Uncategorized

TUBALI Page 21 to 30

Kallo mai cike da tarin takaici ya watsa mata, rikitattun idanunshi cikin nata kwayar idanun kasan cewar suna fuskantar juna.

Wani irin azabebben zogi lips ɗinshi sukeyi sabida yadda ta bugi gemunshi da goshinta, har hakan yasa lips ɗin suka haɗe da kyawawan haƙorinsa.

Zut-zut haka yakeji suna zogi.

Da raɗaɗi, wani irin tafasa zuciyarshi takeyi tare da harbawa, files ɗin campany’nsa da yake da matuƙar mahimmanci da suke watse a ƙasa ya zubawa idanu.

Wani irin mugun kallo ya kuma watsa mata duk a cikin abinda baifi 5 second ba.

Idonshi ya kai bisa hannunta dake shaƙe da kwalar rigarsa ta gefe.

Hannunshi na dama yasa ya damƙo hannunta da azaban ƙarfi, kana ya yarfashi.

Wanda sanadin fizge hannun nata da yayi kuma wayarshi, kirar iphone 12 pro max dake cikin al’jihun rigarsa ya faɗo ƙasa.

Kana ita kuwa Jannart wani irin masifeffen karkarwa jikinta keyi.

Yayinda kuma gaba ɗaya hankalinta kecan baya.

Sabida masifar tsoron Yah Junaid da ta tabbatar muddin ya ganta sai ya kusan kasheta.

Haka yasa gaba ɗaya ma hankalinta baya kanshi, bare taga ta’adin da ta aikata mishi.

Tangal-tangal tayi lokacin daya yarfa hannun nata, da sauri ta dafe ginin gefenta tare da gyara tsayuwarta, cikin rashin sa’a ta sauƙe ƙafarta ta hagu kan glasss ɗin fuskar wayar tashi, da tsinin takalminta mai masifar ƙarfi.

Saurin yin ƙasa da kansa yayi, sakamakon jin ƙaran sautin fashewar glass din wayarsa, wanda take dauke da screen mai tsada. 

Idonshi ya rumtse da ƙarfi.

Yana mai jin tamkar ya shaƙe wuyanta sai tayi sanyi.

Sam Ba ɗaruruwan kudin wayar yake tunawa ba, muhimman abubuwansa dake cikin wayar yake tunawa wanda yasan tabbas zai iya rasa wani abun.

Ita kuwa Jannart da sauri ta sunkuyo jin ta taka wani abu kuma tsantsi ya ɗebi ƙafarta.

Da sauri ta janye ƙafar tata cikin wani akasin kuma, ta sauƙe tsinin takalmin nata, kan tattausan ƙafarsa dake cikin tattausan takalmin fata,

dai-dai kan farcen babbar yatsarshi ta kafa tsinin takalmin tare da sake iya nauyi ta.

“Auchhhhhh!!”. Ya sake wani irin sauti tare da rumtse idanunshi da ƙarfi, hade kuma da taune lips ɗin shi na kasa dake ta zogi tun buge shi da tayi.

Ƙara rumtse idanunshi yayi sabida wani irin,

masifeffen azaba da yaji tun daga tsakiyar kanshi har cikin ƙoƙon ranshi, kana ya iso kan babbar yatsar tashi.

Da sauri ta kuma janye ƙafarta, tare dayin baya kaɗan tana mai wai-wayen bayanta, alamun sam hankalinta baya gabanta sai baya.

Wani irin kallo ya zubawa tarin ɓarnar da tayi mishi,a lokaci ɗaya ta lalata mishi abubuwa da yawa, har lfyarshi bai tsiraba

Ta nuƙurƙusashi tamkar wanda yayi karo da tirela.

Wani irin nannauyan numfashin ta sauƙe ganin Salman ne ke biye da ita a bayan yana ce mata ke ɗin.

Da sauri Salman ya iso garesu.

Ganin yadda suke tsaye cirko-cirko.

Rayyern ya kalla cikin nitsuwa,

tare da fahimtar karo sukayi, cikin sauri yace.

“Innalillahi karo kukayi, bawan Allah kayi haƙuri.”

Ya ƙare mgnar yana sunkuyawa files din ya fara tattarewa, yana mai cewa.

“Subahanallahi, wayarka duk ta dare, Jannart garin ya akayi haka”.

Ita dai Jannart sai numfashin tsoro take sauƙewa, ta gaza cewa komai sabida ganin wani irin mugun masifeffen kallon da yake watsa mata, sai yanzu idonta ya kai ga ta’adin da tayi mishi.

Da sauri tayi ƙasa da kanta dan bata da jarumtar da zata iya jurar kallon nan daga kwayar fitinennun idanunshi.

Yatsun ƙafarshi ta tsurawa ido ganin yadda suke tsuma alamun tsananin azaba, ga kuma jini da take tsastsafowa.

Dib-dab-dib-dab haka taji zuciyarta na bugawa a 170. 

Salman kuwa cikin yanayin damuwa ya miƙowa Dr Rayyern Mai-nasara Takardun da wayar cikin yanayin jin ba daɗi yace.

“Dan Allah da Manzonsa kayi haƙuri bawan Allah”.

Idonshi ya rumtse da ƙarfi tare da miƙa hannunsa ya amshi takardun da wayar.

Sabida Salman ya gama dashi, tunda yace.

“Dan Allah da Manzonsa yayi haƙuri, to ya zame masa wajibi kuma dole yayi haƙuri sabida wannan shine mafi ƙololuwar al’farmar da mutun zai nema a wurin musulmi yayi mishi, wannan shine kalaman da Abban sa ke cemasa a mafi akasarin lokuta.

Amman badon haka ba yaso ya yarfawa wannan birkitacciyar yarinyar mari ɗaya rak, taji salon yadda tafin shi yake, so yayi ya yarfa mata mari da hannun hagunshi wanda yasan tabbas sai ta saki fitsari sabida ya lura bata iya bada haƙuri ba, kuma bata da nitsuwa.

Wani irin juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo da fuska a murtuƙe,

“Mchewwwww “. Yaja mata wani irin tsaki tare da yin kwaffa kana ya juya yayi gaba ba tare da yayiwa Salman mgn ba.

Cikin kaɗuwa Salman yace.

“Jannart ya akayi haka, kinga asarar da kikayi mishi kuwa, nasan tabbas duk yadda akayi kece da laifin karon tunda kin hango mala’ikan ɗaukan ranki, kina gudu kina rawan jiki kina wai-waye kinzo kin mishi ta’adi.

Kin kuma san kuɗin wayar nan da kika fasa mishi sarai amman ko a jikinki. 

Sannan kin tsaya kinyi shiru, wannan wanne irin tsorone kijeyiwa Junaid?”

Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe, tare da lumshe idanunta a hankali cikin nutsuwarta da ta fara dawowa tace.

“Allah ya bashi haƙuri, wlh Salman na rasa ta ina zan fara bashi haƙuri ne, kagafa wani irin kallon da yakemin tamkar zai shaƙeni ya kasheni, tsoronshi naji.

Sannan kuma duk tsorona kada Yah Junaid ya ganni, wlh in ya ganni a nan kuma bance zanzo nanba bisa aikina sai ya kusan kasheni, duk allurarsa ta sojoji a kaina zai direta.”

Cikin takaici Salman yace.

“Shike nan ai mun rasa damar farko, dan yanzu dai da wuya in Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara bai wuceba tun tuni, matsalar ba sanin fuskarsa akayi ba bare ace da mun ganshi zamu ganeshi.

Dama dole bincike zamuyi da numbers din motocinsa, da aka bamu zamu ganeshi mubi bayanshi muga gidansu. Kinga har lau dai tsoron Junaid yana hanaki nasara.

Har nima ta shafeni.”

Cikin takaici tace.

“Toh ya zanyi?”.

Kwaɓe fuskarsa yayi tare da juyawa yayi baya.

Itama kuwa juyawa tayi tabi bayanshi.

Riyyam-nsra kuwa, ɓat RAYYERN da Usman PA suka ɓacewa ganinsa.

Gaba ɗaya ya gama zagaye wurin babu su ba dalilin su.

Wani irin masifeffen kuka yakeji tun daga can ƙasan maƙoshi sa yana taso mishi.

Saboda lokaci daya yaga samu ya kuma ga rashi.

Kana layinshi bazaiyi aiki a nanba bare ya kira Mammy ya sanar mata halin da yake ciki.

Hakan yasa yake jin wani irin ƙuncin rai.

Gefe ya koma ya zauna bisa kujera, tare da maida kanshi ya jingine yana mai jin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi.

Da sauri Salman ya nunawa Jannart Riyyam-nsra tare da cewa.

“Ikon Allah Jannart ga mutuminki”.

Juyowa sukayi suna kallonshi.

Shidinma kuwa Idanunshi da sukayi ja ya buɗe yana kallonsu.

A hankali Jannart tace.

“Kai ba shi bane, sai dai ko ƙaninshi”.

Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tsaye tare da rataya jakarshi bisa kafaɗa.

“Assalamu alaikum”.

Yace yana miƙawa Salman hannu.

“Wa alaikassalam”.

Yace tare da bashi hannu.

Sukayi musabiha, cikin sanyi Jannart tace.

“Ayyah dan Allah ka cewa yayanka yayi haƙuri, ban sani bane”.

Cikin fahimtar cewa. Rayyern suka gani suke cewa yayanshi, ya ɗanyi murmushi cikin hikima yace.

“Ta ina kuka haɗu ina yake.

 Ni ya ɓace min ne nasan kuma shima ni yake nema yanzu”.

Da sauri Salman yace.

“Ikon Allah ta nan yayi, to amman ba zuwa za’ayi a ɗaukeku ba”.

Da sauri ya nufi inda Salman ya nuna mishi yana mai cewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button