TAKUN SAKA 49

_________________________
Sam Hibbah bata wani laulayi, kifi kuwa tun daga ranar ko su Habib daina cinsa sukai a gidan. Sai wata tsadaddiyar soyayya Master ke nuna mata suna gurzar amarcinsu yanda ya kamata dan cikin nan ba ƙaramin saka masa kwaɗayinta yake ba. Gashi abin ya haɗa da zaman hutu da yakeyi a gidan harna tsahon watanni uku da aka bashi. Tun kwananta uku da dawowa gidan ita ke girkinta da Master, wani lokacin kuma taje sashen su Baba Saude suyi gaba ɗaya, musamman idan Abdull na gidan. Shafta tsakaninta dasu Habib sai abinda yay gaba. Dan ma an sama musu aiki zuwa yanzu ba zaman gidan sukeba sosai sai idan Master na bukatarsu akan wani aikin.
Komai na Hibbah ya sake canjawa. Ta buɗe ko ina ya cika a jikinta ga ƙiba cikin yana sakata masha ALLAH. Cikinta na watanni huɗu ta fara wani matsanancin laulayi da batayisa a baya ba. Ga shi Master ya koma aiki kuma. Dole Baba Saude ta dawo yini sashen nasu ko yana fita Hibbah ta koma can har sai ya dawo. Dan zuwa yanzu komai bata iyayi sai kwanciya. Ƙarin ruwa kuwa duk bayan kwana biyu sai an mata shi ake samun nutsuwa. Sau biyu Ummi dasu Zahidah na zuwa dubata. Su Yaya Muhammad kam ai basusan adadi ba. Balle Ammar yaji labari wanda kullum babu fashi idan ya dawo school sai ya biyo tanan ya ganta yake iya wucewa gida.
A cikin wannan tsukun da Hibbah ke dirzar nata laulayin aka saka aurarrakin su Habib da ƴammatansu. Zai kama dai-dai da haihuwar Hibbah insha ALLAH. Bayan saka ranar da kusan sati biyu wani aiki ya tasoma Master zuwa kudancin ƙasar. Dole ya tattara matarsa suka wuce tare dan bazai iya barinta a halin da take ciki ba. Ta tafi da kewar su Musbahu, suma ta barsu da kewarta. Dan hatta Ummi taso Master yabar Hibban anan amma dan karta shigar masa rayuwa tai shiru ta bisu da addu’a.
Sai kuma tahowar ta saka Hibbah cikin ɗunbin farin ciki dajin daɗi. Dan kai tsaye wajen shakatawa na musamman a bakin ruwa Master ya samar musu masauki. Kasancewar aikin nasa kuma na sirrine ya sai ya koma a real Isma’ill ɗinsa suka sake baje shafukan soyayya da rainon cikinsu da Master ke matuƙar so da ƙauna da fatan fitowarsa duniya lafiya. Ɗan yawon da yake da ita wajaje daban-daban yasata fara samun ƙarfin jikinta, sai dai randa laulayin ya bugar da ita kuma dole ne su kasance a gida. Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gasu da wattani uku da tahowa har sun shiga na Huɗu.
Taso komawa gida a watan daya gabata dan a farkonsa su Zahidah duk suka haihu kusa da kusa. Sai dai aikin Master dake gab da kammaluwa ya sashi hanata zuwan sai a waya akaita tura mata hoton babys masha ALLAH. Ranar sunayen ne dai da aka haɗe ta birkice masa da kuka harda su zazzaɓi. Sai da ya haɗa da Ummi dasu Yaya Muhammad a masu lallashi sannan ta haƙura. Ammar kuwa ya dage yayta ɗauka mata videon komai yana tura mata. Dan mutane ne sosai suka halarci taron musamman dangin Hajiya mama da ƴan ƙauyen su Ummi. Ita Ummi ma har mamaki da al’ajab abin ya bata. Amma saita ɗau hakan matsayin wani hikima da rahama na UBANGIJI.
Washe garin suna akai zama na musamman da su kawu ballo game da gida da kayan gadon su Yaya Muhammad ɗin da Halilu yaso handamewa. Duk da dama an raba musu tun lokacin da babansu ya bar duniya sai yanzu aka sake raba abinda ya rage musamman gidan da suka taso dan ance su Momy su tashi. Kuka momy ta dingayi tana neman alfarmar Ummi akan a barsu su zauna Hajiya mama dake kwance tace bata yarda ba. Su Ameera su fitar da miji su Yaya Muhammad su aurar dasu. Ita kuma Momy ta koma can gidan da Mahaifin su Hibbah ya bama Halilu tunkan ya rasu ta cigaba da jiyyar Junaid.
Dole kuwa haka akayi, dan su Ameera da suka fahimci tsohuwar son tona musu asiri take babu shiri suka kawo ƴan samarinsu da abaya suka raina. Gudun kar wata matsalar ta biyo baya su Yaya Muhammad suka saka bikin a kurkusa. Dan sati uku kacal suka saka. Komai kuma daya shafi kayan ɗaki basuyi ƙyashin yimusu shi ba.
________________
A satin dasu Hibbah suka dawo a satin aka ɗaura auren su Ameera. Haka taci biki a wahale ta ƙaton ciki Ammar na mata iya shege. Daya kalleta saiya kwashe da dariya. Video kuwa da hotuna yayisu kala-kala. Tun tana kulashi harta daina dan yay bala’in taso rayuwarta gaba shi dasu Habib da ayanzu suka ɗinke abokai shaƙiƙai.
Bikin dai ba wani armashi yayi ba sosai. Dansu Yaya Muhammad ɗin ma sunfi maida hankali a shirye-shiryen nasu Habib da za’ai satin sama. Wanda Ummi ce matsayin uwar anguma I.G uban anguna. Hatta lefe su Yaya Abubakar haɗa hannu sukai da Master aka haɗa komai na birgewa da nunawa tsara. Ana miƙa amare su Ameera ɗakunansu kowa ya maida hankalinsa akan nasu Habib. Dan Hibbah ma dole ta koma gida dan Master yaƙi yarda akan zata zauna anan har satin bikin. Shi fatansa ma ta haihu lafiya kafin a shiga ruguntsumin taron………….✍
[ad_2]