Uncategorized

TUBALI Page 21 to 30

Masifeffen harbawa da babbar jijiyar bayanshi tayi, tare da bugawan ƙirji a jere-a jere, har sau uku.Rumtse idanunshi yayi da ƙarfi dan bai taɓa jin hakan ba,

Wani irin tsuma fatan saman idanunshi suka farayi, kamar shi yake juya su.

Kanshi ya jingina da marfin motar can ƙasan maƙoshin sa, ya fara mai-mai-ta.

“Hasbunallahu wani’imanwakil, innalillahi wa innailaihi rajiun. Subahanallahi Alhamdulillah”.

Shiru PA yayi tare da ratsa gefe, yana mai kallonshi.

Tsawon daƙiƙu 3 suka ɗauka a haka, kana ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da ambaton sunan Allah.

Bayan ya fita ne kuma PA ya maida marfin motar ya rufe.

Kana Driver’n’shi da gwamnatin kasar ta bashi, da ƴan tsaron shi suka fito suka mara mishi baya.

Yayinda PA dinsa ke gefenshi.

Saida Suka shiga har cikin iya inda matafiya ne zasu shiga.

Kana sukayi musabaha duk suka juya suka tafi.

Shi kuwa da Usman PA Suka nufi cikin farfajiyar jirgin kasan cewar an fara cikiyan matafiya.

A can ɗaya sashin kuwa. Riyyam-nsra ne, tsaye gaban Mammynsu.

Yayinda Zayton ke manne da kanta bisa kafaɗarshi, tana rau-rau da idanu alamun zubda hawaye.

Cikin yanayi na rauni da taraddadi Mammy ta kalli Riyyam-nsra cike da jaddawa ta kamo hannunsa ta riƙe da ƙarfi ido cike da hawaye tace.

“Kasan manufar tafiyarka, itace burinmu da farin cikin rayuwata.

Ka kuma sani ina tsoron duk abinda zai rabani da kai.

Riyyam ka sani, kaine GARKUWAta nida ƴar uwarka.

 Lallai tabbas munada ciwo a zuciyarmu.

Ina tsoron kada garin gyaran gira in rasa ido.

Kada ban samu baɗiniba in rasa zahiri.”

Cikin ƙarfin hali da jarunta yace.

“Mammy babu abinda zaki rasa, in sha Allah ƙari zaki samu. Da izinin ubangiji.

Babu wani abu na duniya da zai miki hijabi da mallakinki”.

Cikin zubda hawaye Zayton tace.

“Mammy kin ganshi ko, shi baya tsoro, kada yaje yayi abinda zamu rasashi”.

Hannunshi yasa ya share mata hawaye tare da cewa.

“Koda zaku rasani sai kun samu madadina”.

Da sauri Mammy tace.

“Kamin al’khairi cewa, zaka kiyaye shiga hurumin da ba naka ba, kayi iya abinda ya kaika ka dawo”.

Hannunshi ya ɗaura kan nata tare da cewa.

“Nayi al’ƙawari Mammy na”.

Rungumeshi tayi shida Zayton ɗin jin anata neman matafiya”.

Kanshi ta shafa tare da sa mishi al’barka.

Kana shi yayi ciki, su kuma sukayi baya.

Yana rataye da jakarsa bisa kafaɗa,

yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta matasan zamani.

Kamanninsa da Rayyern sun ƙara bayyana matuƙa, kasan cewar irin shigar Rayyern ɗin yayi.

Wayarshi ya zaro, ya fara ɗabi’ar tasu ta Tiktokers viewing ya farayi, yana jujjuyawa ƙasan jirgin.

Tare da fara, mgn da Hausa.

“Assalamu alaikum Al’ummar Nigeria”.

Sai kuma ya haura ya ajiye wayar bisa steps din marfin jirgin, kana ya dawo baya, ya fara takowa a hankali yanayi yana ɗan rawa, da tsalle.

Mafi akasarin mutanen dake bayansa matasane, shiyasa suka tsaya suna murmushin calikancinsa.

Yana isa gab da wayan second ɗin daya saita na video na cika.

Dan haka yasa hannunshi ya ɗauki wayar kana ya kutsa kai cikin jirgin…

Zaune yake bisa kujera no 23 acan sama VIP, kusa da jikin windown jirgin.

Yayinda Usman ke bayanshi.

Wasu files ya zaro cikin briefcase ɗinsa, tare da biro, a hankali ya sunkuya ya fara buɗe takardun, yana sa hannu a cikinsu ɗaya bayan ɗaya.

Shi kuwa Riyyam-nsra tafiya yakeyi yana ɗan dudduba no ɗin kujerun.

Yana isa kusa da Rayyern ya tsaya tare da cewa.

“Yesss! Kunga ga maƙocina, sarkin aiki har a jirgima aiki yakeyi”.

Bai ɗagoba kuma baici gaba da rubutun da yakeyi ba sai ƙirjinsa dake bugawa.

Jakarsa ya zare a kafaɗarsa ya sakata a mazaunin ta.

Wanda haka yasa saida ya matso kusa da Rayyern.

Yatsun sawun yaron ya zubawa ido cike da mamakin ganin yatsun iri ɗaya sak da nashi yatsun Har nails dinsu.

Da sauri ya ɗan ware idanunshi.

Ganin wani ɗan ɗigon tawadan Allah kan tsakiyar farcen babbar yatsar Riyyam-nsra.

A hankali ya ɗan motsa kafafunshi dan sai yaga kamar ƙafarsa ce.

Shi kuwa Riyyam-nsra zama yayi bisa kujerar dake manne data Rayyern, tare da sauƙe numfashi kana ya lumshe idanunshi saboda wani irin masifeffen bugu da zuciyarsa keyi.

Yayinda gaba ɗaya cikin jirgin kuma kowa ya zauna mazauninsa.

Tsit kowa ya nitsu.

A hankali Riyyam-nsra ya buɗe kwayar idanunshi sabida,

Jin alamun an rufe marfin jirgin kana jirgin ya fara ƙugin tashi.

Shi kuwa Rayyern har yanzu idonshi na kan kyawawan sawun Riyyam-nsra.

A hankali Riyyam-nsra ɗin ya juyo ya kalli gefen da Rayyern ɗin yake.

Da sauri ya ɗan sunkuyo da kanshi ganin inda Rayyern ya fuskanta.

Janye sawunshi yayi tare da cewa.

“Salamu alaikum”.

Da sauri Rayyern ya juyo sabida muryar yaron sak muryar ƙaninsa Ramadan.

Yana juyowa shima Riyyam-nsra yana juyowa ya fuskanceshi.

Wani irin zabura Riyyam-nsra yayi tare da zazzaro idanunshi waje, kana ya yunƙuro zai tashi.

Da sauri ma’aikaciyar jirgin dake bayanshi ta nufoshi da sauri tana cewa.

“Hey Are you okay? please sit down!!”  

Ta ƙare mgnar da ɗan sauti sabida lokacin jirgin, yake raba tayoyin shi na gaba da ƙasa, anfi buƙatar kowa a zaune.

Shi kuwa Riyyam-nsra wani irin masifeffen kaɗuwa al’ajabi mmki da tu’jjudine suka rufeshi, gaba ɗaya jikinshi rawayake.

Cikin buɗe baki ya nuna Rayyern da yatsarshi manuniya kana ya nuna kanshi.

Da sauri ma’aikaciyar ta sake cewa.

“Please I say sit down!.”

Jin hakanne da kuma ganin yanda yake baya baya.

Yasa ya koma bisa kujerar ya zauna.

Cikin kaɗuwa da wani irin fuska mai cike da mmki yace.

“Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, daya haliccemu da kamanni iri ɗaya.”

Shiru Rayyern yayi yana mai kallonshi da gefen ido.

Bai iya shiga sabgar da ba ta saba, a rayuwarsa baya taɓa sa kansa a lamarin da bai shafeshi ba.

Da sauri ya juyo jin Riyyam-nsra na cewa.

“Ina ma Mammy na ta ganka.

Allah mai iko.

Inama ace jirgin nan bai tashi ba, da na roƙeka da girman Allah da Manzonsa muje Mammy na taga mai tsananin kama dani.”

Sai kuma ya kalli sajen Rayyern cikin tsananin farin ciki, so, ƙauna, bege, yace.

“In sha Allah nima daga yau zan fara tara saje irin naka”.

Sai kuma ya matso kusa da Rayyern tare da dago wayarshi.

A hankali Rayyern ya ɗan juyo kwayar idanunshi kan fuskarshi ganin alamun zai manna kanshi bisa kafaɗarsa.

Fuskarshi ya tsuke tare da tsareshi da ido.

Da sauri ya kwaɓe fuska tare da karkata kai cikin turo baki yace.

“Na tuba”.

Sai ya ganshi lammanim ƙaninsa Ramadan sak da yayi haka, dan haka Ramadan kanyi mishi duk sanda ya tsareshi da ido.

Ido ya ɗan zubawa lips ɗin shi yana cewa.

“Please kayi haƙuri hoto zamuyi zan nunawa Mammyna ne, zata so ganinka”.

Ya juyo da nufin zaice a a.

Kawai sai yaji Riyyam-nsra ya ronƙofo kanshi da kyau.

Ya manna kansa bisa kafadarsa.

Yana murmushi yayi musu selfie.

Sai ya zama suna kallon juna.

Kafaɗarshi ya ɗan manna da nashi dan jin bugun zuciyarsu ya dai-dai-ta yana harbawa a tare a tare, dib-dib.

Sai kuma ya zuba mishi ido ganin ya taso ya zauna ya juyo ya fuskanceshi da kyau.

Hannunshi ya miƙa mishi tare da sallama.

Dole ya bashi hannu ya kuma amsa sallama tunda horaswar Musulunci ne.

“Sunana Zakariyya amman Riyyam-nsra nakeso a kirani, ni ɗan ƙasar Ethiopia nanne, ban taɓa zuwa Nigeria’n ba sai yau.

Dalilin abokina Nasiru Ahmad zanje.

Kai kuma fa?”.

Fuska ya kuma kwaɓewa ganin ya janye hannunsa bai kuma ce mishi komai ba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button