Uncategorized

TAKUN SAKA 37

         Hibbah da sam bata fahimci ma’anar furcin ƙarshe ba tai saurin jinjina masa kanta, “Na yarda da sharaɗinka, ko wanene jinin naka ka haɗani da shi muje wlhy baza’a taɓa cutar da shi ba koda da harara”.

        Kallonta yay cike da salon izza yana sakin wani shaiɗanin murmushi da ɗage gira sama. “Kin tabbata?!”.

      “ALLAH shine zai zama ahaidarmu”.

     Hibbah ta faɗa cikin sauri da kaguwa.

        “Da ga yanzu zuwa ko yaushe zaki iya ganin kanki gaban ahalinki da Isma’il ɗinki, amma ni minene makomar igiyoyin aure na dake kanki?”.

         “Zan tayaka addu’ar ALLAH ya baka wadda ta fini”.

       Maimakon amsa sai ya nuna mata kayan breakfast ɗin da Habib ya ajiye. Da sauri tace masa “Banajin yunwa”.

      “Nike ji ai”.

Ya bata amsa kansa tsaye. Hankalinsa nakan aikinsa. Batare da musu ba Hibbah ta haɗa masa komai gabansa tana satar kallon takardun dake barbaje a ƙasan carpet da bata san na minene ba.

        Shi dai duk da yana lure da kallon kurillar da takema takardun bai nuna ya gani ba. Sai ma turesu da yay gefe yaja abincin data haɗa masan ya hau ci hankalinsa kwance, kai kace baida wata damuwa. Sai da yasha kusan rabin cup na tea ɗin sannan ya miƙa mata. Kai ta girgiza masa batare da ta kallesa ba. Shima batare da yace komai ba ya kamo hannunta cikin nasa. Yanda yay ɗin ya tilastata ɗago idanu ta kallesa. Kofin ya ɗaura mata yana ɗan wani cizar lip da ƙanƙance idanunsa.

       Haka kawai kallon da salon nasa ya saka tsigar jikin Hibbah tashi. Babu shiri tai azamar amsar kofin shayin tana maida kanta ƙasa ta duƙar. Shima ɗauke kansa yay ya maida ga aikin da ke gabansa. Lokaci-lokaci yana amsa wayar da ita kanta batasan da su wanene ba dan maganar ma a cuɗe suke yinta.

        “Ciwonka ya daina zafi?”.

Ta faɗa cikin suɓutar baki daboda idonta daya sauka akan ƙafarsa dake harɗe ɗaya kan ɗaya tamkar wani jinin sarauta. 

         Duk da ya jita bai tanka ba. Hakan yasata ɗago ido ta ɗan dubesa. Ganin gaba ɗaya hankalinsa nakan system ɗin tai tunanin baiji ba, sai ta sake maimaitawa. 

      “Kin damu da ni har haka?”.

Ya faɗa batare da ya kalleta ba. Fuska ta ɓata, tare da kumbura baki ta cigaba da shan shayinta. “Daga tambaya”. 

         Kallonta ya ɗanyi ya ɗauke kansa. Yanda tai maganar kamar zatai kuka ne yaso bashi dariya. Amma sai ya gimtse abarsa yamaki cewa komai. Itama bata sake cewar ba harta kammala ta ajiye kofin zata miƙe. “A ina baba Saude take zanje wajenta”.

         “Aiki zakimin nima anan”. Ya fa ɗa yana nuna mata gefensa. A marairaice ta ce, “Zanfa gaisheta ne”.

      Maimakon ya bata amsa sai ya ɗakko lap-top da ke gefensa kalar pitch ya miƙa mata fuskarsa sam babu alamar wasa. Maganarsa ta dazun da yace mata rashin haƙurinta ya hanata zuwa wajen su Ummi ne ya sata zama a inda ya nuna matan. Koda ta kunna sai taci karo da hoton yayunta a screen ɗin harda yaya Isma’il. Babu shiri ta saki tattausan murmushi tana dubansa. “Nagode sosai ALLAH ya shiryeka kabar ƙwamushe kuɗaɗen mutane”.

        Harara ya zabga mata yana sake tsuƙe fuska. A zuciyarsa kuwa kokawa yake da dariyar dake taho masa yana mamakin shegen kauɗinta. Wato tsoron jiya harya barta ta dawo normal. “Idan kikai wasa yau babu accaunt ɗin dazai kwana da ko naira acikin yayunki har Isma’il ɗin naki ma”.

        “Wayyo, dan ALLAH kayi haƙuri wlhy wasa nake maka fa. Ai kaima kaga yanzu ka zama ɗan uwanmu ko”.

         Hararar ta ya sakeyi ya ɗauke kansa. Itama sai bata sake magana ba ta ɗauke kanta tana murmushi. Dan idan yay harara ita dariya yake bata. Sai da ta kammala dai-daita komai sannan ta dubesa. “Mizanyi to?”.

         Batare da yayi magana ba ya jawo takardun gefensa ya miƙa mata, sai kuma ya ɗan matso har jikinsu na haɗuwa. matsawa ta ɗanyi kaɗan, komai baiceba ya fara nuna mata abinda zatayi. 

       “Ni dai dan ALLAH karka sakani satar kuɗ…”

      Bata ƙarasa ba yasa yatsa ya ɗalli laɓɓanta. “Idan wannan baki bai daina damuna ba sai na cinyesa ALLAH”.

       Hannu tasa ta dafe bakin hawaye na ciko idanunta dan taji zafi. Shiko ya ɗauke kansa da cigaba da nuna mata ɗin kamar bai ganta ba. Sam ta manta da gargaɗinsa, yana gama faɗa cikin marairaicewa ta sake faɗin, “ALLAH bana son cutar kow…..”

          Tai saurin sake dafe bakin batare data ƙarasaba ganin yanda ya juyo. Kanta ta shiga girgiza masa idanunta na cika da ƙwalla. Lap-top ɗin da ke akan cinyarsa ya ajiye tare da juyowa gaba ɗaya. Babu shiri ta miƙe zumbur tana ajiye tata gefe tare da takardun zata gudu yasa ƙafa ya harɗota. Gaba ɗayanta ta faɗa saman cinyarsa. Ya cije baki saboda ciwonsa. Cikin daburcewa ta shiga son tashi a jikin nasa tana faɗin. “Dan ALLAH kayi haƙuri ALLAH bazan sake ba”.

        Bakin da ke maganar ya zubama lumsassun idanunsa da ke cike da mura. Sai yatsun hannunsa da ya tallafo ƙugunta har zuwa saman cikinta da yake ɗan motsawa. Zata sake yunƙurawa ta tashi ya sake nutsa hannunsa a saman cikinta dole ta koma ta sake zama tamkar zatai kuka. Kunyar duniya ta baibayeta tamkar zata halaka ta. Narkakken kallon da yake mata ya sata kai hannu zata rufe idonta dan rumtsewar ma ji take kamar bazai hanata ganin idanun nasa dake da matuƙar kaifi a gareta ba. Tana gab da kaisa saman fuskar tata ya riƙe. Da ƙarfi ta matse idanun da sake shagwaɓe fuska. “Nace fa kayi haƙuri”.

      Hannunta daya riƙo ya murza cikin nasa da wani salon da yasa jininta tsinkewa a lokaci guda. ya sake kusanto da fuskarsa gab da tata yana sake marairaice idanunsa “Ni idan akai min laifi sai na rama ai”.

       Ya faɗa cikin wata irin murya data saka Hibbah buɗe idanu ta kallesa babu shiri. Ganin fuskarsa gab da tata tai saurin sake maida idanun ta rumtse tana motsa baki alamar maganace a ciki babu damar faɗa. Fuskar tasa ya sake kusantawa da tata yana busa mata numfashinsa. Ji take tamkar ta fasa kuka dan yanayine da bata taɓa fuskanta ba a rayuwarta na kusanci da namiji irin haka. Tana ƙoƙarin buɗe idonta da son roƙonsa taji saukar laɓɓansa saman nata a bazata. Wata irin zaburar data bashi damar sake nutsata cikin ƙirjinsa ya rungume tayi. Tsabar rikicewar datai bama tasan ta saƙalo hanunta a wuyansa ba tana mintsini. Wata zazzafar ajiyar zuciya yaja yana sake narkewa bugun zuciyarsa na ƙara ƙarfi dan shima wannan shine karon farko a rayuwarsa daya tsinci kansa a irin wannan yanayin mai wahalar fassara da mantawa, daga shi har ita jikinsu rawa yakeyi, duk yanda yaso ganin yay control ɗin kansa ya barta ya kasa, sai ma sake ƙaimi yakeyi da canja salon tafiyar tasu zuwa wani abu daban.

     Firgici ya saka Hibbah fara jujjuya kanta hawaye na zirara, duk mintsinin da take masa baisa yajita ba balle ta samu kubutar da take fata da ga garesa, sai ma yazam tamkar ƙara masa ƙaimi take da mintsinin.

         Samun damar ɗaura hannunta da tai saman ciwonsa ta ɗan danna ya sashi janye jikinsa yana jan wani bahagon numfashi. Ba ƙaramin shiga tai cikin matsanancin firgici ba ganin yanda gaba ɗaya kamanninsa suka sauya mata lokaci ƙanƙani. Tai ƙoƙarin fisge jikinta da son tashi ya sake riƙota. “Na roƙeka dan ALLAH ka bari banaso, ka tausaya min karka ci amanata. Inason na cikama mahaifiyata burinta na tun farko akan auren Yaya Isma’i……”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button