TAKUN SAKA 33
Sake fashewa da kuka Hibbah tai da komawa ta kwanta tana jan bargon har saman kanta. “Ni wlhy ban yafe ba kwarto kawai”.
Karaf a kunnen Master dake fitowa a bayi alamar alwalar daya fara ihunta ya fiddosa yaje ya sako. Kobi takanta baiyiba dan kansa ciwo yake ya kabbara salla. Harya idar bata tashi ba. “Zaki tashi kiyi salla ko saina hawo gadon?”.
Ya faɗa a yanda yasan dole zataji tsoro. aiko zumbur ta miƙe, ta ƙudundune bargon har kanta tana sauka a gadon da gudu tai toilet. Saurin riƙota yay, dan yasan tana shiga da bargon toilet ya gama yawo. “K miyasa sam mai bai wadaci kanki ba?”. Yay maganar fuska a tsuke. Jikinta taso fisgewa ya zuba mata ranƙwashi tare da fisgota ta dawo jikinsa. Zata fashe masa da kuka yace, “Karma ki soma”.
Dolenta ta haɗiyesa kuwa. Jallabiyar sa daya cire mata jiya da daddare ya ɗakko mata. Yana ajiyewa a kan gadon ya juya ya fice a ɗakin yana danne dariyar dake taso masa. Raka bayansa tai da harara kafin taja jallabiyar ta saka. Koda ta shiga toilet ɗin saita yanke shawarar yin wanka. A gurguje tai wankan tayo alwala ta fito.
Salla ta fara gabatarwa kafin ta kimtsa cikin kayan da aka kawo mata. Har lokacin master bai dawo ɗakin ba. Dan haka ta fara gyara ɗakin. Tana gab da kammalawa Habib yazo yay kiranta. Sai da ta saka Hijjab sannan ta fito tana ta faman ɓata fuska. Duk zaune ta samesu a dining har uban gayyar daya canja kaya alamar yay wanka a inda bata sani ba. A kallo ɗaya zaka fahimci baida lafiya. dan idanunsa jajur suke ga wata ƙatuwar rigar sanyi daya ɗora. Gaisuwar da su Musbahu sukai mata ta amsa cikin ƙara ɓata fuska tana hararsu. Su dai murmushi kawai sukai dan babu damar magana boss na a wajen. Habib yaja mata kujerar kusa da Master dake karyawa, koda suka fito baiko ɗago ya kallesu ba abincinsa yake tsakura fuska a ɗaure, dan sam baya masa daɗi saboda mura. Dan ma yasa sun masa mai ɗan yaji da kayan ƙamshi ne.
“Nifa na ƙoshi”.
Ta faɗa kanta a ƙasa dan gani take kamar duk suna kallon abinda ya faru jiya da daddare a fuskar tata. A karon farko ya ɗago ya kalleta da jajayen idanunsa. Babu shiri takai zaune dan kallo ne na gargaɗi da babu alamar wasa a cikinsa. Kofi ya ɗauka da kansa ya haɗa mata shayi tare da zuba mata soyayyan doyan ya tura gabanta. Kallon juna su Habib sukayi cike da iya shegensu. Adam ya dafe saitin zuciyarsa yana wani lumshe ido irin dai ƙauna takai ƙauna kenan.
Hibbah kam kamar zatai kuka murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Dan ALLAH a rage yamin yawa”.
Bai ma nuna yajita ba, balle tasaka ran zai karɓi ƙorafinta. Sai ƙaramin bowl ɗin daya sha farfesun ya ture yana warwarar tissue ya goge bakinsa. Baya ya ɗanyi da kujerar yana ɗaukar wayarsa yabar dining ɗin. Su Idris na ganin haka sukai azamar cigaba da cin abincinsu dan sunsan yau akwai aiki tunda basu sami damar yi a daren jiyan ba saboda abinda ya faru. Ɓata lokaci kuma yana nufin amsar hukunci a wajen babban yaya.
Khalid ne da yaga Hibbah na tsakurar abincin yace, “Aunty Queen ALLAH ki maza dan yana kallonki”. Hararsa tai tana tusa doya cikin baki. “To shikenan ashe da rabon ai miki ɗura ko”.
Cokali ta ɗauka zata jefesa yay saurin mikewa yana dariya sauran ma na tayasa. Tashinsu a dining ɗin ya bata damar cigaba da cin abincin, sai dai kunnenta na jiyo mata bayanin da yake musu wanda bata fahimta ba cikin muryarsa da ke tabbatar da mura ta shakesa bana wasa ba. Har ya gama jawabinsa duk suka mike bata kammala ba. Sai da Habib ya fito yana sanar mata tayi maza ta kammala ita yake jira sannan ta mike. Ganin yana tattara kwanikan ta tayasa suka kai kitchen. Fitowarsu yayi dai-dai da fitowar su Salis cikin sabon shiri. Da kallon mamaki ta bisu ganin kowanne ya canja kamanni zuwa na daban. Zatai magana Master ya fito, dole ta haɗiye tata ta dauke kanta dan bata son koda wasa su haɗa ido.
Cikin dakewarsa da ƙasaita ya fara magana cike da gargaɗi. “Ku kula, komai kanƙantar matsala ku sanar dani. Khalid kai da Salis zaku tafi a napep. Idris da Musbahu ku hau mashina. Idan komai ya dai-daita ku sanar dani muma zamu taho. Musbahu ka tabbatar duk layin da zaka shiga ya zamto mai tsayi ne, kamar na masu amsar ATM ko Customers care ”.
“Insha ALLAH sir”.
Musbahu ya amsa cike da girmamawa. Kallonsu kawai Hibbah take tamkar ta samu television. Mamaki bai nema halakataba sai da taga sunkai zaune a falo sunyi addu’a nema nasara ga UBANGIJI kafin su Salis duk su fice a barta ita da sauran sai shi. Batare da ya kallesu ba yace. “Ku kuma ku biyo ni”
_______________________________
☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????☀️????
*_K’AMSHI,K’AMSHI RAHAMA NE MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA SU SUKA SAN MUHIMMANCIN DA K’AMSHI YAKE DASHI MUSAMMAN A WAJAN MAI GIDA ,_*????????????????
*_Zafafan turarruka masu zazzafan k’amshi hade da wasu irin manyan sirrika na mallaka cikin sauki ba boka ba malam hajiya , Zaki jefe tsuntsu biyu da dutse d’aya , domin zamowa star azuciyar mijinki_*????????????
*_nasan dai kunada labarin mashahuriyar Mai Saida kayan k’amshin Nan Wanda akafi sani da *HUMKAM GIDAN K’AMSHI* *_a wannan karon ma ta sake kawo maku da sabbin kayanta masu abun al’ajabi Wanda da kud’i k’alilan zaku more zafafan turarruka Kuma ki shiga jerin Mata masu aji_*
*IDAN SARI KIKE BUKATA INA BADAWA SANNAN INAGYARAN JIKI CIKI DA WAJE SHIN KINA FAMA DA INFECTION INA HADA MAGANIN SA DA IZININ ALLAH KISHA KI WARKE*
*Kadan daga cikin kayan da muke dasu*????????????????????????????????????????
*BLACK KAJII*
shin kina bukatar turaren da Zaki turara gidanki ya dauke maki warin sanyi ya kwana biyu Yana k’amshi ,?ki saye black kajiji Zaki Gane banbancinsa da sauran wannan ba k’amshi kawai yake ba idan kina turara. Jiki dashi Yana maki maganin kala kala ciki kuwa har da na sanyi , nemi naki Kar ayi Babu ke☀️????☀️????????08132506044 HUMKAMINCENSE
*ANA WA HABIBY* Wannan harkan na oza room ne special turare Dan matan aure kadai yana dauke da abubuwa Wanda bazan fadesu anan ba sannan bashi kadai bane akwai Crazy powder da na ke hadawa dashi zakisha garin sannan kishafa turaren hmm
*SUDANESE HUMRA* Turare dake dauke da sirrika Mai DAUKAR hankali kamshin ya banbanta da sauran turare Hajiya babbar sirrine Wannan hadin manyan Mata 08132506044 HUMKAMINCENSE
*GLOWING OIL*
Wannan yasha bam bam da irin Wanda kuka Saba gani ,Yana kashe kuraje Yana cire tabo Yana maganin kezbi da duk wani matsalan fata ,stretch marks duk Yana ciresu ….
*MOWAR MACE*
turaren mowar mace turare ne da larabawa suke amfani dashi Wanda da yawa mutanenmu Basu San da wannan iccen ba Mai dauke da magani k’amshi da sauran abubuwan masu matukar amfani ga fata ba
Shi wannan iccen yanasa hasken fata yanasa fata tayi laushi da santsi sannan d’an alk’awari ne matuk’ar kina amfani dashi zai tsirga maki cikin fata ta yadda ko Bakiyi amfani dashi ba zakiji k’amshin shi na fita ta cikin fatar ki ,ke amfanin iccen mowar mace yanada yawa jaraba ko don gyaran fatarki , ????????????????????????????????????????
Muna gyaran jiki na amarya da uwargida zakizo har gida ayi maki gyaran jiki irin na Mata masu aji zakiyi kyau kiyi fresh ga kamshin da zai Kama jikinki????????????????????????