KWARATA 54

???? —— 54
Har muka isa daga ni har Alaji babu wanda yayi ma wani magana a cikinmu , kuma munyi sa’ar samun Baban Hafsa kamar dai yadda nayi tunanin dama zamu sameshi , gabansu nasa Alaji yayi parking ban fito daga cikin motar ba na sauke gilashin gefe na tare da cewa Assalamu Alaikum….
Cikin farin ciki ya ɗago daga latsa wayar da yakeyi jin muryana , ba tare daya ansa sallamar ba yace Hajiyata da kina duniyar nan ? Kin kama waya kin rufe ruff , saboda kunsan layina na farko Dikko ne ya karya shi , nace Ey wallahi , tasowa yayi daga cikin mutane yana kaucewa inda babu jama’a cewa fito kiji mana.
Fita nayi daga cikin motar nabi bayanshi bayan wata container dukanmu muka tsaya , kusa dani ya matso sosai ya riƙemin ƙuguna magana ƙasa² yayi cewa haba ina kika ɓoye haka kika barni ina ta garari a garin nan na rasa ina zan samu labarinki ? Shiru nayi ban bashi ansa ba kuma ban cire hannunshi daga riƙo da yayi min ba ,
Yace ya na ganki duk rai a haɗe ko anyi miki wani abu ne ? Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa Binna , me Binna yayi miki ne ? Neman sa nake saina ga bayanshi , kashe shi zakiyi kenan ? Nace tabbas kuma ba gudu babu ja da baya , amma me yayi miki haka da ciwo wanda kikayi ƙudirin ɗaukar fansa rayuwarshi haka babu sassauci…..?
Cikin ƙunar rai nace shin ko kasansa ne ? “Yar dariya yayi ta duniyanci sannan yace ai wani ya rigaki shafe labarinshi a duniyar nan , ɗago kaina nayi na kalleshi nace wane mai zarra ne haka wanda yafi mace zafin nama ? Baban Hafsa yace abin duhu ne amma ke wane irin duhun ya baki na rayuwa haka ?
Sauke hannunsa nayi daga riƙon da yayi ma ƙuguna nace , shin wai da kake tambayana duhun da Binna ya bani kama san waye Binnar tukunna ? Ni kuwa nasan Binna domin Babanmu ɗaya dashi , kamar walƙiya haka naji duniya ta juya , cikin dakiya nace amma kasan ɗan uwanka ne ka barni nake furta kalmar kisan sa daga bakina ? Sake rungumoni yayi ya rumgumeni sosai , kunsan akwai runguma akwai rungumewa tou rumgumewa yayi ya kwantar da fuskarshi a saman ƙafaɗata , hawaye ya cikamin ido wato wannan shi Yayan Babana ne ?
Goge hawaye na nayi tare da saita muryata nace me yasa bakwa zuminchie da Binna ne ? Har yanzu yana kwance a saman jikina , cikin disashshiyar murya yace aishi kanshi Binna bai isa yasan ni wayen shi ba bare kuma “ya “yanshi , banma san gidan da yake zama ba amma kaf rayuwarshi da duk wani motsinshi a tafin hannuna yake ,
Amma me yasa ka sakawa rayuwarshi ido bayan kuma ya fita daga rayuwarku ? Ai bashi ya fita daga rayuwarmu mune muka fitar dashi , akan wane dalili ? Ɗago kanshi yayi tare da sunbata ta yace labarin yana da tsayi ni kuma na yanke miki wahala tunda an sheƙar miki da Binna zuwa duniyar mutuwa…
Murmushi nayi mai nuni ina farin ciki amma a baɗinance ina cikin tashin hankali , ƙarfin hali nayi tare da cewa labarin yana da tsayin gaske amma duk meye musabbabin fitinar taku ne…. ? Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskata yace keko kuɗi ne silar komai , yanzu dai zamu ɗan rage dare ne ko yadai…. ?
Share maganar nayi da cewa wai kasan “ya “yan Binna kuwa ? Taɓe baki yayi cewa shi kanshi Binnar dakel na sansa bare wasu “ya “yanshi can na wahala , dariya nayi nace tou ina da sharaɗi ɗaya tak zanyi tarayya dakai amma duk wata so ɗaya ka yadda ? Yace Eh na yadda , nace yau nawa ga wata ne ? Ya faɗamin , nace tou ni bana zini a farkon wata da tsakiyar wata sai ƙarshen wata kuma shima ƙarshen wata sai daren da wata zai fita haka yayi maka ne ? Eh na yadda nace tou idan Allah ya kaimu gobe dani dakai mu haɗu a *Erudite comprehensive sch*.
Me zamuyi a makaranta kuma ? Zubin adashe zaka fara dan zan koma makaranta ne kuma itace makarantar da nake so , sabon machine uniform littafai da duk abinda makaranta ta buƙata zaka biya ne sai ka biyamin kuɗin makaranta tun daga aji 1 zuwa aji 3 idan haka yayi maka mu ƙulla tarayya dakai bana san surutu ka kame bakinka kayi shiru abinka kamar yaro ya kama nonon uwarshi….
Zai sake magana nace yi haƙuri 9:44pm zan tafi gida ana rufe mana ƙofa 10:00 , mu haɗu makarantar idan Allah ya kaimu gobe misalin 12:30pm kuma karka zo da aboki ko ɗan rakiya , ina faɗin haka na wuce da sauri na koma cikin mota Alaji yaja muka tafi…
Tunda na shiga motar wasi² nakeyi kenan Hafsat “yar uwata ce da Baban Hafsa da Babana babansu ɗaya ? Tou wane irin sirri ne kuma Aunty Mamy ta ɓoyemin wanda tace da Binna yasan matsayin Hafsa a wurinshi daya haɗiye zuciya ya mutu ? Tunani nayi mai zurfi zuciyata ta faɗamin cewa ko shima Baba kwarto ne ? Da sauri nace astagafurillah , ita kuma Amisty ya muke da ita ne ? Hmm Allah ka iya mana ,
9:57pm a ƙofar gidan Baba Ƙarami tayi mani nacewa Alaji yayi haƙuri yaje zamuyi waya idan na shiga ciki yace tou , kuɗi ya bani har 10k ina san Alaji ko ba komai akwai kyauta , godiya nayi na shige ciki , ina shiga Baba Ƙarami ya fara banbamin bala’e daga gidan uwar wa kike a tsohon daren nan ? Balbaɗaɗɗa irin iskanci da kika saba a gidanku idan kikace zakimin shi nan saidai ki tattara ki kama gabanki “yar iska karuw…… Kuɗin hannuna na miƙa mishi duka sai yaci gaba da cewa Allah yayi miki albarka ubangiji ya ƙara koro kasuwa yasa kifi haka matsayi.
Ban mishi magana ba nayi cikin ɗaki , maman safiya kuma tace sai ki kwashe duka ki bashi ai ya kamata ma ki riƙa biyan kuɗin hayar ɗakin nan , ko inda take ban kalla ba na kwanta tare da saka airpiace a kunne na ina sauraron firata da Baban Hafsa , bayan na gama ji tass nayi murmushi tare da kiran wayar mutumina amma a kashe take har yanzu , saida na kalli hotonshi sannan nayi bacci.
Jiddah da Al ‘ Ameen zaune a gaban bokansu ya kwarara ihu tare da ɗirkaka uwar ashariya bayan duk sun kora mishi bayani , roƙo na farko abinda aljannu suka buƙata shine a basu jinin jariri sabuwar aihuwa , matakin farko kenan , mataki na biyu kuma idan ba’ayi wannan ba ita Jidda zata kawo jinin al’adarta , mataki na ukku shine za’a kawo maniyin Dikko , wane kuka zaɓa ne ? Boka ya tambaye su ,
Cikin rawar jiki Jiddah tace haba a ina za’a samu wani jinin jariri ne ? A daina maganar jariri gaskiya , wata irin dariya bokan yayi mai firgitarwa , yace arne zaisha jini ne shine zai shiga zuciyar ita yarinyar ya sanya mata wasi² , idan kuma kika bayar da jinin al ‘ adarki duk duniya yadda Dikko zaiji maganarki ko ta uwarsa bazaiji haka ba , idan kuwa aka kawo maniyinsa labarin yarinyar ya goge a zuciyarshi kwata² har abadan abada zaima manta daya taɓa sani wata yarinya wai ita Sultana , bazai sake san wata mace ba sai ke , ke ɗaya ke ya sani kuma ke zaiyi ta ƙauna har a mutu , Hahahahaha…..
Jiddah tace boka aini yanzu bana tare dashi ya koroni gida yace sai yaga ita Sultanar zan koma kuma babu wanda yasan ma inda take zaune a halin yanzu dan ita mahaifiyar Dikko tace tabar katsina kwata² , dariya bokan yayi sosai sannan ya ɗaga hannunshi daga gefen shi yace tana katsina gata nan , lafiya lau aka nuno hoton Sultana kwance , Jiddah tace Eh wallahi itace , itace boka , dariya yayi tare da ɗaukar kaza ya wurga sama cikin seconds ta dawo ƙasa har an tsotse mata jini , Jiddah ta firgice sosai boka yace idan har kika faɗa masa tana katsina sai ya dawo , idan ya dawo daga nan komai zai tafi mana a sauƙaƙe ,
Al ‘ Ameen yace haka za’ayi ranki ya daɗe kinga idan kika samu kika samo sai ki bani ni kuma sai nazo na kawo ko ? Jiddah tace Eh , tadai daɗe tana faɗawa boka yadda take san aikin ya tafiyar mata yadda take buƙata , da suka tashi tafiya ta yayyafawa boka ruwan kuɗi shi kuma ya watsa kuɗin sukayi sama…..
Koda suka koma gida Al ‘ Ameen sai ƙara jaddadawa Jiddah yake tayi ƙoƙarin samo sperm in mai gida idan aka goge ko wace mace a zuciyarshi aka sakata ai taci lafiya , Jiddah tace ai yanzu wanka zanyi na kirashi , Al ‘ Ameen yace ki bada himma dai karki tsaya sanya , tace insha Allah , sallama yayi mata ya fice daga palon ,
Yana fita ya kira Mardiyya , bayan ta ɗauka yace doughter nasara tana ƙara tunkaro ahalinmu , lallai ke mai nasara ce kuma kece tauraruwarmu gaba ɗaya , fitila mai haskawa amarya a gidan mai gidana , dariya Mardiyya tayi tare da cewa Uncle ya ake ciki yanzu ? Al ‘ Ameen yace boka yasa a samo masa sperm in mai gida kuma na faɗawa boka yadda zaiyi kinga ina kai masa za’a goge Jiddah a goge banzar Sultana , filin zuciyar mai gidana naki ne ke ɗaya my doughter , Mardiyya tace godiya nake Uncle Allah ya taimake ka ya bada sa’a , Al ‘ Ameen yace am3n. Sukayi sallama !
Koda Jiddah ta faɗawa Dikko Sultana ta dawo katsina cewa yayi da kyau , ta tambayeshi ranar da zai dawo yace shi daga nan ma gaba yaci , tace haba Yaya nidai tunda an ganta ya kamata kayi haƙuri ka dawo , Dikko yace kiyi wata maganar bana san wannan , Jiddah tace dawowa na ne baka so ko kuwa zancen Sultanar ne yanzu baka so ? Tsoki yayi ba tare daya bata ansa ba ya katse kiran ,
Yana katse kiran Jiddah ya fara kiran mai gadinsa na goruba gidan daya ajiye Sultana , bayan sun gaisa Dikko ya tambayeshi ko An mata tazo nemansa ne ? Yace A , a , gaskiya bata zo ba , katse kiran yayi ya kira Umar yace masa An mata ka ganta ne a katsina ? Umar yace gaskiya bata dawo ba , shima katse kiran yayi tare da cewa “yar ranin hankali ashe kinga dama kin dawo , hmmm kedai kika sani mara aikinyi kuma aradu bazan kiraki ba.
Washe gari bayan na gama duk abinda nakeyi na kira Aunty Suwaiba muka gaisa , nayi mata sannu da jiki ta ansa cikin farin ciki da faɗamin tayi kewata , nace mata insha Allah ai zanzo , tace Allah ya yadda , nace ko Aunty ta kira waya ne ? Aunty Suwaiba tace har yanzu dai shiru gaskiya bata kira ba saidai wata number ake ta kiran wayar da ita , nace kin ɗauka ne ? Tace tunda naji namiji ne ban sake ɗauka ba , ki turomin number , Aunty Suwaiba tace a , a gaskiya Sultana kiyi sabgar gabanki ki fita daga rayuwar wani zaƙule² , Aunty turomin number da Allah , Aunty Suwaiba tace gaskiya bazan turo ba , juyin duniya nayi amma taƙi haka nan na gaji na haƙura mukayi sallama.
Dani da Baban Hafsa dukanmu 12:30pm a cikin makarantar tayi mana , a napep nazo bayan na iso na anshi kuɗi a wurinshi na sallami mai abin hawa , daga nan kuma muka ɗunguma zuwa Ofishin shugabar makaranta , bayan gaisuwa Baban Hafsa da kanshi yayi bayani tare da nema min gurbin karatu a makarantar , duk dai abinda ya kamata shine yayi , duk wani rubuce² shine ya cike komai da hannunshi da sunan MARYAM ALIYU ,
Bayan ya gama ya tambayi shugabar makaranta shin ko zai iya biyan kuɗin makaranta na daga aji 1 har zuwa 2 tace anayi zai iya kuma ta ƙara masa da cewa ana shiga aji dan koyon karatu na musamman bayan ɗalibai sun tashi , extra lesson , tambayana yayi ko ina ra’ayi nace masa ina so , gaba ɗaya akayi lissafi yayi mata transfer kuɗin zuwa cikin asusun makaranta ,
Ranar da zan fara zuwa makaranta aka faɗamin fita nayi daga ofishin na basu wuri domin su ida abinda suke san kammalawa , bayan sun gama ya fito dani dashi duka wurin motarshi muka nufa , bayan munje muka buɗe kowa yayi ma kansa mazauni.
Bayan mun zauna yace min Hajiyana gaskiya baza ki hau machine ba wurin zuwa makaranta , motar makaranta zata na zuwa tana ɗaukarki , sch bus , nace kuɗi ne baka da ko a ina matsalar take ne ? Yace ina da kuɗi kawai dai girmanki ya wuce ki hau machine , faɗuwa gabana yayi kardai yaga hotona a lokacin da akayi ta yamiɗiɗi dani a social media lokacin da Dikko ya bani motarshi ?
Dakewa nayi nace shin wane irin girma ne kake gani ina dashi wanda har kake tunanin nafi karfin hawa machine ? Jawoni yayi jikinshi yana cewa aike babbar ƙaddara ce samunki sai namiji mai babban rabo , tarayya dake kuma sai jarumin namiji irina , matsayinki da darajarki saima kin ɗora mutum a linzaminki zai tabbatar da haka nine zan tabbatar idan har muka keɓe na samu nasarar taka ruwan cikinki , murmushi nayi tare dayi mishi kallon ɓatacce.
Lalube jikina ya farayi , kallon sakarai nayi masa tare da ƙara ƙureshi da ido sosai yanzu na tabbar da ɗan uwan Babana ne dan naga kamarshi da Baba harta ɓaci wallahi kuma sai yanzu na fahimci maganarsu iri ɗaya sukeyi yanayin kallonsu da komai dai iri ɗaya saidai shi Babana yafi shi haske sosai kuma yafishi hanci da ƙaramin baki amma gadai jinin nan yana yawo a jikinshi.
Hannunshi ya tura cikin rigata tare da ƙoƙarin haɗa bakina da nashi na riƙe hannunshi na kauda fuskata gefe ɗaya idona ya cika da hawaye dan wallahi kallonshi nakeyi kamar Babana , cijewa nayi cikin jarumta nace kar ka manta da nace maka bana ci sai ƙarshen wata , ƙara riƙoni yayi yana cewa tou ai ba cewa nayi zanyi ba koma zanyi kina tunanin zanyi a mota ne ? Kuma a motar ma tsakar gari da tsakiyar rana ? Murmushi nayi tare da cewa ai ba matsala bane ba ra’ayinka ne cin duk abinda kake buƙata yayin da yunwa ta taso maka dan ba’a tarar abinda za’aci a dai² irin lokaci buƙata ɗaya kawai aji ciki yayi nauhi ,
Kin san da haka tou kike ta wahalar da rayuwata ? Kika ɓace min ɓat kuma da kika dawo sai kika zo da wani tsarin banza , jifa yanzu ko hidimar da nayi miki ai ya isa ki bani tukwuici mana , tou kayi min gori ka biyamin kuɗin makaranta , a , a ba gori nayi miki ba ina so dai kisan yadda akeyin halakkaci da sakayyar farin ciki yayin da akayi maki karamci ya ƙarasa maganar tare da haɗe bakina da nashi wuri ɗaya zuyzuy ya riƙa lashewa yana tsotsewa wani irin ihu nayi tare da cewa nace bana so wai kai maye ne iye ?
Dariya yayi irin dariyar Babana yace maye ne ni mana , kin taɓa ganin namiji ba mayen mace ba ? Duk uztazancin namiji duk imanishi duk haukarshi ko hankalinshi duk talaucinshi ko arziƙinshi duk wani matsayi da yake taƙama dashi mace ce remote control inshi , ke yaufa duk masifarki saina sha wannan dadɗan bakin naki wallahi , matsowa yayi daga saman kujerar da yake zaune yayi sosai dan sai zuƙewa nakeyi inayin baya amma maye ɗan mayyar saida ya jawoni ya ƙara lasar bakina , cikin kuka nace haba Bab….. Kimace Baban ai na isa in haifeki tunda yarinyata ta huɗu ma nasan zata girmeki amma dady suke cewa. Kema sai kice Dady daga yau….
Cikin kuka nace dan Allah ka daina irin wannan abun mana ! Ai yanzu na fara miki irin wannan abun dan ni daɗi nakeji idan inayi miki , haka zamuyi dake ƙarshen watan iye ? Haka zaki ta ihu kina kiran Dady har maƙota suji kukanki ? Fuskata kaca² da hawaye nace tou ka bari sai ƙarshen watan yayi mana ka bari ƙarshen wata yazo idan bakayi abinda kake so ba sai kacemin marowaciya ce ni mana , Allah ya taimakeni yace Allah ya kaimu yayi maganar tare da gyara rigarshi ya gyara fuskarshi dana daƙune hawaye ,
Ajiyar zuciya nayi a lokacin daya fara tafiya da motar yana cewa ina zan ajiyeki ne ? Ajiye ni kasuwa , me zakiyi kasuwa ? Yayi tambayar yana kallona nace hijabi zan siya , sai me kuma ? Nace shikenan , yace tou a siyo hada niƙaf dan banasan ayi ta kallemin wannan kyakkyawar fuskar mai ɗaukar hankali ya karasa maganar tare da shafo fuskata nace tou ,
Har muka zo kasuwa daga haka babu wanda ya sake magana sai shashshekar kukana dake tashi kaɗan² , bayan ya ajiyeni kasuwa ya bani 30k yana cewa sun isheki ? Da sauri na buɗe mota nayi gaba ko ansa ban bashi ba , murmushi yayi tare da bin Sultana da kallon mai tattare da tsantsar so , saida ya daina hangota ya wuce yana mai addu’ar Allah ya bashi sa’ar “yar yarinyar can ya more abunshi…..
Ta bayan kasuwa nabi na fice daga kasuwar ina ta kuka tare da goge bakina wai Yayan Babana shine yake haɗa bakina da nashi har yake addu’a Allah ya bashi sa’ar hawa saman ruwan cikina ? Wayyo Allahna wai meya haɗa wannan bala’e wanda yasa “yan uwa suke cuɗanya da “yan uwansu babu wanda yasan matsayin kowa , wayyo Allahna Aunty Mamy me yasa tun farko baki faɗamin abinda ke tsakanin Babana dasu Amisty ba ? Juyawa naji garin yanamin , Malam Ɗayyu ya faɗomin a rai dan haka na fara kiran wayarshi !
Bayan ya ɗauka muka gaisa nace Malam kamin bayanin abinda ka sani akan abinda ke tsakanin Babana da Bello tou ko kasan dalilin da yasa matar Babansu Babana ta kori su Baba daga gidansu ? Malam Ɗayyu yace a , a , nace Aunty Mamy ta faɗa maka tsakanin Amisty Hafsa da Babana ? Karka ɓoyemin komai ka faɗamin abinda ya riga ya wuce ya wuce ka faɗamin meye tsakanin Babana dasu don Allah……..?
Malam yace Eh gaskiya abinda mariganya ta cemin shine , tace shi Bello yace yana san ya jefe ƙiyayya mai girma a tsakanin ahali ɗaya duk akan fansar budurcin matarsa da Binna ya ɗauka a ranar da yake tunanin itace ranar sa ta farko a angwanci , shine yayo dillacin ita Hafsa da Amisty wadda ita Amistyn da Baban shi Binna da Kakan Amisty suke Baba ɗaya , da sauri nace tirrr da wannan ahali , malam bana san sanin zuminchie su sauran bincike da sanin dalilin da yasa aka kashe min Babana da wanda suka kashe shi bana kowa bane nawa ne , miye tsakanin Babana dasu Hafsa ?
Malam yace muradi ne , nace wayyo Allahna wane irin muradi Malam ? Malam yace muradi wanda baya buƙatar kawaici kunya ko kara , tirrrr Allah ka tsinewa Bello albarka tsinannen Allah ubangiji ma bazai barka ba kuma nima bazan barka ba da zaran na gama haɗa abinda nake buƙata ƙaryarka ya ƙare aihuwar asara ban yafe maka ba kuma kada Allah yaba uwarka ladar aihuwarka , kashe wayata nayi tare da dafe goshina da hannun damata kaina naji yanamin ciwo kamar zai faɗo ƙasa , Aunty Mamy tayi gaskiya da tace gaba ɗaya ahali sun zama *KWARATA…*.
Baba ya nemi Amisty kuma ya nemi Hafsa , ɗiyar Yayanka , da ɗiyar shi ta zumincin Allah , kowa mayunwanci ne duk wanda aka bashi saiya ansa yaci babu mai haƙuri inama anfanin irin wannan muradi , yanzu nima gashi Baban Hafsa yana muradina a hayaniyance nace ni kuma ba muradikanka nakeyi ba dukiyar da tasa mahaifiyarka ta lalata zuminchie itace muradina kuma saina ga bayanta kaf saina mayar daku faƙiran ƙarfi da yaji , tunda har tayi sanadin lalacewar zuminchie ta fasa kan “yan uwa saina tarwatsa komai har gobe dai zata rayu da taƙaicin *BINNA* kuma saikin mutu da nadamar sanin *BINNA* , kun kashe maciji amma baku sare kanshi ba , kun kashe *BINNA* amma baku sani ba *BINNA* yana nan a saman doron ƙasa na ƙarasa maganar tare da buga ƙafata ƙasa , sai kun mutu dukanku da baƙin cikin *BINNA* domin Binna ya dawo daga duniyar mutuwa………
A sassauce nace koma miye yasa kuka korashi daga duniya kuma sai kun tafi baku ci koma miye ba kuma haka zaku tafi ku barshi kunaji kuna gani…
A gajiye na koma gida zuciyata cike da masifu iri² , a ƙofar gida na samu Baba ƙarami zai fara magana na bashi kuɗina kaff amma bai ansa ba yace ki tattara naki ya naki ki kama gabanki domin zamanki a tare dani babban haɗari ne da kuma barazana a rayuwata , cike da ladabi nace yanzu kuma laifin me nayi maka ne ? Idonshi cike da hawaye yace babu abinda kikamin amma yau duk mutumin dake anguwar nan babu wanda bai shiga tashin hankali ba da ɗimuwar rayuwa ba sanadinki ,
Ƙara tausasa muryata nayi cikin kuka nace sanadina kuma Baba ? Nida bana nan me kuma ya faru ? Baba yace wasu mutane ne suka zo ni banma taɓa ganin irinsu ba sai yau suka shigo anguwar nan sai hauka sukeyi sukayi ta harbe² suna nemanki duk gidajen anguwar nan babu gidan da basu binke ba suna nemanki , nace su waye su ? Hukuma ce ko kuwa “yan gani na iya ne ? Baba yace koma “yan waye ki tafi daga anguwar nan dan zasu iya dawowa ko wane lokaci , murmushin ƙarfin hali nayi tare dayi ma Baba godiya na wuce……
Ina tafiya ina nazari , babu yadda za’ayi Bello ya fito fili yasa a nemo mishi ni saboda ta ƙarƙashin ƙasa yakeyin cutarsa kuma idan ma banda wata sahihir sheda babu yadda za’ayi nayi shara’a da Bello , tou wane sabon abokin gabar ne ya ɓullo haka a lokacin da abubuwa sukayi ma kaina yawa ? Wata zuciyar tacemin Mardiyya ce , kaina na girgiza tare da cewa a , a , Ummu Affan ce ? Ba ita bace , su Amisty ne ? Um ummm basu bane ,Momy ce , tabbas itace tunda dama tace idan aka sake gani a garin katsina aka faɗa mata zatamin tire² tabbas itace ba kowa ba , wallahi itace ma , dariya nayi tare da cewa nayi gidan ɗanki kije can ki kamoni , na karasa maganar a dai² lokacin dana tsaida napep nace mishi kaini goruba road.
Tafiye muke a napep ina kiran wayar Dikko a kashe dai take har yanzu , amma ina mamaki ya akayi Momy tasan nazo katsina ? Murmushi nayi koma dai miye na tafi wurin Dikko naga yadda za’ayi dani dan na lashi takobin zama katsina ko za’a kasheni , tunani dai iri² a zuciyata muka isa goruba road 1k naba mai napep saboda babu canji , yana wucewa nima na shige gidan ,
Gidan a buɗe yake , gaisawa nayi da mai gadin na wuce ciki , palon kuma abokan Dikko ne cike wasu nacin abinci wasu kuma hankalisu yana kan tv suna kallon boll duk yadda akayi Dikko yana nan ko kuma zaizo dan ba’a irin wannan zaman sai idan yana nan ko kuma idan zai dawo daga tafiya ,
Banma kowa magana ba na wuce ciki kuma suma babu wanda yayi min magana dan ko sallama banyi ba , ɗakin da nake zama na wuce na shiga da sallama , yana nan dai yadda nasanshi tun farkon farko , kayana a gefen katifa lulluɓe kamar dai yadda aka saba lulluɓesu , zama nayi gefen katifa na rufe wayata na ɓoyeta dan idan har Dikko yazo nasan zaiyi bincike , kuma bana buƙatar yasan matsalar data shafi ahalina da rayuwata saboda wata rana dan bansan inda abun zai tsaya ba , kuma babu wanda yasan abinda gobe zatayi sai Allah ,
Rufe ɗakin nayi na wuce bayi nayi wanka bayan na fito na canja kaya , kwanciya nayi naci gaba da tunanin rayuwa irin tawa , sai kuma su Amisty suka faɗomin a rai ko sun daina karuwanci yanzu ? Allah sarki Hafsa har tasan Babana ya gogeta taso ita da Amisty su gurjeni suma , hmmm ko ina labarin Ummu Affan ? Ina san sanin rayuwar Aunty Suwaiba duk yadda akayi cire mata ƙafafuwa akayi tou fa , naji dai da rayuwata naga wannan irin rayuwa.