TUBALI Page 21 to 30
Cikin sanyi tace.
“Toh Ngd matuƙa”.
Daga nan sukayi sallama.
Salman ta kira yana ɗagawa yace.
“Ya jikin namu?”.
Cikin sanyi tace.
“Da sauƙi waya gaya maka?”.
“A’isha Lawal ce ta gaya min tace ɗazu data kira Mom ce ta ɗaga wai jikinki ya tashi.”
Ayyah tace a taƙaice kana ta mishi bayanin da Mahmoud ya mata ta ƙara da cewa.
“Ka shirya da yamma muje Airport ɗin bari in turoma hotunan”.
Toh yace kana sukayi sallama.
Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin international Airport Abuja.
Bayan wasu ƴan daƙiƙu, aka fara fitowa.
Mutun kusan 21 suka fito.
Kana Rayyern ya sako ƙafarsa ta dama kan matakalan forko.
Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali tare da zuƙan iskar ƙasarshi abin sonshi da al’faharin shi.
A hankali ya fara takowa yana sauƙa cikin haiba.
Da sauri ya ratayo jakarsa a kafaɗa tare da biyoshi a baya da gudu.
Usman kuwa shima jakarsu ya ratoyo kana ya biyoshi a baya.
da sauri ya matsoshi.
Juyowa yayi jin an riƙe mishi hannun damanshi.
“Hamma Rayyern daga nan wanne state ɗin zaka tafi”.
Ya rasa gane meyasa zuciyarsa ke bawa yaron amanna ko dan kamar da sukeyi ne.
Sam bai shiryawa amsa mishi ba kawai yaji lips ɗinshi sun furta.
“Kano”.
Wani irin tsalle yayi tare da cewa.
“Yesssss! Nima Kano zan tafi ai”.
Cike da mamaki Usman ya nufosu har yana tuntube tare da cewa.
“Sir wannan fa?”.
Juyowa yayi ya kalli Usman da salon.
Baya son shisshigi.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri ya dawo kusa da Usman hannu ya bashi tare da cewa.
“Ni ƙaninsa ne”.
Baki buɗe Usman ya bishi da ido.
Daga nan masallacin cikin Airport ɗin suka wuce, ganin azahar tayi har lokacin yaso zarcewa.
Suna idar da salla Usman ya miƙe da nufin fita ya samo abinci.
Dan yasan ubangidan nasan bazai buƙaci abinci yanzuba.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Riyyam-nsra tare da cewa.
“Bishi kuje Restaurant”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Bana jin yunwa”.
Kai kawai ya gyaɗa mishi.
Nan suka zauna har la’asar tayi.
Bayan an idar da sallane kuma, suka koma ciki.
Domin shiga jirgin da zai wuce Kano.
Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai jirginsu ya tashi daga birnin tarayyar Nigeria zuwa Kano ta dabo tumbin giwa.
A nan cikin Kano kuwa.
Jannart ce zaune cikin motar, Salman kana shi kuma yana gaba gefe.
Baba Ado dake jansu.
Yayinda sauran garadan dake tsaronta, suke hangame da baƙi a zatonsu tana can cikin ma’aikatar nasu, dan sam basu lura da lokacin da ta fitoba, koda yake Salman ne ya bawa Baba Ado key kana ya jawo motar har zuwa bakin mashigansu ya kawo mishi.
Shiyasa suka fita, basu ganeba.
Kai tsaye filin jirgin sama na malam Aminu Kano suka nufa.
Sosai kuwa Jannart tayi kyau acikin shigar pallazo da kuma tight shirt din dake jikinta, wanda ya bayyana lafaffen cikinta, kasancewar kuma rigar nata na d’an bayyana nipples dinta ne, yasa ta daura wata Navy blue fashion top akan shigar ta ta, wanda tsawonsa ya kawo har guiwanta, Yayinda ak’afanta take sanye da wani navy blue hill shoe, na company’n gucci mai kyau da tsada da uban tsini, akanta kuwa wani had’add’en medium vail ne wanda ya sauko harkan kirjinta.
Sam akan fuskarta babu wani kwalliya sosai, saidai kuma hakan bai hana zallar kyawun fuskarta bayyana ba, Yayinda small lips dinta suka sha peach lipstick, acikin jikinta kuwa wani sassanyan k’amshi ne yake tashi.
Suna shiga cikin Airport ɗin sukayi paking a Airport parking.
Kana suka wuce suka nufi cikin.
Bayan isarsu da kamar 5 minute, jirginsu Rayyern yayi sauƙar angulu.
Bayan yan daƙiƙu ne kuma matafinyan suka fara fitowa.
Da sauri Usman ya matso kusa da uban gidan nashi, cikin yin ƙasa da murya yace.
“Sir in kira driver?”
Shiru yayi ganin ya ɗan kaɗa mishi yatsarshi manuniya.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sassarfa yake biye da Usman a baya.
A haka har suka fito asalin filin da matafiya kan zauna su jira masu tarbarsu.
Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli taron mutanen, yatsarshi yasa ya ɗan gyara zaman farin glass ɗin dake idonshi.
Gefen lips ɗinshi na ƙasa ya ɗan kamo ya ɗan tauna a hankali.
Da sauri kuma ya ɗan juyo ya kalli bayanshi.
Inda ya hango Riyyam-nsra can baya yana ɗan tahowa yana waige waige a alamun shi yake nema.
Gabanshi ya nunawa Usman tare da yin mgna can ƙasa.
“Ƴan jarida ne, zanbi nan, in sun tsareka kaji dasu.”
Yana faɗin haka, ya ratsa yabi yar siririyar hanyar dake gefen damanshi.
Shi kuwa Usman ya nufi hanyar fitan.
Jannart kuwa da sauri cikin tsananin razana ta koma bayan Salman tare da yin ƙasa da kanta murya can ƙasa tace.
“Innalillahi Salman gacan Hakim abokin Yah Junaid idan ya ganni zai gaya mishi.”
Sai kuma ta zaro ido jikin tashin hankali ta dafe kirjinta tare da cewa.
“Na shiga ukuna tare suke da Yah Junaidu ma gashi can bayanshi”.
Da sauri Salman ya ɗan kalli gabanshi kana ya juyo.
Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi sabida hango Hakim Da Junaidu sun nufosu gadan-gadan.
Jujjuyawa tayi.
Ganin wata ƴar siririyar hanyar ne gefen hagunta, wacce nan Rayyern yabiyo.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ratsa cikin ƴar hanyar ta ɓacewa ganin su.
Nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe, tare da ci gaba da tafiya cikin yar siriyar kusurwar.
Tana tafiya tana wai-waye da juyawa tana kallon bayanta.
Shi kuwa Rayyern, cikin ɗan sassarfa yake tafiya.
Saboda so yake kafinma Usman da Riyyam-nsra su fito, ya shiga taxi ya tafi.
Tafiya yake yana dai-dai-ta kan files da takardun da yayi ta aikin rattaɓa musu hannu a cikin jirgi.
Haka yasa bai lura da gabansa.
Ita kuwa Jannart tafiya take tana wai-waye shiyasa bata ganin gabanta.
Jin kamar takun wani a bayanta ne kamar ana boyota, kuma yasa ta ƙara saurinta.
Dai-dai lokacin kuwa Rayyern ya iso gab da ita.
Jin ana ce. Ke! Ke!! Yasa ta juya da nufin zata arta da gudu.
Sai kawai ta jita jikin mutum sunyi karo.
Goshinta ya bugi gemunshi da azaban ƙarfi.
Take files da Takardun hannunshi suka watse.
Yayinda ita kuma tayi tangal-tangal ta koma baya zata faɗi ƙasa, da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin sauti mai cike da tsoro, hade kuma dasa hannunta da nufin dafe ginin dake wajen, dan kare kanta daga faɗuwa ƙasa.
Kawai sai ta kamo kwalan rigarshi ta gefe ta cikin da kuma Suit ɗin dake saman da ƙarfi.
Pet-pet haka boturan jikin rigar duk suka ɓalle, kab suka watso ƙasa, hakan yasa gaba ɗaya rigunan jikinshi suka buɗe.
Cikin wani irin masifeffen takaici yasa hannunshi ya fisge hannunta dake shaƙe da gefen kwalar rigarshi.
Ya yarfa hannun tare da zuba mata wani irin masifeffen….!
Kuyi hakuri rashin jina da wuri.
Rayyern da ban Riyyam-nsra da ban ai sunayenma ba iri ɗaya bako.
Free PAGE ne wannan.
By
*GARKUWAR FULANI*
By
*GARKUWAR FULANI*????????????????????????????????????????????
*TUBALI*
PAGE 5
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????????????????????????????????????
*FREE PAGE NE*
*Littafin TUBALI na kuɗine, ki biya 500 in saki a ƙaramin group, ko kuma ki biya 1000 in saki Special Group, wanda cikin mako biyu kacal zamu ƙare part 1. Ki turo kuɗin ta asusuna na GTBank, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan numben whatsApp na 09097853276. Ki saya ki karanta cikin salama ba tare da hakkina a kankiba, in bazaki sayaba ga littatafai nan birjik kamar jompa a Jos sai ki samu na kyauta ki karance salim alin*