Uncategorized

TAKUN SAKA 33

    Waige-waige ta shigayi cikin falon sai dai babu alamarsa. Sautin muryar tasane kawai data kasa fahimtar da ga ina yake fitowa. Kuka ta fashe dashi tana komawa ta zauna a kujerar. Lallai ta tabbatar yau tana a tsaka mai wuya. Abinda takeji a labari yau shi hannunta zai aikata.

      “Kuka bazaiyi magani ba aunty Queen, duk wani motsinki dake anan tamkar akan idonsa ne garama kiyi kawai”.

     Habib yay maganar cike da lallashi. Kamar ta makesa shima takeji, shiyyasa taki tanka masa ta cigaba da abinda takeyi zuciyarta na kawo mata wani shawara acan gefe. Yarda da shawaran yasata share hawayenta ta maida hankalinta ga aiki kamar yanda Habib ke nuna mata shima yanayi.

      A ɓangaren Master kuwa sun isa banki a tsohuwar motar da Adam ya tuƙasu. Adam ne ya taimaka masa ya fito a motar shi a dole ga dattijon da yaci duniya jiki yay laushi. Yana gaba Zaidu na biye da shi yana zuga surutu da kyalƙyala dariya irin dai garorin nan yan bani na iya na gefen alhaji. Shiko Master sai wani gaftarar goro yake yana ƴar dariya da bama Zaidun amsar wasu zantukan nasa.

     Gaba ɗaya kallon garori securitys ɗin bank ɗin sukai musu. Bayan an dubasu babu alamar wani abun ashha tare da su aka basu damar shiga. Yanda Zaidu ke zabga surutu Master na dariya yasa mafi yawan mutanen dake akan layin tura kuɗi da amsa kallonsu, wasu na musu dariya wasu na musu kallon ƙauyawa ne. Master dake lure da motsin kowa ya yafito wani gaye da ya tsuƙe cikin shigar manyan yara yanata bada iska. “Yaro yaka nan ka taimakeni, dan wannan mai bakin kamar bututun mai yanda bansan a ba shima ba bihim ya sani ba. Garama ni nayi yaki da jahilci lokacin da nake zuwa sarin atamfofi na manta wasu abubuwanne kawai.

     Gayen da gaba ɗaya ya gama ƙiyastama ransa tsuntsu da ga sama gasashshe ya karaso yana wani taɓe baki. Wata cimirmiɗaɗɗiyar takarda Master ya fiddo a aljihu ya mikama gayen. “Yarona duba mini nan, ƴan kuɗaɗena na kayan amfanin gona dana noma na sayar zan buɗe akawun na zuba. Nima jikana dake can kudu ya bani shawara amma yace na nema wannan daya rubuta min anan zai taimaka mini aimin komai na buɗe akawun din na zuba kuɗaɗena a ciki naje gida nai barci babu ruwana da takadarai”.

     A karon farko gayen ya dashare baki da faɗin, “Ai babu damuwa baba koni ma na maka. Kaga zomuje can sama acan ake buɗewa.”

    Babu musu Master ya amince. Suka nufi saman bene Zaidu na biye da su. Gaye da gaba ɗaya hankalinsa nakan jakar hannun Zaidu ya sami ma’aikaci guda sukayi magana. Form aka basu da zasu cike suka koma can gefe inda babu yawan mutane. 

     A ɓangaren master tun shigowarsu wajen yaga Musbahu, shima kuma ya gansa dan cike da ƙwarewa sukaima juna alama da ido. Kafin Master ya ɗauka ƴar nokia ɗinsa ya fara magana da ƙarfi har hankalin mutane na dawowa kansa. Wasu na dariya wasu na tsaki wasu taɓe baki. Dan kuwa dai garanci zam Master ke zubawa abinsa Zaidu na tayasa cikin kwakwazo shima.

     Da wannan damar gaye yay amfani wajen saƙala hannunsa a hankali ta ƙasan teble ya zuge jakkar hannun Zaidu. Rafar yan dari biyar ya jawo har sau uku ya tura aljihu, yayinda a gefe tuni Zaidu ya sane wayar gaye daya ajiye akan table shi kuma. A dai-dai nan Musbahu yazo a ɗan fusace yana faɗin, “Haba baba dan ALLAH kake magana a hankali mana. Nan fa ba ƙauye bane ko gida cikin banki ne”.

      Cire wayar Master yay a kunne yana zabgama Musbahu dakuwa. “Kaci gidanku dan bantan ubanka. Anki ayi a hankalin idan lahirace nan ɗin jefani a wuta. Mara mutunci takadarin banza.”

     Yanda Master ke masifar yasa mutane fara bashi hakuri da nunama Musbahu kuskurensa na kodan furfurar Master ɗin ya kamata ai ya tauna harshensa yay masa magana ta hankali. Yayinda wasu kejin daɗin abinda Musbahun yayi. Ga Zaidu da tuni ya zurama Musbahu wayar gayen nan a aljihu yana nunashi da dan yatsa alamar bama ogansa kariya. Yanda suke abun baka isa tunanin suna da wata alaƙa ba. Musbahu ya fice a wajen a fusace saboda securitys da sukazo suka tasashi gaba. Yayinda suke bama Master dake matsar kwalla haƙuri.

     Sai da wajen ya samu nutsuwa Gayen nan ya cigaba da cikema Master form yana tambayarsa. Yayinda Master ke amsa masa cikin raba hankalinsa. Dan nokia ɗinsa yake ta dannawa wai yana neman lambar jikansa daya sakashi zuwa ya buɗe akawun……….

    Anan bangaren Hibbah kam aiki take yanda Habib ya nuna mata hankalinta na ga ɗakin da suka kwana. Habib na cewa su ɗan dakata ta miƙe wai zatayo fitsari. Ɗakin ta shiga ta maida key ta kulle ranta fal farin ciki, dan tayi alƙawarin saita buɗema su Master aikin da suka tafi yi. Wadrobe ta nufa ta fiddo wayar da taga ya ajiye a ciki yau da safe, cikin sa’a kuwa ta ganta. Koda ta ɗakko a kashe take, cikin rawar jiki ta kunnata sai ko gata ta kawo. Wani ɗan tsalle ta buga zuciyarta na mata canki in canka akan wayarwa zata fara kira ne. (Ta yan sanda) zuciyarta ta bata tabbaci. lambobi da yaya Abubakar ya taɓa sanar mata cewar na taimakon gaggawane da ga hukumarsu ta loda a wayar, cikin sa’a tanayin dialing kuwa ta shiga????…………..✍

(Hibbah????????????????????????????).

        *_Kuyi haƙuri na zama sai a hankali sa kun haɗa da addu”a_*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????

#team ZAFAFA BIYAR????????????????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

 

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button