TAKUN SAKA 40

Salis yace, “Ni nasan laifin daya aikata, amma ku jira dai ya dawo muji a bakinsa”.
Kansu duk suka jinjina alamar gamsuwa. Kafin su ajiye aikin gaban nasu a koma buɗe ledojin tsaraba cike da jin daɗi da farin ciki.
Habib kam koda ya fito can ya hango master ya ɗebo sauran ledan daya bari a motan. Nufarsa yay ya amsa suka sufi sashen nasa tare. Kamar yanda yabar falon a haka ya samesa. Ya kai zaune bisa kujerar 1seater yana ɗan dafe kansa da ke masa ciwo har yanzun. Yasan akwai issue ɗin jini tattare da shi, shiyyasa ciwon kan yaƙi barinsa sam. Bayansa ya kwantar jikin kujerar da zare mask ɗin fuskarsa ya ajiye, yana daura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, razanannun idanunsa ya zuba akan Habib dake tsaye kai a ƙasa.
“Miyasa ka aikata?”.
Yay maganar yana dauke idonsa a kansa ya maida ga takardun dake a saman centre table ya ɗebo su yana dubawa.
Habib da kansa ke ƙasa saboda girman laifin da ya aikata. Sanin halin yayan nasa akan buƙatar yin magana kai tsaye koda ta laifi ce, yace, “Itama taji irin raɗaɗin da kaji”.
Master da bai ɗago ba ya sake tamke fuska da cizar lip yana cigaba da aykin gabansa
“Yaushe na fara wasan banzan nan da kai?”.
Shiru Habib yay yana faman haɗiyar zuciya.
Master da yaji shiru ya ɗago ido ya dubesa fuska a tamke. “Ince da kai nake magana ko?”.
Yanda yay maganar aɗan zafafe yasa Habib ɗin girgiza masa kai. “Yaya hakan dazan mata ne kawai zaisa na huce da ga abinda ya faru, itama kuma zata kiyaye sake yin wani yunƙuri makamancin hakan.”
Idanu kawai Master ya zuba masa saboda mamakin Habib ɗin matuƙa. Shiko yaki yarda ya kallesa dan yasan yayi ba dai-dai ba.
Kansa ya sake maidawa ga takardun, “Hum aure kake buƙata kenan? Ko ka fara neman mata ne?”.
Da sauri Habib ɗin ya ɗago ya dubesa yana girgiza masa kai. “Wlhy Yaya ni ko ɗaya babu a raina. Kawai dai…..” sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba
Takardun hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba ɗaya garesa yana sake tsuke fuska irin yanda bai taɓa gani ba. “Ƙawai dai me?. ƙarya kakeyi, idan har baka neman mata taya kasan ka sakamin pills nasha dan naje ga mace koda babu niyyar haka a gareni.”
Habib da idanunsa suka kaɗa sukai jajur ya kai tsugunne gabansa. “Wlhy yaya ban taɓa aikata zina ba ka yarda dani, kamar yanda na faɗa maka kawai nayine dan karta sake tunanin kwatanta abinda ta aikata, sannan inason ku rayu har abada”.
“Kai da wa kukai shawarar aikata hakan a cikinsu?”.
“Ni kaɗai ne, dukansu babu wanda yasan abinda ya faru sai Yaya Abdull da ya bani”.
Idanu kawai master ya zubama Habib ɗin batare da ya sake cewa komai ba. Dama ya zargi babu wanda zaiyi wannan aikin garesa sai Abdull ɗin. Tunda aka ɗaura aurensa da Hibbah kullum cikin masa tsegumi yake su baby suke so da wuri. Habib da yaji yay shiru ya ɗago ya dubesa, shi kaɗai ne ya san ainahin fuskarnan a cikinsu, dan haka bai wani damu da ganinta a yanzu ba. “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri. Nasan nayi kuskure tunma kan na aikata hakan. Inason naga kunyi zama irin na kowaɗanne ma’aurata da ita. Bana son ka rabu da ita saboda ƙyawawan halayyarta. Duk da ƙarancin shekarunta tasan kanta matuƙa kuma tanada tarbiyyar da kowanne irin nagartaccen namiji zaiso ta kasance uwar ƴaƴansa. Mu ɗin nan marayune, daga mace tagari kawai muke saran samun zuri’a mai albarka da zamu sake ginawa. Wadda zaka fara ginawa kuma itace ginshiƙin da zata riƙe tamu mu duka bakwai ɗin”.
Harararsa Master yay, da alamar dai ya huce ya ɗauke kansa. Matsowa Habib yay jikinsa ya ɗaura kansa bisa ƙafafunsa. “Please yaya karka rabu da ita dan ALLAH, inaji a raina idan tasan kai ɗin ko wanene zata sakko ta fahimceka ku rayu tare”.
Lumshe idanu yay bai tankaba nan ma. Shima kuma Habib bai janye kansa ba. Kusan mintuna biyu yaja ajiyar zuciya da furzar da numfashi, a hankali ya kai hannunsa bisa kan Habib ɗin ya shafa. Habib da wani farin ciki ya mamayesa ya miƙe da sauri ya rungumesa yana dariya. “Thanks you Mastern mu. I love you so much”.
Karan farko Master ya rankwashi kan Habib ɗin yana murmushi. “Mara kunya tashi mun a jiki tunda ka sadaukar dani ai.”
Cikin shagwaɓa Habib yace, “A’a Yaya ba duka na bataba fa. Ita rabi mu rabi.”
Nan ma murmushi kawai yayi baice komai ba. Sai da ya miƙe batare da ya dubesa ba ya nufi hanyar bedroom ɗin da Hibbah ke ciki yana faɗin, “Kaje ka sanar musu kowa ya nemo matar aure nan da wata biyu”.
Idanu Habib ya zaro, kafin yace wani abu Master ya shige. Wata shaƙiyyar dariya ya saki yana haɗiye sauran maganar a ransa ya juya ya fita da gudu dan kai rahoto.
Master da ke jiyo dariyar Habib ɗin baima san murmushi ya kufce masa ba shima. Ya ɗan girgiza kai yana ƙarasawa cikin ɗakin da sallama a bakinsa. Shiru babu motsin komai alamar barci Hibbah keyi har yanzun. Ya zare jacket ɗin jikinsa yana ƙarasawa gaban gadon ya zauna ta gefenta. Babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kwanciya. Sam bayajin ƙarfi da daɗin jikinsa dauriyace kawai. Dan bashi da burin daya wuce ya tattare aikin nan ya ɗauki matarsa suje su huta. Bargon da take ciki ya ɗan janye da kai hannunsa saman goshinta. Zazzaɓin ya sauka, a yanda numfashinta ma ke fita kawai ya isa tabbatar da hakan. Yaji daɗi har cikin ransa, fasa tashinta yayi dan karya takaloma kansa wata rigimar, ya ɗauka ledar daya shigo da ita ya sake fita. Babu jimawa ya dawo ɗauke tea. Zama yay yasha tare da maganinsa. Shima yay shirin barci ya haye gadon yana sauke ajiyar zuciya…………✍????
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]