TUBALI Page 11 to 20
Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu’amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki????????…
Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa.
*Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al’ajabi, Sa’ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya*
Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number’s din ki turo min ta whatsApp number’n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer’n katin 9mobile dan layin nada matsala*
Za’ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za’a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy*
????????Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,????????????????????????????.
Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al’farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k’il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, ????????Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama????????????????????????.
*Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo*
Masifeffen harbawa da babbar jijiyar bayanshi tayi, tare da bugawan ƙirji a jere-a jere, har sau uku.
Rumtse idanunshi yayi da ƙarfi dan bai taɓa jin hakan ba,
Wani irin tsuma fatan saman idanunshi suka farayi, kamar shi yake juya su.
Kanshi ya jingina da marfin motar can ƙasan maƙoshin sa, ya fara mai-mai-ta.
“Hasbunallahu wani’imanwakil, innalillahi wa innailaihi rajiun. Subahanallahi Alhamdulillah”.
Shiru PA yayi tare da ratsa gefe, yana mai kallonshi.
Tsawon daƙiƙu 3 suka ɗauka a haka, kana ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da ambaton sunan Allah.
Bayan ya fita ne kuma PA ya maida marfin motar ya rufe.
Kana Driver’n’shi da gwamnatin kasar ta bashi, da ƴan tsaron shi suka fito suka mara mishi baya.
Yayinda PA dinsa ke gefenshi.
Saida Suka shiga har cikin iya inda matafiya ne zasu shiga.
Kana sukayi musabaha duk suka juya suka tafi.
Shi kuwa da Usman PA Suka nufi cikin farfajiyar jirgin kasan cewar an fara cikiyan matafiya.
A can ɗaya sashin kuwa. Riyyam-nsra ne, tsaye gaban Mammynsu.
Yayinda Zayton ke manne da kanta bisa kafaɗarshi, tana rau-rau da idanu alamun zubda hawaye.
Cikin yanayi na rauni da taraddadi Mammy ta kalli Riyyam-nsra cike da jaddawa ta kamo hannunsa ta riƙe da ƙarfi ido cike da hawaye tace.
“Kasan manufar tafiyarka, itace burinmu da farin cikin rayuwata.
Ka kuma sani ina tsoron duk abinda zai rabani da kai.
Riyyam ka sani, kaine GARKUWAta nida ƴar uwarka.
Lallai tabbas munada ciwo a zuciyarmu.
Ina tsoron kada garin gyaran gira in rasa ido.
Kada ban samu baɗiniba in rasa zahiri.”
Cikin ƙarfin hali da jarunta yace.
“Mammy babu abinda zaki rasa, in sha Allah ƙari zaki samu. Da izinin ubangiji.
Babu wani abu na duniya da zai miki hijabi da mallakinki”.
Cikin zubda hawaye Zayton tace.
“Mammy kin ganshi ko, shi baya tsoro, kada yaje yayi abinda zamu rasashi”.
Hannunshi yasa ya share mata hawaye tare da cewa.
“Koda zaku rasani sai kun samu madadina”.
Da sauri Mammy tace.
“Kamin al’khairi cewa, zaka kiyaye shiga hurumin da ba naka ba, kayi iya abinda ya kaika ka dawo”.
Hannunshi ya ɗaura kan nata tare da cewa.
“Nayi al’ƙawari Mammy na”.
Rungumeshi tayi shida Zayton ɗin jin anata neman matafiya”.
Kanshi ta shafa tare da sa mishi al’barka.
Kana shi yayi ciki, su kuma sukayi baya.
Yana rataye da jakarsa bisa kafaɗa,
yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta matasan zamani.
Kamanninsa da Rayyern sun ƙara bayyana matuƙa, kasan cewar irin shigar Rayyern ɗin yayi.
Wayarshi ya zaro, ya fara ɗabi’ar tasu ta Tiktokers viewing ya farayi, yana jujjuyawa ƙasan jirgin.
Tare da fara, mgn da Hausa.
“Assalamu alaikum Al’ummar Nigeria”.
Sai kuma ya haura ya ajiye wayar bisa steps din marfin jirgin, kana ya dawo baya, ya fara takowa a hankali yanayi yana ɗan rawa, da tsalle.
Mafi akasarin mutanen dake bayansa matasane, shiyasa suka tsaya suna murmushin calikancinsa.
Yana isa gab da wayan second ɗin daya saita na video na cika.
Dan haka yasa hannunshi ya ɗauki wayar kana ya kutsa kai cikin jirgin…
Zaune yake bisa kujera no 23 acan sama VIP, kusa da jikin windown jirgin.
Yayinda Usman ke bayanshi.
Wasu files ya zaro cikin briefcase ɗinsa, tare da biro, a hankali ya sunkuya ya fara buɗe takardun, yana sa hannu a cikinsu ɗaya bayan ɗaya.
Shi kuwa Riyyam-nsra tafiya yakeyi yana ɗan dudduba no ɗin kujerun.
Yana isa kusa da Rayyern ya tsaya tare da cewa.
“Yesss! Kunga ga maƙocina, sarkin aiki har a jirgima aiki yakeyi”.
Bai ɗagoba kuma baici gaba da rubutun da yakeyi ba sai ƙirjinsa dake bugawa.
Jakarsa ya zare a kafaɗarsa ya sakata a mazaunin ta.
Wanda haka yasa saida ya matso kusa da Rayyern.
Yatsun sawun yaron ya zubawa ido cike da mamakin ganin yatsun iri ɗaya sak da nashi yatsun Har nails dinsu.
Da sauri ya ɗan ware idanunshi.
Ganin wani ɗan ɗigon tawadan Allah kan tsakiyar farcen babbar yatsar Riyyam-nsra.
A hankali ya ɗan motsa kafafunshi dan sai yaga kamar ƙafarsa ce.
Shi kuwa Riyyam-nsra zama yayi bisa kujerar dake manne data Rayyern, tare da sauƙe numfashi kana ya lumshe idanunshi saboda wani irin masifeffen bugu da zuciyarsa keyi.
Yayinda gaba ɗaya cikin jirgin kuma kowa ya zauna mazauninsa.
Tsit kowa ya nitsu.
A hankali Riyyam-nsra ya buɗe kwayar idanunshi sabida,
Jin alamun an rufe marfin jirgin kana jirgin ya fara ƙugin tashi.
Shi kuwa Rayyern har yanzu idonshi na kan kyawawan sawun Riyyam-nsra.
A hankali Riyyam-nsra ɗin ya juyo ya kalli gefen da Rayyern ɗin yake.
Da sauri ya ɗan sunkuyo da kanshi ganin inda Rayyern ya fuskanta.
Janye sawunshi yayi tare da cewa.
“Salamu alaikum”.
Da sauri Rayyern ya juyo sabida muryar yaron sak muryar ƙaninsa Ramadan.
Yana juyowa shima Riyyam-nsra yana juyowa ya fuskanceshi.
Wani irin zabura Riyyam-nsra yayi tare da zazzaro idanunshi waje, kana ya yunƙuro zai tashi.
Da sauri ma’aikaciyar jirgin dake bayanshi ta nufoshi da sauri tana cewa.
“Hey Are you okay? please sit down!!”