suka idar ran Hibbah fal mamakin jin yanda yake karatun sallar cikin nutsuwa da tabbatar da ashi ɗin yanada ilimin addini.
Bai wani samu nutsuwar addu’a ba ya miƙe dan jikinsa sai rawar sanyi yake. Ledan da Salis ya kawo ya buɗe, ya fiddo safa ya saka a ƙafarsa ya sake hayewa gadon yaja bargo. Sai dai kafin yakai kwance Habib yay sallama ɗauke da ruwan ɗumi. Yanzunma Hibbah ta amsa masa, ya shigo idonsa akan Yayansa da ya tabbatar yana cikin wani hali, sai dai shi mutumne mai juriya shiyyasa ba’a cika ganowa ba, amma yasan yana da raki idan yana ciwo kuma. Dan in yana ciwo koma musu yake kamar shine karamin sune manyan tsabar rakinsa, kai kace ba Master bane maiba su A.G ciwon kai da jami’an tsaro da manyan ƙasa????.
Ita dai Hibbah tana gama shan maganin da Habib ɗin ya bata ta mike tana faɗin, “Habib wane ɗaki zan zauna?”.
Habib da yasan gidan bawasu ɗakuna bane kuma ga halin da Master ke ciki na bukatar wani a kusa, dama idan yana ciwo shine ke zama tare da shi, tunda kuma gata yana ganin ai an wuce wajen. Mastern da yay kamar baisan sunai ba ya kalla. Ganin yanzun ma bashi da alamar cewa komai yasa Habib cewa, “Anan zaki zauna gidan babu ɗakuna sosai, sannan yana bukatar wani a kusa da shi, kiyi haƙuri ki zauna anan doctor na zuwa dubashi”.
Ta buɗe baki zatai magana. Yay ma Habib alamar yaje. Babu musu ya juya ya fita. Fuska ta ɓata sai dai babu damar yin magana. Komai baice mata ba shima yaja bargo ya sake rufe har saman kansa. Tamkar Hibbah zata fasa kuka ta cigaba da zama a saman abin sallar har lokacin isha’i, a ranta tana tunanin ita tayaya ma zata iya zama da shi a ɗaki guda. Batai zaton zai tashi sallar ba sai gashi ya miƙe da alama ma ba barcin yakeba daman. Yanzun ma shine ya ja musu sallar isha’i kowa yay shafa’i da wutirinsa. Gadon ya sake komawa ya kwanta, baifi mintuna biyarba Habib yazo da doctor. Wani farin dattijone mai cike da kamala. Gaishesa tai ta cigaba da kallon yanda taga yana tarairayar master ɗin. Sai faɗa yake masa a tausashe akan shiga ruwa da yay bayan yasan minene matsalar jikinsa da ruwan sanyi da kuma rashin iya ruwa.
Shi dai Master komai baice ba sai wani langabewa yake. Doctor yay masa allura yana faɗin, “Kaga yanzu babu abinda kafi buƙata daga dakatawar wannan rawar sanyi kamar ɗumin jikin mutum. Gashi kaƙi aure Shuraim. Last daka samu irin wannan matsalar Habib ne ya baka ɗumin jikinsa lokacin bai kai haka girma ba. Amma ni yanzu bansan yanda za’ai ba”.
“Doctor Ibrahim mutumin kirkine kuma ɗan amanarsu. Wanda suke kallo tamkar uba a yanzu, duk da ya musu nisa saboda bai cika zama ba. Shiɗin ɗan uwa ne ga baba wanda ya taimaki mamynsu kuma ya riƙesu. tunda Mastar na yaro shine yake kula da issue ɗin ciwon nasa na rashin son ruwan sanyi da likitoci da yawa suka tabbatar masa yanada alaƙa da jininsa ne. Sam jikinsa baya son ruwan sanyi, shiyyasa ya kasance ko alwala zaiyi sai da ruwan ɗumi, amma kuma yana son sanyin ac duk da shima yakan bashi wahala wasu lokutan.
“Uncle ai yayi aure fa”.
Habib ya faɗa a hankali yana satar kallon Master. Cike da mamaki Doctor ya kalli Master ɗin dake kallon Habib cikin alamar waya tambayeka”.
“Shuraim da gaake ne?”.
Doctor yay tambayar yana raba hankalinsa biyu na kallon Master da Hibbah. Kai kawai Master ya ɗaga masa, sai kuma ya motsa baki a hankali yace, “Haka abin yazo babu shirine Uncle”.
Daɗi ne ya kama doctor Ibrahim. Ya shiga sakama Master albarka da Hibbah, dan shi da da farko harya fara zargin ko master ya fara neman mata ne duk da yaga Hibbah ƙaramar yarinyace. To amma yanda zamani ya sauya komaima zai iya faruwa. Ya nuna farin cikinsa sosai, tare da yi musu addu’ar zaman lafiya da zuri’a mai albarka. Da ga ƙarshe yay ma Hibbah bayanin yanda zata kula da shan maganin master ɗin tare da bashi ɗumin jikinta.
Ita gaba ɗaya ma tabar fahimtar yaren da yake magana. Saurarensa kawai takeyi da kunne. A ganinta tayaya zata bashi ɗumin jikinta tunda ba jini bane balle a ɗiba?. Harya gama ya miƙe zai wuce bata dawo hayyacinta ba. Sai da Habib ya kirata da ɗan ƙarfi sannan ta ɗago ta kallesa. “Uncle ne ke miki sallama”.