THE GOVERNOR’S WIFE 3

Hajiya Bilkisu ta bi su da kallon mamaki. Saboda waɗannan matan First lady ta zaunar da ita na tsawon awa uku.
“Ba ki tafi ba?” First lady ta faɗa da mamaki
Hajiya Bilkisu ta buɗe baki cikin kaɗuwa.
“Bilkisu Kachallah. Ashe ke ce ake ta damun First lady wai tana da baƙuwa”
Hajiya Hadiza kenan da wannan magana.
“First lady saboda waɗannan kika shanyani kaman kayan wanki” ta yi maganar tana nuna su.
“Tabbas saboda su kuwa. Bilkisu na ji duk abinda kika yi tun kafin na dawo amma ki sani ba zan lamunci hakan ba. Taron matan Gwamnoni aka ce za ayi ba na matan mataimakan Gwamnoni ba. This is the last time da za ki sake haɗa taro idan bana gari”
“Sai da muka gaya ma ta ta bari ki dawo kafin ayi taron nan amma ta ƙi. Wallahi matar Gwamnan Ekiti sai da ta gasa mana magana a wajen taron nan, kin san yarabawa ai”
“Ni! Ni ki ke wa munafurci Hadiza?”
Hajiya Hadiza ta juya kai tana tura baki.
“Ki tsaya iya matsayinki Bilkisu sai a samu zaman lafiya” First lady ta faɗa a fusace
Hajiya Bilkisu ta haɗiyi wani abu daya tokare mata maƙoƙoro.
“Nagode First lady. Dama na zo yi miki barka da dawowa ne amma na ga alama ba ki cancanci gaisuwar ba. Mu kwana lafiya”
Hajiya Bilkisu ta juya da sauri ta fice daga gidan.
A cikin mota danne ƙirjinta ta yi saboda yadda ya ke bugawa yana sukanta. Ba ta iya ɓacin rai ba dan tana farawa zuciyarta ke fara ciwo. Shekarun baya ance tanada hawan jini shiyasa ta ke kaffa-kaffa da duk abinda zai ɓata ma ta rai.
Bayan ta koma gida ba wanda ta kula ta wuce ɗakinta ta sa key sannan ta kwanta akan gado har lokacin ba ta cire hannu a ƙirjin ba dan ji take idan ta cire zuciyarta zai iya bugawa. Ƙarshe ta tashi ta ɗauko maganinta ta watsa a baki ta haɗiye zuwa minti shabiyar maganin ya fara aiki dan bugun ƙirjinta ya fara raguwa.
Idan ba ƙaddara ba da First lady da Hajiya Hadiza da ita Hajiya Kaltumen dukkan su babu sa’anta cikin su. Idan ba muƙami da mazajen su ke riƙe da shi ba babu wadda a cikin su ta taka ƙafarta wajen gata da daraja. *Bilkisu Sani Kachallah* ce fa. Waye bai san tarihin ahalin gidan Kachallah ba. Familyn Kachallah su ne da Jahar Congo gaba ɗaya.
Bilkisu Kachallah ba za ta iya tuna lokacin da bacci ya ɗauketa ba. Ta dai farka tsakar dare ta ganta kwance da kayan jikinta sai alokacin ta tashi ta cire kayan ta saka na bacci sannan ta dawo kan gadon ta zauna dan bacci ya washe a idonta, tunani kala-kala ta zauna yi har Asuba.
***
Shahidah na bacci wayarta ya hau ƙara. Ta sa hannu ta jawo wayar da ke gefen gado saura kaɗan ya faɗo ƙasa.
“Hello” ta faɗa da muryan bacci
“Mine kin tashi kuwa? Na kusa isowa fa”
“Ka manta anyi suspending ɗina jiya”
“Subhanallahi! Ok ok barin zo in gaida Abba sai na wuce office…” ai bai ƙarisa bama Asiya ta kashe wayar saboda baccin da ke cinta.
Da sassafiya Bilkisu ta shirya ta sauko ƙasa. Daga wajen dining room wanda ke haɗe da babban falon ƙasa ɗan ta Junior ya ƙwala ma ta kira “Mommy” ta juya da sauri tana maƙalawa fiskarta murmushin bogi wanda ya ɓoye ɓacin rai da ta ke ciki.
“My boy”
“A’a Nana yaushe kika dawo. Zunairah ya Maman ki?” Ta jera maganar tun kafin ta iso wajen su
“Mommy ina za ki sani kuwa. Jiya ina miki magana haka kika shareni kika wuce sama. Daga baya na je na yita buga ƙofar ki amma shiru ba ki buɗe ba”
“Sorry Dear, jiya na gaji ne dayawa”
“Miyasa Junior ke cin abinci shi ɗaya ina Hansa’u?”
“Hansa’u” ta ƙwala ma ta kira da ƙarfi
“Mommy Airah ce ta aiketa ta kawo mata boiled egg”
“Ok girls barin fita, idan Daddyn ku ya tashi ku ce ma sa na tafi Kachallah House”
Bayan tafiyar Hajiya Bilkisu sai ga Hansa’u ta fito da wani bowl ɗauke da ƙwai guda uku ta ajiye a gaban Zunairah.
Zunairah ta zaro ido ganin ƙwai da ɓawonsa a jiki sai tiririn zafi ya ke
“And what is this? N Luv kinga shirmen wannan crazy old fool ɗin ko?”
Nana ta kalli Hansa’u ta ce ” yanzu Hansa’u ita ki ke so ta cire ɓawon ƙwan kenan?”
“Ke ce ki ka ce na kawo shi kwili-kwili (quickly-quickly) kuma na ji Hajiya na kira shiyasa na kawo shi haka nan”
“Dalla je ki ɓare ƙwan ki kawo” Nana ta faɗa da tsawa.
Hansa’u ta ɗauke kwanon ta koma kitchen da sauri.
Hajiya Bilkisu da ta fito ba ta wuce ko’ina ba sai Kachallah House. Da ta shiga gidan ba ta wuce sashen kowa ba sai sashen mahaifinsu wanda ya ke gefe da asalin cikin gidan, a nan ya ke karɓan baƙin sa a nan kuma ya ke duk wasu harkokin sa. Sashen ya ƙunshi falo guda ɗaya da dining room sai manyan ɗakuna guda huɗu. Ba kowane ya sani ba amma ita Bilkisu ta san akwai falon sirri a gidan wanda Mahaifinsu ke karɓan baƙi na musamman inda ake yin meeting na tsakar dare a ciki.
Shekarunta shabiyar lokacin da ta gano ɗakin, ta je duba wani littafi a library ɗinsa ne hannunta ya danna wani switch a jikin bango sai gashi carpet ɗin wajen ya ɗage. Ba tareda tsoro ba ta leƙa wajen daya buɗe ɗin sai taga matakala ce a wajen. Ta sa ƙafa ta fara taka matakalar har ta nitse ciki dan falon underground ne. Ta san turawa na yin ɗaki ko basement a cikin ƙasa amma ba ta taɓa tunanin sashen mahaifin na su na da irin wannan ba. Falo ne Babba da ya sha kayan alatu fiye da ɗaya falon sai ɗakuna biyu wanda tayi-tayi ya buɗu ya ƙi buɗuwa shiyasa ma ta haƙura ta fito ba tareda ta ga abinda ke ciki ba.
Ta ci sa’a Baban na su na nan dan lokacin ne ma ya ke ƙoƙarin karyawa ga tulin abinci kala-kala da aka ajiye ma sa wanda aƙalla mutum shida za su iya cin abincin su ƙoshi sarai.
“Bilkisu” ya kira sunanta da mamaki.
Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe bakwai da minti arba’in da bakwai.
“Lafiya dai ko?”
“Lafiya Baba”
Bayan ya tambayi lafiyar mijinta da ‘ya’yanta sannan ya tambayi mi ke tafe da ita da sassafen nan dan yasan haka kawai Bilkisu ba za ta nemeshi ba.
“Saifu ne zai miki kishiya?”
“Baba idan kishiya ce ai da sauƙi. Baba tambaya na zo yi”
Alhaji Sani Kachallah ya suɗe romon kan rago da ke shirin gangarowa zuwa gwiwar hannunsa. Wani lokaci idan Mahaifinsu yai wani abun kamar wani faƙiri wanda ba shi da gata ko kaɗan. Yanzu miye na suɗe hannu?. Ta yi saurin kauda wannan tunanin a ranta ta maida hankalinta zuwa abunda ya kawota.
“Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?”
Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata.
“Wace tambaya ce kuma wannan?”
“Baba dan Allah ka amsa min tambayata”
Alhaji Kachallah ya kalli idon ‘yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce ” idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba”
“A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?”
Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe ya ɗaura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido.
“Babu yadda za’ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka ɗaura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar ma su zuwa sun yi nisa sosai”
“Bilkisu!”
“Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and…”
Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi.