Uncategorized

TUBALI Page 21 to 30

“Insha Allah.” Still ya fada yana me gyara kwanciyarsa. 

“Okay to saida safe kurman dole, mitsss mutun baya gajiya ma da shirun.”  

Sulaiman ya fad’a yana me katse kiran. 

Rayyern kuwa ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da fesar da wani irin numfashi.

“Ashyhhhhh”. wanda kuma yayi hakanne saboda zogi da yakejin yatsar k’afarsa nayi masa, duk da kuwa yasha magani, amma dai har yanzu yakanji k’afar nad’anyi masa zogi.

Labb’an bakinsa ya cije da d’an k’arfi tare da rumtse idanunsa, lokaci daya ya soma tuna yanda yarinyar tayi masa babban b’arna, kuma wai dan saboda tsabar raini, ko hakuri ta kasa basa dan girman kai, sai wuki-wuki da ta soma yi masa da mayun idanunta. 

“Mchewww.” Yayi tsuka abayyane tare da cewa. 

“Da wani dan bakinta kaman na tsuntsu, dama irin wayannan ƴan yaran. Sam ba kai daya garesu ba.” 

Yakai karshen maganan yana sake gyara kwanciyarsa, tare da sakin kowanni irin tunani ya kama ambaton sunan Allah Acikin ransa, da haka bacci ya d’auke sa, yau ko samun daman duba system d’inshi baiyi ba. 

        Taheer Quest Palace.

Riyyam-Nsra ne kwance akan makeken bed din dake cikin d’akin hotel d’in daya kama.

12:30 am kenan amma har yanzu wayarsa kirar iphone 11pro ne ke rik’e ahannunsa, Yayinda yayi kwanciyar nan irinta rub da ciki, gaba d’aya hankali, tunani da kuma nutsuwarsa ya badasu ne ga wayar tasa, Inda yake ta receiving DM da kuma comments na mutane, akan videos d’in daya sake d’azu na shigowarsa Nigeria, inda mutane da yawa kanyi masa message akan cewar, suna matuk’ar son su had’u dashi, ciki kuwa harda y’an mata masu tambayarsa awanni masauk’i yake, domin acewarsu zasu kawo masa ziyara, burin mutane da yawa shine su had’u dashi suyi videos, wasu kuwa zallan kyawunsa ne yake rud’arsu, wanda hakan yasa suke bayyana maitarsu afili, ko kunyar kai da addininsu basaji, amatsayinsu na musulmai, kuma yaya mata, wanda kowa yasani Mace nada matuk’ar daraja, amma Ina wasu matan kam haka suke watsar da kansu kamar shara a bola. 

Shikuwa Riyyam nsra ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewar, mutanen Nigeria nada matuk’ar mutumci da kuma iya karrama bak’o, sannan da yawansu suna nuna masa k’auna k’warai. 

 

Bayan ya gama amsa DM na mutane ne kuma yayi posting videos d’insa, wanda yayi musu shida Rayyern, Yayinda a k’asan videos d’in yayi godiya da irin karamcin da Rayyern d’in yayi masa, wayyo Allah ai kuwa kaman jira mutane suke, suna gama watching na videon ya fara samun new comments and DM, wanda shi kansu bazai iya amsasu duka ba, Yayinda mafi yawancin mata kuma suka sake haukacewa, nanfa kowacce ta fito ta fara maganganu kala-kala, harda masu tambayarsa wai dan Allah ko zai had’asu da kyakkyawan yayanshi. 

Shidai ya gani amma baiyi reply ba.

Bakin shi ya dan zumbura gaba tare da cewa.

“Wayyo wannan Hamma Rayyern ɗin ya kashemin kasuwa fa, ji duk an shareni sai mgnarsa ake,”.

Ya kare mgnar da murmushi

Ana Cikin hakanne kuma saiga k’iran Nasir Ahmad ya shigo cikin wayar tasa.

Koda ya d’aga hira suka sha inda Nasir Ahmad ya dinga yi masa fadan cewa bai Kirasa ba, da kuma mai yasa zai sauka a hotel, saboda da ace yakirasa da bazai taba bari ya sauka a hotel ba.

Hakuri Riyyam din ya basa, daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu, ananne Nasir din ke tambayan a Riyyam hotel din daya sauk’a, bayan ya fad’a masa cewa a Taheer ya sauk’a ne kuma sukayi sallama, inda Nasir din ya shaida masa cewar, Gobe Insha Allah zaizo nan Taheer Guest Palace din, ya d’aukesa su tafi gidansu…!

Uhummmmm, akwaifa abu a wanga littafin, fatana dai Allah ya bamu aron rai da lfy, mu gama lfy, amman kam ku shirya karatu da murmushi a fuskokinku????????????

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button