Labarai

Yadda aka gano wata karamar yarinya a raye cikin rijiya kwana uku bayan ta bace

An tsinci wata karamar yarinya Lydia Azatyom, mai shekara uku a duniya a cikin wata tsohuwar rijiya, kwanaki uku bayan tayi batan dabo a unguwar Tudun Wada ta Jos, babban birnin jihar Filato.

Shafin Labarun Hausa ya rawaito:

Ganin karshe da aka yiwa karamar yarinya ya auku ne a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, tana wasa da kawayenta a kofar gidan su kafin bacewar ta.

 

Duk wani kokarin iyayenta da makwabta na ganin an gano inda take yaci tura, har sai zuwa bayan kwana uku, lokacin da wani Dauda Dung ya tabbatar da cewa an gano ta.

Shafin LIB ya ambato cewa wani matashi ne ya gano yarinyar a cikin wata tsohuwar rijiya a wani kango dake unguwar.

 

An tattaro cewa matashin yaje kangon ne domin yin bayan gida inda yaji karar alamun motsi a cikin rijiyar wacce bata da ruwa.

 

Ginin kangon dai an dade ba a amfani da shi inda yanzu aka mayar da shi wurin zubar da shara da yin bahaya.

 

 

Lydia ta samu raunika a wajen kanta inda aka garzaya da ita asibiti inda take cigaba da samun kulawar da ta dace.

 

Har yanzu dai ba a da masaniyar cewa ko yarinyar bisa tsautsayi ta fada cikin rijiyar ba ko kuma wani ne ya jefata ciki.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button