Uncategorized

TUBALI Page 21 to 30

Cikin yanayin shagwaɓa yace.

“Please dan Allah gaya min”.

A nitse ya juyo ya kalli yaron da yakeji.

Sonshi da ƙaunarshi na ratsa mishi jinin jiki da zuciya, haka nan yaji wani aminci na musamman a kan yaron.

Cikin tattausan muryar da irinta yakewa Ramadan mgn yace.

“Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara”.

Ruggumeshi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.

“Nice name. Please Zan iya ce maka Yaya?”  

Kai ya jujjuya mishi alamun a a.

Da sauri yayi rau-rau da idanunshi tare da cewa.

“Dan Allah fa, to me zan ce maka”.

A taƙaice yace.

“Hamma Rayyern”.

Wani irin murmushin jin daɗi yayi tare da cewa.

“Hamma Rayyern”.

Sai kuma ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa da tun tuni yake musu video.

Kusan a tare suka sauƙe ajiyan zuciya lokaci da jirgin ya gama ɗagawa, yayi sama ya rabu da ƙasar Ethiopia.

A hankali ya ɗan juyar da kanshi kana yaci gaba da aikin da yakeyi.

Da sauri ya kuma kalli Riyyam-nsra da ma’aikaciyar jirgin nan tazo tana ce mishi lfy kuwa, ɗazu yake ta rawan jiki ta ƙare mgnar cikin yanayin saninsa da son suyi hoto tare.

Murmushi yayi tare da nuna mata Rayyern kana yayi ƙasa da murya yace.

“Yayana ne zai zaneni wai na cika surutu”.

Murmushi tayi tare da kallon fuskar Rayyern kana tace.

“Ka cika rawar kai, ba kamar yayanka ba.”

Sai kuma ta ɗan kalli Rayyern tare da cewa.

“Sir a rinƙa yi mishi faɗa yaron nan baya jin mgn a TIKTOK”.

Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya kalleta ba.

Hoto sukayi da Riyyam-nsra kana tayi gaba.

Usman PA kuwa yana can baya.

A hankali jirginsu yayi ta keta gajumare, yana ratsa sararin samaniya.

Tafiya ta nisa kowa sabgogin gabansa yakeyi.

Amman banda Riyyam-nsra gaba ɗaya ya shigewa Rayyern shigewa mai tarin yawa.

Ya kuma kasa yakice yaron.

Duk yadda yayi sai yake jin zuciyarsa mai raunice a kan yaron.

Wani irin son yaron yakeji har cikin ƙahon zuciyarshi.

Ga mamakinsa ko yanayin cimar da suka fiso iri ɗaya ne.

Domin tunda Riyyam-nsra ya shigo bakinsa bai zauna banza ba, sweet da chocolate ya cisu iri daban-daban.

Ya lura yaron bakinsa bai zama shiru.

Hoto kuwa yayi musu sunfi hamsin video kuwa sun kai goma.

Haka sukaci gaba da keta hazo…

A nan gida Nigeria kuwa gidan Alhaji Idi Saleh Dakata.

A hankali Jannart ta fara motsi, alamun farkawa daga baccin da allurar ya sa tayi na tsawon.

Awanni biyu da rabi.

A hankali ta fara motsa fatar idanunta da sukayi mata nauyi.

Dai-dai lokacin kuma Barrister ya turo ƙofar ɗakin tare da sallama.

A hankali Mom dake zaune gefenta ta amsa mishi.

“Wa alaikassalam, Barrister ka dawo”.

Cikin kula ya gyaɗa mata kai tare da ƙarasowa bakin gado.

Ido suka zuba mata cikin tausayawa, ganin hawayen dake bin gefen idanunta suna sauƙa har cikin kunnenta.

A hankali Mom tasa tafin hannunta ta fara share mata hawayen.

Ba tare kuma da ta buɗe kwayar idanun nata ba, ta fara sakin Shessheƙan kuka.

Zama Barrister yayi a bakin gadon, tare da kamo hannunta ya riƙe, cike da tausasawa da kulawa yace.

“Sorry Jannart kiyi haƙuri ki dena, kuka dukkan abinda yayi tsananin zaiyi sauƙi”.

Jin muryar ƙanin mahaifin nata, mafi kulawa a gareta ne.

Yasa ta buɗe Idanunta, tare da yunƙurawa, zata tashi zaune.

Da sauri Mom ta tallabota, ta zauna tare da jingina bayanta jikin allon gadon.

Gyara zama Barrister yayi tare da kallon Mom yace.

“Mom Abdul a kawo mata wani abu ta ɗan ci”.

Da sauri Mom ta miƙe tare da cewa. “Toh”. Ta nufi hanyar fita cike da kekyawar niya da zuciya.

Shi kuwa Barrister ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Jannart data gaza tsaida hawayenta.

Murya can ƙasan maƙoshi ta fara mgn.

“Abba ƙirjina yana ciwo! Kaina yana bugawa, tunani ya hanani samun sauƙi, na gaza gano Yah Junaid wanne irin ɗan uwane a duniyar nan.

Anya kuwa Abba Yah Junaid yana da cikekken hankali da sanin haramcin babban fasadin da yake son ai katawa gareni.”

Sai kuma hawaye shar-shar, suka soma zubo mata ta kasa ƙara sa mgnar.

Shi kuwa Barrister cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa da firgici mai birkita tunanin iyaye na gari yace.

“Me kike nufi Jannart wanne irin fasadi kuma?”.

Murya na rawa ta kalleshi cikin rauni tace.

“Abba Yah Junaid fa fyaɗe yake son yamin, a lokuta ma banbanta, yana ƙudirin yi min Fyaɗe, idan na ƙi amince mishi ne, yake yunƙurin kasheni.

Abba cewa yakeyi fa zai kasheni in ban amince da shiba.

Ya kuma ce muddin na gayawa wani zai kasheni.

Wlh Abba zai kasheni.

Abba ya zanyi? Ina zan shiga a rayuwata in samu sauƙi, Ɗan Allah Abba ka rabani da gidan nan in ba haka ba Yah Junaid zai kasheni kuma Daddy ba zai hanashi ba”.

Ta ƙare mgnar cikin tashin hankali.

Da ya ta azzara nitsuwar Barrister Kabir saleh Dakata.

Wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai zafi ta soma tsastsafo mishi.

Cikin tuno abubuwa da dama na rayuwar duniya, ya kamo hannunta tare da fuskantar ta da kyau kana yace.

“Jannart! Jannart!! Jannart!!!”.

Ya kirata sau uku duk da amsa mishi da takeyi.

Cikin yin ƙasa da murya yace.

“In sha Allah, Junaid bazai kashe kiba, da izinin ubangiji sai kin rayu, rayuwa mai Al’barka domin ke ayace, kuma izinace sannan taƙin shaida mai ƙarfi”.

Hannunta ya kuma riƙewa cikin irin sona uba da ɗiyarsa yace.

“Jannart zaki rayu cikin aminci. 

Domin Ubangijin daya raya Annabi Musa acikin gidan Fir’auna cikin lfy da aminci.

Shiya rayaki a gidan nan cikin lafiya da aminci.

Ya rigada lokacin ya ƙurewa Magautan, bazasuyi nasaraba, dan sunyi nasararsu tun shekarun baya sun gama nasara, yanzu nasarar tamu ce. 

Gsky zatayi halinta, in sha Allah zanci gaba da zame miki jigo. Kuma zan nema miki GARKUWA, cikin gaggawa kafin su juyo garemu”.

Shiru tayi tana jin kalaman ƙanin mahaifin nata, sai dai ta kasa sama musu mizanin da zata aunasu ta ajiyesu ta fahimci manufarsu.

Gogewar hausarta batayi surfin ta Ƙanin mahaifin nataba.

Cikin ruɗanin da kalamanshi suka saka mata tace.

“Abba ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ka sake roƙon Daddy ya bakani ko zai yarda, in koma gidanka.”

Cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.

“Jannart sake roƙar tashi tamkar wasa da rayuwarki ne, kamar dai kusanto da a …”.

Da sauri ya haɗiye ragowar mgnar sanin ƙwaƙwalwarta bazata fahimci zancen nasa ba.

Ita kuwa cikin sanyi ta zuba mishi ido.

Dai-dai lokacin kuma Mom ta shigo da tray a hannunta, cup ɗin tea ne mai kauri, sai soyayyan irish da ƙwai.

Cikin nitsuwa tace.

“Abba to..”.

Hannu ya ɗan ɗaga mata tare da cewa.

“Ya isa da yamma zan dawo muyi mgn Jannart kada ki kuma yin kuka”.

Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye.

Kai kawai ta gyaɗa mishi kana ta bishi da ido har ya fita.

Bayan ya fita Bathroom ta shiga, ruwa ta ɗan watsa, bayan tayi brosh kana ta fito.

Ba laifi ta ji sauƙin sosai numfashin ta ya dai-dai-ta.

Tea ɗin kawai ta iya sha.

Kana ta koma ta kwanta dan Alllurar bata ida saketa ba.

Can cikin bacci taji wayarta na suwa.

“Mahmoud”.

Tace tare da amsa kiran.

Nan yake shaida mata cewa.

Dr Rayyern Mai-nasara yana hanyar dawowa Nigeria tun safe jirginsu ya taso.

Zuwa azahar zasu sauƙa Abuja.

Kuma yau ɗin zasu shigo Kano cikin alamun bacci tace.

“Toh ya akayi kuma lbrin ya sauya Mahmoud ba sai jibi ba kace?”

Gyara zamanshi yayi tare da cewa.

“Uhumm kin kuwa san waye Dr Rayyern, mutun yana nan tamkar Wahainiya gane shirinsa ko manufarsa fa wuyane dashi.

Ke dai in kin samu dama kiyi ƙoƙarin zuwa Airport da yamma wata ƙil a dace, zan turo miki hotuna Yah Usman PA Yayan Abokina Deen wanda yayisu a bayan motocin Dr Rayyern ɗin so sai ki ɗauki number’s ɗin motocin ta wannan hanyar zaki iya samun damar bibiyarsa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button