Uncategorized

TUBALI Page 21 to 30

“Dan Allah kuzo ku nuna min inda yayin”.

Cikin nitsuwarta tace.

“Wani aiki mukazo yi nan Airport ɗin kai dai kawai kayi nan ɗin zaka ganshi.”

Salman ne ya ɗan harareta irin hararar da har yau bata gano manufarsaba,

Bayan Riyyam-nsra yabi tare da cewa.

“Na nawa kuma aikin yau dai ai mun rasa damar sai dai mubi mataki na gaba, kuma dan Allah fa yace so muje mu nuna mishi.”

Dole tabi bayansu.

Gaba ɗaya harabar wurin Airport parking din babushi babu alamarsa.

Kana sun dudduba gefe-gefen duk bashi, cike da gajiya da son komawa gida Jannart tace.

“Kai to ka tare taxi mana ya kaika gida”.

Dafa motarsu yayi tare da kwaɓe fuskarsa kana yace.

“Ai baƙone ni, mu baƙine daga Ethiopia, wani aikine Hamma na yazo yi, shine mukazo tare”.

“Toh ka kirashi a waya mana”.

Cewar Salman.

Dafe kai yayi tare da cewa.

“Toh ai dole sai na sai layin nan ƙasar taku nasa.

Shiru sukayi baki ɗayansu,

Can dai Jannart tace.

“Toh yanzu ya zakayi”.

Cikin danne tarin damuwarsa yace.

“Ku taimaka ku kaini na sayi layi.

Sannan sai in nemi masauƙi”.

Haka kuwa akayi Salman ya amince bayan sun kaishi, ya sayi sim card layin Mtn, yayi register.

Tuni lokacin biyar ta gota,

A hankali suka fito bakin shagon.

Cikin kula da alamun kallon akwai inda Salman ya sanshi yace.

“Toh ƙanina yanzu ina zakaje ne?”.

Jingina kansa yayi da jikin motar kasan cewar, CRV ce tanada tudu.

Idonsa ya lumshe tare da fara wassafo dajar shigar dake jikin Rayyern.

Kama daga Suit ɗinsa agogon hannunsa takalmansa zoben yatsarsa, uwa uba wayarsa.

Da kuma irin takardun da yaga yana ciccikewa da matsayin inda suka zauna.

Cikin sauƙe numfashi ya ɗago kansa tare da gamsuwa da tunaninsa yace.

“Ku taimaka ku kaini hotel mai kyau, wanda yake anguwar manyan mutane.

 In na isa na samu layi na ya hau zanyi mishi text ta Email ɗinsa”.

Da sauri Jannart tace.

“Toh ni dai Salman ka medani kafin ka kaishi.”

Murmushi Salman yayi tare da cewa.

“Toh ai sai mun wuce ta inda yake so ɗin ba yace unguwar manya ba, mu kaishi hotels ɗin Nasarawa GRA kawai”.

Juyowa tayi ta kalleshi kana tace.

“Uhum kafa san abubuwan wuraren tsada garesu ko, sannan kai kana ma da kuɗin ƙasar nanne?.”

Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.

“Yess ina dasu, nayi canji tun a ƙasata, kuma in ma bazasu isaba ai zasu amshi transfer ko?.”

Kai ta gyaɗa mishi tana kallon tarin kamanninsa da wanda tayi karo dashi.

Bayan sun shiga motar ne.

Baba Ado yaja.

Salman na gaba kusa da Baba Ado shi kuma yana gefenta.

Cikin hausarsa da bata isasshen inganci yace.

“Hotel mai kyaufa”.

Gyara zama Salman yayi tare da cewa.

“Kada ka damu. *Nasarawa GRA* itace unguwar da ta tara kaf manyan masu kudi na Kano,babu wani babban mai kudi ko ɗan siyasa na Kano da ya isa yake ji da kansa dama sauran jahohi da basu da gida a. Nasarawa GRA hatta Government House ma anan yake. 

 Sannan a cikin GRA din akwai manyan layuka da sunayensu 

*Lamiɗo Creasend* da kuma *Ahmadu Bello way* da kuma sauran ƙana nan layuka.

Kana akwai manyan Hotel’s din da suke Nassara GRA akwai *Tahir Guest Palace*

 da kuma *Ni’ima Hotel* da *Green Park* da *Liyafa Hotel* duk wadannan suna cikin Nasarawa GRA ne, kuma manya ne sosai ana ji da su suna da tsada da kuma kyau da inganci, zaka samu duk abinda kakeso a ciki.

Yanzu sai ka zaɓi wanne zan kaika, kaga dare ya fara yi mana.”

Numfashin ya ɗan sauke cikin jin daɗi da gamsuwa da bayanin unguwar da suka shigo ɗin, daga shiga unguwar kasan ta manya ce.

“Muje Taheer Guest palace hotel”.

Riyyam-nsra ya faɗi yana kallon gefen titin garin.

“To Alhamdulillah gashi ma mun kusa.

”Salman yace yana mai karya kwanan shiga layin da hotel ɗin yake.

Suna shiga bayan yayi parking, Suka sallameshi suka tafi.

Salman na cewa.

“To sai zuwa gobe zan kiraka in sha Allah inji ko ka gane ya’yan naka. Tunda na amshi number taka ta ƙasarmu”.

Toh yace tare dayi musu godiya.

Suna fita Suka nufi ma’aikatar su ta Arewa 24. Tafiya ce mai ɗan tazara tsakani.

Hakane yasa Baba Ado yake gudu.

Mintuna kaɗan suka isa.

Suna isa suka samu su Sunday a tsaye ƙiƙam to babu salla bare salati sai tsaron Jannart in wata tayi a biyasu makudan kud’in, da su kansu har yau basu gano manufar tsaron da ake bata, fiye da shi kanshi Alhaji Idi Sale Dakata’n ba, ko kanshi bai bawa wannan tsaron ba haka babban ɗan sa dasu Abdul, to ko dan ita macece shiyasa.

Cikin hikima Baba Ado yayi parking jikin motarsu.

Kana suka fita suka shiga cikin ma’aikatan jim kaɗan Jannart ta fito.

Suna ganin ta fito suka mara mata baya.

Tana shiga mota Baba Ado yaja.

Kana yaja suma sauran suka bishi a baya ganin. Yaja ɗin.

               *Dr Rayyern*

Wani Irin karkarwa ƙafarsa keyi, sosai yatsar ke fidda jini.

A haka ya tsaida ɗan taxi ya shiga, ba tare da yace komaiba, mai taxi ɗin yaja.

Bayan sun fita Airport ɗin sun miƙa hanyar cikin gari.

Kanshi ya jingina da jikin kujerar, wani irin masifeffen zafi yakeji zufa na tsastsafo mishi tako ina, sabida zogin da yatsarsa keyi, ga lips ɗinsa dake raɗaɗi kana ga zuciyarsa dake tafarfasa.

Sosai mai taxi ɗin ya dai-dai ta motar tasa bisa titi, a hankali yace.

“Sir ina muka nufa?”.

Shiru yayi tamkar bai jishi ba sabida zogin fashewan farcenshi da yatsarsa su suka buwayeshi.

Sai da ya kuma tambaya kana cikin taune lips ɗinsa yace.

“Nassarawa GRA”.

Toh yace kana yaci gaba da driving.

Tabbas da AC cikin motar amman bai gamsar dashi haka yasa yaketa haɗa zufa.

Suna shiga cikin tsakiyar anguwar Driver’n ya kuma juyowa ya ɗan kalleshi a hankali yace.

“Sir ta ina zamu ɓullo?”.

A takaice yace.

“Ahmadu Bello way”.

To ya Kuma cewa kana sukaci gaba da tafi kan kyakkyawan titin mai faɗi da wadatan tsabta.

Tafiya yakeyi a hankali.

Yanayi yana ɗan kallon tabka-tabkan gidajen dake shumfud’e na gani na faɗa tamkar abirnin India.

“Kayi hannun dama”. Dr Rayyern Mai-nasara ya faɗa mishi a hankali.

To yace tare da ratsa wa damanshi.

Wow yace lokacin da suka fito kan ɗan madaidacin titin, da wani irin tamfatsetsen gida mai tsananin kyau na al’farma yake forkon layin.

“Yayi tsaya a nan”. 

ya kuma tsinkayo muryar Dr.Rayyern.

Juyowa yayi ya kalleshi kana ya juyo ya kalli tamfatsetsen gidan, na al’farmar da in ya kintata nanne gidansu.

Cikin ransa yake tasbihi ga Allah.

Tare da juyowa ya kalli shi kana a mutunce yace.

“Mai gida in shigar da kai ciki mana, naga tun kan ka shiga yatsarka na zubda jini”.

Wani irin taɓe fuskarsa yayi,a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da haka, mutun ya shiga harkar sa, sam shi a tsarinsa babu ruwansa da shiga sabgar da bata shafeshi ba, sai dai kuma yana matuƙar son tausayawa sabida shi mai tausayine.

Cikin dakekkiyar murya yace.

“No ba matsala.

Bani da canji ko zaka bani Account number ɗinka inyi maka transfer’n in ba matsala?”.

Da sauri mai taxi yace.

“Okay Sir”.

Kana ya fara karanto mishi ac no ɗin.

Wata ƙaramar waya ya zaro a al’jihun rigarsa ta ɗaya gefen.

Ya ɗan lallatsa jim kaɗan ya medata al’jihun.

Cikin tsananin jin daɗi mai taxi ya kalli text ɗin Alert daya shigo masa na dubu ashirin. 

Cikin jin daɗi yace.

“Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya jiƙan iyaye”.

“Amin”. 

Yace kana ya sako ƙafarsa waje, a hankali ya takata.

“Shehyytt”. Ya ɗan fidda sautin sabida ƙafar tayi tsami, tuni yatsar ta kumbura.

Bayan ya fito ne kuma mai taxi ɗin yaja motar ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button