Uncategorized

TAKUN SAKA 49

     Sassanyan murmushi ya saku da ɗago fuskarta ya sumbaci goshinta. Kasancewar Habib a wajen ya sashi daurewa bai tsotse janbakin ba. Bai kuma sake magana ba har suka isa wajen taron daya gama cika fam da nutane.

     Tarba ta musamman ta mutunci suka samu. tare da wajen zama da aka tanada dominsu. Ba’a wani ɓata lokaciba wajen fara gudanar da taron daya tara manya-manyan mutane. Inda aka gabatar da abubuwa masu yawa tare da kyaututtuka ga su Master. Aka kuma tayasa murnar aure da kowa ke ɗauka yanzune yayisa. Daga haka akaci akasha taro ya tashi lafiya.

        A yanzu kam dole Hibbah tabi su Ummi suka koma gida tare dan ƙarasa shirin miƙata gidanta nan da anjima. Dan acan ɗinma sun baro baƙi sosai dan ma su Mama Jiddah nan dasu Ummansu Zahidah.

      Kamar da wasa sai gashi anyi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan su Hibbahn, anci ansha an rakwashe an ƙwalle musamman su Habib da suka jone da Ammar sukasha shaftarsu. Zuwa takwas na dare kuma aka haɗu a babban hall ɗin da aka tanada domin gudanar da liyafar cin abinci. Anan ɗin ma ba ƙaramin zauta Master gayun na Hibbah yayi ba. Dan gaba ɗaya ta wani canja masa tamkar ba ita ba. Itama kanta gayun nasa ya matuƙar ɗaukar hankalinta danko sanye yake da shadda ƴar ubansu dataji ɗinkin zamani mai ɗaukar hankali. Anci ansha su Habib sun cashe a filin rawa sai kace wasu ƴan daudu????. Tun Master na hararsu harya shiga sahun masu dariya duk da ƙoƙarin dannewa da yay tayi. Ƙarfe goma dai-dai taro ya tashi, daga nan kuma aka ɗunguma rakkiyar amarya sabon gidansu inda Master ya ɓoye su Ummi. Zuwa yanzu an gama komai gida ya haɗu matuƙa kai kace wani ƙaramin estate ne. Dansu Musbahu kowa da sashensa matan aure kawai suke jira. Mutane basu wani zauna ba kowa ya kama gabansa akabar amarya da angonta dasu Khalid da suma gajiya ta sakasu kwanciyar wuri a sashin baƙi da suke zaune yanzu kafin matayen nasu su shigo kowa ya koma nasa sashen.

        Master da dama yana gidan abinsa dan tare suka taho da ƴan rakkiyar amarya suna tafiya ya nufi ɗakin Hibbah da kayan tsarabar da aka tanadar mata dan yaga bataci komai ba a wajen liyafar.

     Tana zaune a tsakkiyar gadon tana kwasar kuka kai kace yau ɗin aka fara kawota gareshi. Kayan hannunsa ya ajiye ya nufi gadon yana murmushi, cikin neman tsokana ya ɗaga mayafin yana faɗin, “Haba Hajjaju keda kika dawo wajen mijinki minene na kukan?”.

      Hannu tasa ta ture nasa tana ƙoƙarin juya masa baya ya riƙota yana sakin wata siririyar dariya data nema narkar da Hibbah, dan a cikin kunnenta yakeyi. Ƙoƙarin haɗe bakinsu yakeyi tana ture masa kai cikin bore hardai ya samu nasara. Salon da yake mata da kuma halin da take a ciki yasata miƙa wuya har tana maida murtani. Sai da ya tabbatar ya sakata yin laushi sannan ya barta yana sauke ajiyar zuciya. Kunya ta sata saurin sauka a gadon ta nufi toilet dan fitsari takeji.

          Ta kammala tana ƙoƙarin fitowa sukaci karo da shi zai shiga shi kuma. Hanunta ya kama yana binta da wani kallo ƙasa-ƙasa daya sata kauda kanta daga kallon nasa. “Muje muyi alwala”. Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi tamkar mai gudin ajisu. Ba yanda ta iya dole ta bisa suka koma. koda suka yo alwalar suka fito tare suka gabatar da salla. Yaja musu addu’oi masu tsayi na zaman lafiya da haƙuri da juna Hibbah na amsa masa da amin. Bayan sun kammala duk yanda taso zillewa bai bartaba sai da ya sakata cin abinda ya shigo dashi. Gasasun ƴan shila ne da yogurt dayay mata matuƙar daɗi har tana masa cin zalama da ya bama Master mamaki. Sai dai baice komaiba ya sata yo brush da barin mata ɗakin dan tai shirin barci.

        Har taji daɗi ya fita sai gashi ya dawo tana ƙoƙarin kwanciya. Badan taso hakanba ta kwanta kamar yanda shima kai tsaye gadon ya hawo yay kwanciyarsa hankali kwance.

    Wata irin soyayya ce mai tsayawa a rai da zuciya da Hibbah bazata taɓa mantawa da ita a rayuwartaba Master ya nuna mata a wannan dare. Sai dai ta jigatu matuƙa dan har saida taita masa kuka da magiya amma bai sauraraba sai da ya more kwanakin kewarta tsaf. Tun a daren suka gyara jikinsu suka koma barci, da Asuba suna idar da salla bai sarara ba sai da ya ƙara dan gaba ɗaya ta dagula masa lissafin kansa, saboda gyaran da tasha bana wasa bane ba. Ga ƙaramin ciki a jikinta wanda shi baisan dashi ba yaketa faman bidiri da bireɗensa.

         Yasha taɓara da shagwaɓa dan daƙyar ya lallaɓata suka dawo falo kusan sha ɗaya na safe dan ta samu ta karya. Sun sami ƙayataccen breakfast daga baba saude dasu Habib, tsananin yunwar da Hibbah keji yasata zaman dirshan ta dira kan abincin nan babu sauƙi. Tana gab da gamawa ta buɗe kular ƙarshe da nufin duba abinda ke ciki dan Master yace natane shi bayacin sa. Wani irin dukan kanta ƙamshin farfesun kifin yayi. Cikin zabura ta saki murfin kular tai baya har abin na bama Master tsoro. 

     Kanta ta dafe dake juya mata tana masa nuni da hannu akan ya rufe amma bai ganeba. Babu shiri ta saki aman dake taso mata dan ƙamshin kifin sake hauro mata kai yakeyi.

        Da hanzari Master ya miƙe kanta ya riƙota. Ganin aman daya tsaya yake sake taso mata dole ya kwasheta da sauri suka nufi hanyar bedroom. A toilet ya direta yana riƙe da ita harya lafa. Ya gyara mata jikin yana jera mata sannu cikin damuwa da tambayarta dama bata da lafiya ne.?

      Kanta ta girgiza masa a galabaice ga hawaye shaɓe-shaɓe ta sanar masa batason ƙamshin kifi ne. Mamaki ya kamashi dan yasan dai tana cin kifi ai, akwai lokacin da ya taɓa jin su Habib na sanar mata shi baya cin kifi tace saiko ta sakashi yaci wataran saboda ita kifi tamafi sonsa akan nama.

          Saboda laushin da jikinta yayine ya sashi neman number Abdull domin zuwa ya dubata. Babu bata lokaci kuwa Abdull ya iso, sai lokacinne ma su Habib kejin Aunty Queen babu lafiya. Gaba daya suka ɗunguma sashen domin dubata. 

         Tun a kallo guda da Abdull yay mata ya fahimci cikine da ita. Amma sai ya bata tsinken gwajin ciki yace su gwada ya gani yanzun. Ana kuwa gwadawa da tsinken ciki ya nuna kansa. Wayyo farin ciki ga waɗan nan ahali ai bama acewa komai. Master kam jin abun yayi tamkar wata almara ko tatsuniya. Ya tsare Hibbah da idanunsa dake canja launi suna tara hawaye. Abdull dake kallonsa ya rungumesa yana mai tayasa murna. Hakama su Habib gaba ɗayansu suka ruƙunkumesa suna ihun murnar zasuyi ɗa. 

        Hibbah dai baka gane farin ciki ko akasin hakan tattare da ita. Dan tunda taji ihunsu Salis na hawa mata kai ta rarrafa ta koma ɗaki ta kwanta. Acan Master ya sameta. Ya ƙanƙameta hawayen da yake riƙewa na ziraro masa. Yana hawaye yana murmushi da kissing Hibbah tako ina. Yama rasa ta ina zai bayyana farin cikinsa a rayuwa. Godiya yaketa faman jerama UBANGIJI da kirari a zuciyarsa. 

       A gaba ɗaya yinin yau waɗan nan ahali sun yisane cikin wani irin farin ciki mara misali da kwatance. Duk da zuwa azhar Hibbahn ma ta martaye garau tamkar ba itaba. Sai dai ta samu tumatur ɗinta mai yawa tasha dan yanzu bata da abu mafi soyuwa sama da shi.

           Duk da garau ɗin data koma dukan motsinta a idanun Master ne. Kaɗan-kaɗan saiya tambayeta mike mata ciwo? Mitake son ci?. Tun tana cemasa babu komai harta koma tura masa baki irin ya dameta ɗin nan. Ko kaɗan baijin haushi, sai ma murmushi da yakeyi kawai.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button