Uncategorized

TUBALI Page 11 to 20

Yana tafe cikin gudu kamar maiyin doguwar tafiya.

Yana isa kai tsaye Office ɗin Dr Sajo ya wuce.

Yana ganinshi ya miƙe tsaye tare da cewa.

“A a Ƙanina! Ka iso, ko ina mara lafiyar?”.

Cikin girmamawa da alamun tsohuwar amintaka yace.

“Barka dai Yaya Sajo, dan Allah kayi haƙuri mara lafiyar tana gida.

Ni kuma daga Campany’n Yays Dakata nake, so kafin in koma gida in ɗaukota komai zai iya faruwa, kasan matsalar cutar athsman shiyasa nace bari in biya mu tafi tare. Dan Allah kayi haƙuri”.

Murmushi Dr. Sajo yayi tare da fara tattara abin buƙatarsa yana mai tuno amintaka da mutuntakar da ke tsakaninsa dasu a baya.

Cikin kuma kula da amintaka yace.

“Ba komai ƙanina muje, dama na gama yau bani da aiki”.

Cikin jin daɗi ya juya ya fita, shi kuwa yana biye dashi a baya.

Motarshi suka shiga, shiyasa yake taka motar da kyau.

Tsoro yakeji yasan yadda ciwon ke wahalar da ita.

A can gida kuwa, gaba ɗaya Mom da Abdul sun rikice.

Ita kuwa Jannart tuni ta gama gigicewa ta fita haiyacinta, fuskarta nan tayi jazir.

Sai fuzgo numfashin takeyi da ƙarfi.

Wayar Abdul ne tai ringing yana ɗagawa yace.

“Abba jikin fa ya tsananta”.

“Subahanallahi Abdul gani nan zuwa yanzu”.

Toh yace kana ya katse kiran.

Suna isa kai tsaye cikin gidan sukayi.

Abban na gaba Dr Sajo na biye dashi a baya.

Suna shiga Dr. Sajo ya fara aikinsa, allura yayi mata dan samun dai-dai-ta numfashin ta.

Allah cikin ikonsa kuma a take ta fara sauƙe ajiyan zuciya, lokaci ɗaya jikinta ya fara sakewa.

Sai ga wani irin bacci mai nauyi ya kwasheta…

Kusan a tare suka sauƙe ajiyar zuciya baki ɗayansu.

Cikin kuma sauƙe numfashi Abba yace.

“Alhamdulillah”.

Hakama Mom.

Abdul kuwa shiru yayi yana mai jin tausayin yar uwar tasa.

Dr. Sajo kuwa, harhaɗa kayan aikinshi yayi, kana ya kalli Barrister Kabir, gyaran murya yayi tare da cewa.

“Ciwonta yayi zurfi a jikinta, kuma bata bin doka da ƙaidar maganin yadda ya kamata”.

Da sauri Mom tace.

“Ai ba’a bata magani Allura kawai akeyi mata duk wata”.

Cikin mamaki yace.

“Allura kuma? Toh wacce iriyar Allura ce duk wata kuma!?.”

Cikin sanyi Abdul yace.

“Gaskiya bamu san wacce iriyar Allura bace”.

Da sauri Dr Sajo ya kalli Barrister tare da cewa.

“Wanne Dr ne yake duba ta?”.

Numfashi mai nauyi Barrister ya sauƙe kana a hankali yace.

“Dr. Lukman ne”.

Wani irin shiru Dr Sajo yayi tare da alamun nisan nazari.

Kana yace.

“Ok muje ko Barrister”.

Toh yace kana suka nufi hanyar fita.

Sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Mom dake gyarawa Jannart din kwanciyarta, cikin nitsuwa yace.

“Kada ki damu, zata samu lfy in sha Allah, sannan zamu canza mata Dr da zai na kulawa da ita da kyau”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Mun gode”.

A hankali Dr. Sajo ya juyo ya kalli Barrister Kabir dake jan mota, dan medashi asibitin sa.

“Ƙanina akwai buk’atar a canzawa Jannart likitan da zaina dubata.” 

Cikin nitsuwa Barrister Kabir ya ɗan juyo ya kalleshi tare da cewa.

“Yaya Sajo meyasa!?”.

Kafaɗarshi ya ɗan ɗaga tare da cewa.

“Noh ba komai, kawai dai ciwonta yanada buƙatar gamayyar likitocin zamani bawai a tsaya kan ɗaya ba, a samo wani shima ya gwada kwarewar sa”.

Uhum Dr.Sajo bai tuna cewa da babban Lawyer yake mgna ba.

Cikin fahimtar wani abun Barrister Kabir yace.

“Toh ba matsala in sha Allah za’ayi haka. Amman ina zamu samu likitan?”.

Da sauri yace.

“A wannan mai sauƙine, akwai wani Babban Doctor yarone matashi mai ƙuruciya da sanaiyar ilimin likitanci na juya da yau, kana harna gobe yana bincika yasan aikinsa, mun gamsu dashi, Dr Rayyern Mai-nasara.”

Da sauri Barrister yace.

“Zakayi mana hanyar ganinshi kenan? Dan ance yana da wuyar gani”.

Ya ƙare maganar yana yin parking.

Kai ya ɗan juyo ya fuskanceshi tare da cewa.

“Eh to Gaskiya yana da wuyar samu, saboda yawan aiyuka, kuma a wani sashin bashi da wuyar gani, in har kaje Mai-nasara Hospital ɗinsa, muddin dai yana ƙasar, toh zaka ganshi sai dai ko in baya ƙasar, in kuma bakayi sa’a ba, sai a turaka wurin wani Dr ƙaninsa da kuma amininsa ɗin ba shiba, tunda yanzu aikin Company’s dinsa sun tasoshi gaba, dole ya samo wasu likitocin bayan shi. 

Saɓanin da da shi kaɗai ke jan ragamar asibitin.

Amman idan nasa hannu na baku takarda zuwa gareshi kuna zuwa shi ɗin zaku gani”.

Cikin gamsuwa Barrister yace.

“Alhamdulillah nagode matuƙa Yayana”.

“Haba ba komai Kabir yiwa kaine. Yauwa sai kuma batun allurar da akeyi matan nan, abar yi matashi akwai buƙatar in santa, sannan ina son sanin sunan allurar”.

Ya ƙare zancen yana fita daga cikin motar.

Cikin gamsuwa Barrister yace to.

Kana sukayi sallama.

Ganin lokacin sallan azahar yayine kuma yasa ya nufi masallaci.

Koda aka idar da sallah kuwa.

Gidan yayan nashi ya koma.

                 Ethiopia.

Dr Rayyern Mai-nasara ne. Tsaye cikin wasu tattausan Suit masu masifar kyau da taushi tare da sheƙi.

Inda Riga da wondon suit din suka kasance pink color masu dauke da zane-zanen fari, sai kuma neck tie ɗin shi daya kasance fari, yayinda long sleeve dinsa ma ta kasance white, takalmin dake kafansa kuwa pink color ne mai dauke da harafin R-M.

Sai kuma Diamond watch din dake hannunsa mai ɗan karen sheƙi da tsada.

Wayarshi kirar iphone 12pro max ne saƙale a kafaɗarshi yayinda ya mannata a kunne yana magana.

Kana kuma hannunshi ɗaya na riƙe da System ɗin shi. Daya hannunshi kuma na lallatsashi.

Bisa alamu aiki mai muhimmanci yakeyi.

Ga kuma wani irin masifeffen ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa da yake fitarwa.

Lallausan Sajenshi nan ya kwanta lib, yayiwa kyakkyawar fuskarsa kawanya sai sheƙi yakeyi.

Haka kuma Ɗan madaidaicin bakinsa mai jajayen lips na motsawa a hankali.

Yayinda siraran idanunshi suka fito ras, cikin ɗan siririn glass mai ruwan garai-garai, irin na Doctor’s daya liƙashi cas bisa karan hancinsa.

A hankali ya juyo ya kalli Usman daya shigo cikin alamun shiri.

“Sir gani”. Usaman ya fada anutse.

Da idanunshi yayi masa nuni da jakarsa, yana maici gaba da maganar da yakeyi a wayar.

“Uhumm”. Yace tare da lumshe idonshi.

A can ɗaya sashin kuwa ba tare da damuwa ba Sulaiman yaci gaba da magana.

Sabida sanin haka Allah ya halicce Rayyern mafi akasarin lokuta maganar Uhumm, ne ko eh ko hmm koko a’a

Bai cika yawan surutu ba, da fari gani suke miskilanci ne, sai daga baya suka fahimci abin da gaskene. Dan muddin za’ayi ta surutu ko hayaniya ko magana da ƙarfi a kanshi ko kukan yaro ko babba, a take idanunshi ke kaɗawa suyi jazir, lokaci ɗaya ciwon kai ke rufeshi larurarsa.

Ido ya ɗan juyo yana kallon Usman dake tsaye gefenshi.

Yayinda kuma yake jin Sulaiman na cewa.

“Wallahi Rayyern ni kamanninku ya daina bani mamaki yanzu sai dai tsoro, Allah ko da yayi magana da hausa ko muryarshi iri ɗaya da Ramadan kuma”.

A hankali yace.

“Hmmm Sulaiman social media ka biyewa ko?”.

Da sauri yace.

“Dan Allah tsaya kaji, yaushe zaku dawo?”.

A taƙaice yace.

“Jibi!”.

Cikin fidda numfashi Sulaiman yace.

“Toh gashi kuma shi yaron yau zai taho Nigeria, ni nai zaton yau nema zaku dawo ince Allah yasa ku haɗu a jirgi kaga zahiri, abu kamar an dama kunu an raba har ɗan makolloto yake dashi irin naka fa”.

Ɗan gajeren numfashi mai d’auke da gajiya Rayyern ya fesar tare da cewa.

“Uhmm, it’s Okay a gaida Baby”.

Yana faɗin haka ya katse kiran.

Sai kuma ga wani kiran ya shigo.

Da sauri ya zauna bisa kujerar bayanshi kana ya amsa kiran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button