Uncategorized

TUBALI Page 11 to 20

Ta ƙare mgnar da ɗan sauti sabida lokacin jirgin, yake raba tayoyin shi na gaba da ƙasa, anfi buƙatar kowa a zaune.

Shi kuwa Riyyam-nsra wani irin masifeffen kaɗuwa al’ajabi mmki da tu’jjudine suka rufeshi, gaba ɗaya jikinshi rawayake.

Cikin buɗe baki ya nuna Rayyern da yatsarshi manuniya kana ya nuna kanshi.

Da sauri ma’aikaciyar ta sake cewa.

“Please I say sit down!.”

Jin hakanne da kuma ganin yanda yake baya baya.

Yasa ya koma bisa kujerar ya zauna.

Cikin kaɗuwa da wani irin fuska mai cike da mmki yace.

“Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, daya haliccemu da kamanni iri ɗaya.”

Shiru Rayyern yayi yana mai kallonshi da gefen ido.

Bai iya shiga sabgar da ba ta saba, a rayuwarsa baya taɓa sa kansa a lamarin da bai shafeshi ba.

Da sauri ya juyo jin Riyyam-nsra na cewa.

“Ina ma Mammy na ta ganka.

Allah mai iko.

Inama ace jirgin nan bai tashi ba, da na roƙeka da girman Allah da Manzonsa muje Mammy na taga mai tsananin kama dani.”

Sai kuma ya kalli sajen Rayyern cikin tsananin farin ciki, so, ƙauna, bege, yace.

“In sha Allah nima daga yau zan fara tara saje irin naka”.

Sai kuma ya matso kusa da Rayyern tare da dago wayarshi.

A hankali Rayyern ya ɗan juyo kwayar idanunshi kan fuskarshi ganin alamun zai manna kanshi bisa kafaɗarsa.

Fuskarshi ya tsuke tare da tsareshi da ido.

Da sauri ya kwaɓe fuska tare da karkata kai cikin turo baki yace.

“Na tuba”.

Sai ya ganshi lammanim ƙaninsa Ramadan sak da yayi haka, dan haka Ramadan kanyi mishi duk sanda ya tsareshi da ido.

Ido ya ɗan zubawa lips ɗin shi yana cewa.

“Please kayi haƙuri hoto zamuyi zan nunawa Mammyna ne, zata so ganinka”.

Ya juyo da nufin zaice a a.

Kawai sai yaji Riyyam-nsra ya ronƙofo kanshi da kyau.

Ya manna kansa bisa kafadarsa.

Yana murmushi yayi musu selfie.

Sai ya zama suna kallon juna.

Kafaɗarshi ya ɗan manna da nashi dan jin bugun zuciyarsu ya dai-dai-ta yana harbawa a tare a tare, dib-dib.

Sai kuma ya zuba mishi ido ganin ya taso ya zauna ya juyo ya fuskanceshi da kyau.

Hannunshi ya miƙa mishi tare da sallama.

Dole ya bashi hannu ya kuma amsa sallama tunda horaswar Musulunci ne.

“Sunana Zakariyya amman Riyyam-nsra nakeso a kirani, ni ɗan ƙasar Ethiopia nanne, ban taɓa zuwa Nigeria’n ba sai yau.

Dalilin abokina Nasiru Ahmad zanje.

Kai kuma fa?”.

Fuska ya kuma kwaɓewa ganin ya janye hannunsa bai kuma ce mishi komai ba.

Cikin yanayin shagwaɓa yace.

“Please dan Allah gaya min”.

A nitse ya juyo ya kalli yaron da yakeji.

Sonshi da ƙaunarshi na ratsa mishi jinin jiki da zuciya, haka nan yaji wani aminci na musamman a kan yaron.

Cikin tattausan muryar da irinta yakewa Ramadan mgn yace.

“Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara”.

Ruggumeshi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.

“Nice name. Please Zan iya ce maka Yaya?”  

Kai ya jujjuya mishi alamun a a.

Da sauri yayi rau-rau da idanunshi tare da cewa.

“Dan Allah fa, to me zan ce maka”.

A taƙaice yace.

“Hamma Rayyern”.

Wani irin murmushin jin daɗi yayi tare da cewa.

“Hamma Rayyern”.

Sai kuma ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa da tun tuni yake musu video.

Kusan a tare suka sauƙe ajiyan zuciya lokaci da jirgin ya gama ɗagawa, yayi sama ya rabu da ƙasar Ethiopia.

A hankali ya ɗan juyar da kanshi kana yaci gaba da aikin da yakeyi.

Da sauri ya kuma kalli Riyyam-nsra da ma’aikaciyar jirgin nan tazo tana ce mishi lfy kuwa, ɗazu yake ta rawan jiki ta ƙare mgnar cikin yanayin saninsa da son suyi hoto tare.

Murmushi yayi tare da nuna mata Rayyern kana yayi ƙasa da murya yace.

“Yayana ne zai zaneni wai na cika surutu”.

Murmushi tayi tare da kallon fuskar Rayyern kana tace.

“Ka cika rawar kai, ba kamar yayanka ba.”

Sai kuma ta ɗan kalli Rayyern tare da cewa.

“Sir a rinƙa yi mishi faɗa yaron nan baya jin mgn a TIKTOK”.

Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya kalleta ba.

Hoto sukayi da Riyyam-nsra kana tayi gaba.

Usman PA kuwa yana can baya.

A hankali jirginsu yayi ta keta gajumare, yana ratsa sararin samaniya.

Tafiya ta nisa kowa sabgogin gabansa yakeyi.

Amman banda Riyyam-nsra gaba ɗaya ya shigewa Rayyern shigewa mai tarin yawa.

Ya kuma kasa yakice yaron.

Duk yadda yayi sai yake jin zuciyarsa mai raunice a kan yaron.

Wani irin son yaron yakeji har cikin ƙahon zuciyarshi.

Ga mamakinsa ko yanayin cimar da suka fiso iri ɗaya ne.

Domin tunda Riyyam-nsra ya shigo bakinsa bai zauna banza ba, sweet da chocolate ya cisu iri daban-daban.

Ya lura yaron bakinsa bai zama shiru.

Hoto kuwa yayi musu sunfi hamsin video kuwa sun kai goma.

Haka sukaci gaba da keta hazo…

A nan gida Nigeria kuwa gidan Alhaji Idi Saleh Dakata.

A hankali Jannart ta fara motsi, alamun farkawa daga baccin da allurar ya sa tayi na tsawon.

Awanni biyu da rabi.

A hankali ta fara motsa fatar idanunta da sukayi mata nauyi.

Dai-dai lokacin kuma Barrister ya turo ƙofar ɗakin tare da sallama.

A hankali Mom dake zaune gefenta ta amsa mishi.

“Wa alaikassalam, Barrister ka dawo”.

Cikin kula ya gyaɗa mata kai tare da ƙarasowa bakin gado.

Ido suka zuba mata cikin tausayawa, ganin hawayen dake bin gefen idanunta suna sauƙa har cikin kunnenta.

A hankali Mom tasa tafin hannunta ta fara share mata hawayen.

Ba tare kuma da ta buɗe kwayar idanun nata ba, ta fara sakin Shessheƙan kuka.

Zama Barrister yayi a bakin gadon, tare da kamo hannunta ya riƙe, cike da tausasawa da kulawa yace.

“Sorry Jannart kiyi haƙuri ki dena, kuka dukkan abinda yayi tsananin zaiyi sauƙi”.

Jin muryar ƙanin mahaifin nata, mafi kulawa a gareta ne.

Yasa ta buɗe Idanunta, tare da yunƙurawa, zata tashi zaune.

Da sauri Mom ta tallabota, ta zauna tare da jingina bayanta jikin allon gadon.

Gyara zama Barrister yayi tare da kallon Mom yace.

“Mom Abdul a kawo mata wani abu ta ɗan ci”.

Da sauri Mom ta miƙe tare da cewa. “Toh”. Ta nufi hanyar fita cike da kekyawar niya da zuciya.

Shi kuwa Barrister ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Jannart data gaza tsaida hawayenta.

Murya can ƙasan maƙoshi ta fara mgn.

“Abba ƙirjina yana ciwo! Kaina yana bugawa, tunani ya hanani samun sauƙi, na gaza gano Yah Junaid wanne irin ɗan uwane a duniyar nan.

Anya kuwa Abba Yah Junaid yana da cikekken hankali da sanin haramcin babban fasadin da yake son ai katawa gareni.”

Sai kuma hawaye shar-shar, suka soma zubo mata ta kasa ƙara sa mgnar.

Shi kuwa Barrister cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa da firgici mai birkita tunanin iyaye na gari yace.

“Me kike nufi Jannart wanne irin fasadi kuma?”.

Murya na rawa ta kalleshi cikin rauni tace.

“Abba Yah Junaid fa fyaɗe yake son yamin, a lokuta ma banbanta, yana ƙudirin yi min Fyaɗe, idan na ƙi amince mishi ne, yake yunƙurin kasheni.

Abba cewa yakeyi fa zai kasheni in ban amince da shiba.

Ya kuma ce muddin na gayawa wani zai kasheni.

Wlh Abba zai kasheni.

Abba ya zanyi? Ina zan shiga a rayuwata in samu sauƙi, Ɗan Allah Abba ka rabani da gidan nan in ba haka ba Yah Junaid zai kasheni kuma Daddy ba zai hanashi ba”.

Ta ƙare mgnar cikin tashin hankali.

Da ya ta azzara nitsuwar Barrister Kabir saleh Dakata.

Wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai zafi ta soma tsastsafo mishi.

Cikin tuno abubuwa da dama na rayuwar duniya, ya kamo hannunta tare da fuskantar ta da kyau kana yace.

“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.

Ya kirata sau uku duk da amsa mishi da takeyi.

Cikin yin ƙasa da murya yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button