TAYI MIN KANKANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

TAYI MIN KANKANTA 7

 

???????????????????????????????? *TAYI MIN ƘANƘANTA*

????????????????????????????????

*Zahra Surbajo*

*7*

*Bayan shekara ɗaya*

“Modibbo ɗiyata zata mutu a sansanin ƴan gudun hijira,kataimaketa!!!! kataimaketa!!! kataimaketa!!!!!!!!!”

A Razane ya farka daga baccin da yake,wani gumine ya karyo masa me zafi,gudun AC dake ɗakin ya ƙaro,sannan ya samu guri yazauna yana tunani gameda mafarkin da yake yi da Hauwa ƙanwarsa,wacce sanadin faɗan da akayi a garinsu yasa ta ɓace wanda sunyi cigiya har sungaji.

To shi wannan mafarkin da yake da ita me yake nufine,yau kusan kwana uku kenan seyayi mafarkin,ɗiyarta to dama ta haihune ko ya abun yake,a iya saninshi hauwa nada matsalar rashin haihuwa,kuma mijinta ankasheshi a faɗan da akayin.

Haka de yayi zugum shi kaɗai a ɗaki yana tunani,to shi wanne sansanin ƴan gudun hijira zashi,?taya ze iya gano ƴar da be san kamanninta ba,?to bama wannan ba shin mafarkin gaskiya ne?wainnan tambayoyi sune ke yawo a kansa da ya rasa amso shin su.

Haka ya kwana be runtsa ba,da gari ya waye bayan yayi sallar asuba ɗakin matarsa ya nufa,

Da faraarta ta taso ta tarbeshi,bayan sun gaisa ne,tace cike da kulawa”Alhaji naga kamar kana cikin damuwa?”

“Hajiya kwana biyu ina cikin damuwa,hauwa kullum se tazo amafarkina tana cewa in taimaki ɗiyarta,a sansanin ƴan gudun hijira ni na kasa gane kan wannan lamari wallahi”ya faɗi cike da damuwa.

“ka kwantar da hankalinka baban Muhammad,wataƙila akwai wani abu me muhimmanci gameda mafarkin nata nide ashawarata da ka fara duba sansanin ƴan gudun hijirar kagani ko wani taimako suke buƙata yasa hauwan ke zuwa ma a mafarki”

“kema kin kawo shawara hajiya,zanyi hakan in yaso duk week end na dinga zagayawa guraren da ƴan gudun hijirar suke,dan abun akwai ɗaure kai wallahi”

Haka de suka gama jajantawa modibbo ya miƙe ya fice zuwa ɗakinshi,wanka yayi ya kimtsa sannan ya dawo dinning suka ci abinci,agurin cin abincin ne yace “Munyi waya da Muhammad ɗazu ya shaidamin ƙarfe biyu na rana zasu iso, kuma hajiya babba jikinta da sauƙi,shiyasa ze taho,ki tanaji komai,ni zan fita,zan jima kan in dawo”

 murmushi Hajiya tayi  sannan tace”lalle Muhamnad yaci saa da hajiya babba ta barshi yataho,ita da tace se ta masa aure sannan ze dawo”

Dariya sukayi irin ta girma sannan yace”hala ta masa matar ne shiyasa tabarshi yataho”

Miƙewa yayi yana kallon agogon hannunsa yace”hajiya bari in ƙarasa office,zamuyi waya,in kuma naga da lokaci zan ɗan leƙa sansanin ƴan gudun hijira dake nan kusa”

A dawo lafiya tay masa sannan ya fice da hanzari,bodygurd ɗinsa suka mara masa baya.

Ƙarfe huɗu modibbo ya baro office,bayan yayi sallar la’asar,kai tsaye wani gidan abinci ya nufa, domin yaci abinci kamin ya wuce sansanin ƴan gudun hijirar.

A kan idon Zahra motocinsa suka faka,tana can ɗayan gefen titin,da ɗan saurinta ta taho tsallako titin dan tasamu tayi bara agunsu ko zasu taimaka mata,dan kwananta biyu yau bata ci abinci ba,agalabaice take ga ulcer ta data tashi,yanzu ko gabanta ya koma ciwo,yana fitar da wani wari me ɗaga hankali,ko giftawa kayi ta gunta se kaji warin,shiyasa duk inda tayi ake korar ta,hakanne yasa take samun kan bola tayi zamanta,gudun kar akoreta.

Cikin rashin sani mota tayi ciki ciki da ita lokacin da take ƙoƙarin tsallakowar.

Ƙarar burkin motar ne,yaja hankalin mutane da dama, ciki harda modibbo dake ƙoƙarin shiga gidan abincin.

Da gudu me motar daya bugeta yabar gurin be tsaya ba.

A Hanzarce Modibbo yayiwa bodygurd dinshi umarnin su ɗauko wanda aka buge susa a mota,

Hakan sukayi,sede warin da takeyi ne,ya hanasu kuma shiga motar da sauri suka ja baya har modibbo ya ƙaraso.

Warin shi kanshi ya ɗaga masa hankali,shiyasa be tuhumesu me ya hanasu shiga motar ba.

Tsayawa yayi shima yana nazari kamin ya ciro waya ya kira matarsa kasancewarta likita,tana ɗagawa yace”Hajiya akwai emergency yanzu wani ya buge wata mahaukaciya kuma ya tsere,in kaita asibiti ne zaki je yanzu ko in kawota gida?”

“Gaskiya ka kawota gida sabida muhammad be daɗe da dawowa ba bazan iya fita in barshi ba,amma in kukazo naga yanayin lalurar dole se anje asibitin semu tafi”.

Yana kashe wayar ya faɗa motar da kansa yaja,da gudu suka shiga sauran motocin suka mara masa baya zuwa gidan.

Muje zuwa

Surbajo for life.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button