Uncategorized

TAKUN SAKA 50

       “Zona faɗa miki” 

Da sauri ta zille ganin zai damƙota. “ALLAH zaka makara salla ga sojojinka can kuma da alama sun dawo suma”.

     Master dake ƙarasawa gaban Mirror yana goge jikinsa fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Aini na ɗakkosu a school. Dan yau ma tare dasu zanje massallaci. Na bar yarda su Habib namin wayo”.

        Ƙarasowa Hibbah tai garesa ta rungumosa ta baya da kwantar da kanta a gadon bayansa tana murmushi. “Ina bayanka big daddy. Dan kuwa dama kullun mitar yaran nan big Daddy bai zuwa dasu massallacin juma’a ne.”

      Hanunta ya kamo ya zagayo da ita ya jingina da mirror ɗin. Yaɗan lakace hancinta da sumbatar lips ɗinta. “Insha ALLAH zan gyara baby luv. Koda kinga ran juma’a ban dawo akan lokaci ba, kiyi azamar kirana ki tunamin alƙawarin sojojina”.

        Rungumesa tai tana murmushi da sumbatar ƙirjinsa. Shima ya rungumetan ransa fes da tarin so da ƙaunarta.

      Da taimakonta ya shirya cikin ɗanyar shadda fara ƙal harda murza hula. Itama ta kimtsa sauri-sauri suka fito tare suna baza ƙamshi. A falo suka iske su Hydhar daketa faman hayaniya har an gama shiryasu cikin nasu shaddojin farare tas irin ɗaya mazansu da matansu. Da gudu sukayo kan Hibbah duk suka rungumeta suna faɗin “Big Mommy Oyoyo”.

         Durƙushewa tai itama cikinsu tana mai rungumesu da faɗin “Oyoyo sojojin big daddy Ya school?”.

       Atare suka amsa mata da Alhmdllh. Ta miƙa hannu ta kamo Mimi dake gefe tana tunzura baki fuskarta duk hawaye. “Kai! Kai waye ya jangwalo min uwa a gidan nan ne?”.

       Duk juyawa sukai suna kallon mimin har Master dake amsa waya. Mimi ta sake taɓe baki tana nuna Sudies. “Yaya Sudies ne ya cimin cake ɗina a wajen Ammi”.

       Katse wayar Master yayi, ya zirata aljihu yana matsawa inda Mimin take. Cak ya ɗauketa tare da sumbatar kumatunta. “Mamyna shine shagwaɓa kuma bai tashi ba sai yanzun?. Maybe rowanki kikai masa shiyyasa ya ɗiba ai.”

      “Big daddy ƙaryane, nima ta shamin juice ne shiyyasa na mincini cake ɗinta”.

     Cewar Sudies yana matsowa kusa da Master. Dire Mimi yayi kusa da Sudies ɗin ya ɗan duƙo gabansu ya kama hanunsu ya haɗe waje guda. “To tunda kowa yama kowa a shirya. A yafema juna kuma”.

     Kallon juna Mimi da Sudies sukayi, Sudies yasa hannu ya sharema Mimi hawayenta. “Sorry sweet heart bazan sake ba ki yafemin”.

      Mimi dake murmushinta mai kama dana Hibbah tace, “Nima sorry yaya Sudies ka yafemin”. Sai suka rungume juna. Tafi su Hydhar suka farayi musu kamar yanda aka koyar dasu. Master dake murmushi ya sumbaci kumatunsu ɗaya bayan ɗaya yana sanya musu albarka.

    Hibbah dake dariyar wannan hali na Mimi da gaba ɗaya ita ta biyo tace, “Mamana to azo amin oyoyo ɗin idan an huce”. Da gudu Mimi tazo ta faɗa jikinta. 

         Master yay dariya da faɗin “Like mother like daughter”.

      

     Su Habib dake tsaye suma duk suna kallonsu dariyar suke musu. Suka ƙaraso cikin falon Khalid ɗauke da Ansar daya amso hanun Sharifat. Yana ganin Master ya fara miƙa masa hannu. Amsarsa yay yana faɗin, “Oh my sweet Darling ina ka shigane ban gankaba”. Ya sumbashi kumatun yaron mai tsanain kamanni da shi da kullum ake gaddama a gidan akan waya biyo?. Hibbah da Habib dai sai dai suyi dariya kawai dan sunsan Master ne tamkar yayi kaki ya ajiye.

      Ganin zasu makara salla suka fice. Aka bar Ansar na kwasar kuka shi sai ya bisu. Lallashinsa Hibbah ta dingayi daga ƙatshe ta goyasa dai.

      Ana idar da salla basu jimaba a massallaci suka dawo, can cikin garden aka kai tabarmi aka baje tamkar yanda suka saba. Cikin ado da gayu suma matan su Musbahu duk suka iso garden ɗin, cikin girmamawa suke gaida babban yaya Master. Shiko yana amsa musu da kulawa tamkar yanda ya saba. Gaba ɗayansu har baba saude suka ci abincinsu hankali kwance zukatansu fes da farin ciki. Bayan sun kammala su Hibbah suka gyara wajen yara kuma suka fara wasansu. 

     Bayan sallar la’asar kowa yayo shiri cikin kayan ƙwallo su Habib da yaran har Master suka baje a compound suna wasanninsu cike da farin ciki da tsantsar ƙaunar junan da baka isa cewa suɗin ba jini ɗaya baneba. Basu bar wajen ba sai magriba. Sai da sukai har sallar isha’i suka dawo gidan, kowa ya nufi sashensa domin hutawa da iyalansa.

Washe gari gaba ɗayansu suka dunguma gidan Ummi yini. Idan wannan satin sukaje, wani satin sai su Yaya Muhammad da matansu suma da yaransu suzo nan. Lahadi kuma kowa ya ɗauka matarsa su tafi inda yake buƙata. Ko gidansu ko yawon da shi yafi buƙata.✍????

_Alhamdulillahi_

_To masoya nima dai bara na shaƙata anan dan maganar gaskiya na rubutu. Abinda na faɗa dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladan. Wanda nai kuskure ALLAH ya yafe mana baki ɗaya._

*_Littafin TAKUN SAƘA ƙirkirarren labarine bawai gaske ba. Idan kayi karo da abinda kai kake gani a mahangarsa tamkar bazai yuwu ba sai ka ɗaulesa matsayin nishaɗi da marubuci kansa domin ƙawata labarin sa. Abinda yazo domin tunatarwa kuwa sai ka gwada shi ko zaka dace. Wanda ya baka haushi kayi haƙuri haka rayuwa take dama ba komai akeyi dan birgewa ba. Wanda ya baƙanta ranka ma kayi haƙuri rayuwa akwai zaƙi a cikinta akwai ɗaci. Abinda kaso gani baizo a yanda kaso ɗin ba kayi haƙuri ajizancine irin na ɗan adam mai mantuwa da gaggawa._*

_Akoda yaushe ZAFFA BIYAR na godiya a gareku masoya, yanda baku gajiyaba wajen bibiyarmu, muma bazamu gajiyaba wajen yi muku godiya da ƙaunarku akoda yaushe. ALLAH ya barmu tare, alkairinsa yakai gareku aduk inda kuke a faɗin duniya????????????????????????????????_.

*Na yafema dukkan wanda ya ɓatan rai a wannan rubutu, nima ina neman afuwa da gafarar kowa dan zata iya yuwuwa wannan shine littafi na ƙarshe da _Bilyn Abdull_ zata rubuta a duniya????????????. ALLAH ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. ALLAH yasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin ciki a garemu. ALLAH ka zaunar da ƙasarmu lafiya ka azurtamu da shuwagabanni na gari. Ka shiryemu muma talakawan ka gyara mana zukatanmu gurɓatattu*????????????????????

_Sai mun haɗu a zafafa na gaba idan da rabon hakan_.

*_BILYN ABDULL CE????????????_*

_______________________

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button