TAKUN SAKA 37

*_Chapter Thirty Seven_*……….Gaba ɗaya komai ya sake ɗaukar zafi a ɓangaren jami’an tsaro. Dan kuwa dai zuwa yanzu an tabbatar da ahalin su A.G suna hannun Master, sai dai kuma su su A.G sun tabbatar ma da duniya su Ummi basa tare da su. Kawai dai sun faɗa zasu kamasu domin master ya bayyana kansa. Kuma koda sukaje sai basu samesu a gidan ba kwata-kwata.
Wannan magana ta fara canja salon zantikan bakunan mutane harma da wasu a manyan masu fashin baƙi da ke faɗa aji na ƙasar. Da yawa suna faɗin anya kuwa babu wani abu a ƙasa da ke tsakanin su A.G da Master. Dan kuwa dai kalamansu suna kamanceceniya da wanda sukai amai suka lashe abinsu.
Master dai da duk keji da ganin komai bai sake ko tari ba. Tunda ya baje a falo dai ya duƙufa akan aikin da suma su Habib basu san na miye ba. Dan tundama suka shigo suka gaidashi duk sai suka koma ɗayan sashen inda yake kamar matsayin nasu har baba saude. Nan kuma ya zama nashine shi da iyalinshi su madam Hibbah mai zamani????.
Har kusan sha ɗaya na safe baiga Hibbah ta fito ba, shi kuma tunda ya fito a ɗakin bai komaba saboda busy da yayi. Sanin dalilin rashin fitowar tata ya sashi aika Habib kiranta lokacin da ya kawo masu breakfast. Tana zaune bakin gado bayan tayi wanka ta shirya harda gyara ɗakin akai knocking ƙofar. Cikin sanyin murya ta amsa tana miƙewa. Habib da ke tsaye da ga waje ya faɗa mata saƙon Master.
Tamkar tana gabansa ta kwaɓe fuska zatai kuka. Sai dai sanin babu damar tsallake kiran yasata warware ƙaramin mayafin jallabiyar kanta ta naɗashi.
“Good morning”.
Habib ya faɗa fuskarsa sam babu walwala. Ɗago kanta tai ta dubesa a karo na farko. Sai dai kafinma tace wani abu shi yayi gaba abinsa. Idanu taɗan rumtse tana haɗiye abinda ya zo maƙoshinta ya tsaya mai ɗaci. Sai kuma jikinta ya sake yin sanyi dan sam bataso taga mutum yana fushi da ita. Ko sadda tana gaban Ummi inhar tai laifi akai mata faɗa takan yi kuka ta manta, amma inhar taga Ummi cikin ɓacin rai da yayyenta saita kasa zaune ta kasa tsaye. Shiyyasa a yanzu ma duk ta firgice da fushin Master duk da tasan itace mai gaskiya.
Koda ta iso falon tsaye ta iske Habib na tambayarsa a haɗa masa abinci. Batare da ya ɗago akan takardun da yake dubawa a hannunsa ba ya girgiza masa kai da faɗin, “Barshi ta zuba”.
Kai Habib ya jinjina masa. “Okay, bayan hakan babu abinda kake buƙata kuma?”.
Yanzun ma bai ɗago ba ya bama Habib ɗin amsa. “Da ga yanzu itace zata ringa komai anan sashin”.
Daɗi ya ratsa zuciyar Habib. Ya ɗan juyar da kansa gefe yana murmushinsa da ya kasa ɓoyuwa. Ya haɗiye hawayen da ke neman kufce masa tare da duban Hibbah da ke tsaye tana saurarensu, dan kalaman Master ɗin ruɗar da ita sukayi. Ita dake fatan ya barta ta koma ga ahalinta ake kuma ƙirƙirarma aiki. Kallon karki sake cutarmin da ɗan uwa Habib ɗin yay mata, cikin nuna alamar rauninsa da bata dukkan amana. Batare da ya furta komai ba ya juya ya fice a falon tana binsa da kallo harya fice……
“Amana ya baki, duk da bayada tabbacin zaki riƙe masa. Dan a farko sun baki dukkan yarda babu shakku ko ɗar game da ke, amma sai kika sauya musu tunani….”
Master yay maganar har zuwa yanzu idanunsa da hankalinsa naga lap-top ɗin da takardun hannunsa. Idanunta dake kallon ƙofar har yanzu ta lumshe a hankali hawaye masu ɗumi suka ziraro mata. Takai tsugunne gabansa, “Nima iyayena sun yarda da kaine suka baka aure na da tabbacin bazakaci amanarsu ba amma sai kaci Yaya Master. Ka tausaya musu dan ALLAH dan Ummi na da ƴan uwana sunada rauni a kaina tamkar yanda ƴan uwankama kai ne rauninsu. Nima sune dukanin hope ɗin rayuwata. Bani da kuɗin dazan baka sama da wanda su Abba suka baka akan musu aiki. Sai dai inada kalaman roƙo da ban haƙuri a gareka kaji tausayin maraicinmu. Dan ALLAH a wannan gaɓar ka barni na koma ga ahalina su auramin wanda zuciyarsu tafi so da nake da tabbacin bazaici amanarsu ba……”
Tunda ta fara magana bai ɗagoba bai kuma daina uzurin gabansa ba sai yanzu. Idanunsa da har yanzu suke da kalar ja ya ɗago ya zuba mata. Duk son danne ɗacin dake kan harshensa da yayi ya gaza sai da ya bayyana acikin muryarsa. “Wanene shi?”.
A yanda yay maganar ne ya saka Hibbah ɗagowa ta kallesa cikin mamaki. Amma ganin ita ɗin yake kallo shima sai tai azamar maida kanta ƙasa cikin suɓutar baki da fashewa da kuka tace, *_“Yaya Isma’eel!”_*.
Numfashi Master ya fesar a hankali da lumshe ido….
Hibbah da bata san yanayi ba ta cigaba da faɗin, “Yaya Isma’il ya kasance abin alfaharinmu a tun farkon haɗuwa. Sannan shi abin so ne ga ahalina, sun so inama ace shine ya zama zaɓina tun farko, sai dai kash yazo a makare. A makaren da ka rigada kaima rayuwata kutse da yazo bisa alƙalamin ƙaddara ta, sai dai inaji zuwa yanzu a zuciyata tamkar bai makara ba. Gani gabanka gwiwa biyu ina roƙonka domin daraja da rahamar wanda ya haliccemu dan mu bauta masa, ka sawaƙemin aurenka dake kaina ka kuma maidani garesu. Sannan kayi haƙuri akan kuskuren da nai jiya gareka, nima bani da wani zaɓin da ya wuce hakan ne. Ahalina na cikin tarkon masifar ƙanin mahaifinmu, kai kuma ka kawoni nan ka ajiye kana musu aiki bayan suma burinsu ka kammala musu aikinne su ɓadda rayuwarka. Bazan tambayeka miyasa kake biye musu ba, sai dai zan sanar da kai kaima ba komai bane a garesu, lokaci suka ajiye domin ka. A zahiri dai kanada ibada da kiyaye dokokin ALLAH, amma a baɗini kana saɓa masa da babban laifi da ƙazantarsa da muninsa yasa ko’a kan harshe yake da ɗacin faɗa. Miyasa ka zaɓi saɓa masa bayan ni’imar lafiya da yay maka, ya baka ilimin addini, ya baka damar tarbiyantar da marayu, ya baka dukiyar da kake ci kake sha kake tufafi da shimfiɗa abubuwan jin daɗin rayuwa. Yayo ka a musulmi da baya barin lokutan salla biyar su wucesa sai da kuskure. Kaji tsoron ALLAH ka barsu tun kafin kai ALLAH ya barka……”
Duk yanda yaso cigaba da abinda yakeyi hakan ya gagara, dan kalamanta ba zuciyarsa kawai suka daka ba jinin jikinsa da ɓargonsa suke daddatsawa da tsinkawa a lokaci guda. Batare da ya shirya ba bakinsa ya suɓuce wajen faɗin, “Miyasa kike tunanin Isma’il ya fini nagarta?”.
Duk da bawai cikin lallashi ko taushi yay maganar ba sai Hibbah ta samu kanta da sakin murmushi tana ɗan dubansa. “Saboda bai taɓa cutar da mu ba. Kullum burinsa ya bama Ummi da mu kariya a wajen azzalumi Halilu. Bai taɓa tunanin rabani da Ummi na da su Yaya Muhammad ba. Kana ganin kuwa akwai sama da wannan nagartar wajen ƙayatar da yarinyar dake neman mijin aure?”.
Shu’umin murmushi shima ya saki da maida kansa ga aikin gabansa batare da yace mata komai ba. Sai da yaja kusan mintuna uku harma ta fidda ran samun amsa sannan ya bata amsar batare da ya kalletan ba yanzun. “Duk manta da waccan nagartar ta Isma’il ɗin da tunanin mi nake aikatawar ki riƙe Muhammad Shuraim (MASTER) dan a yanzu shine ƙaddararki. Na baki damar farko da zaki iya komawa ga ahalinki amma bakici jarabawar ba saboda gaggawa da ci da zuci irin wanda ke kai rayuwar da yawan mutanenmu ƙasa. Ba ko mai ne akema TAKUN SAƘA ba. Kamar yanda bada kowa ake kafa tubalin ginin TAKUN SAƘA ba. Dakinyi juriyar bina a yanda na ɗoraki da yanzu ba wannan matsayin muke ba. Amma zan miki alfarma a karo na biyu, zakije ga ahalinki, sai dai da sharaɗin tsarabar JINI NA”.