TUBALI Page 21 to 30
Shi kuwa Rayyern a hankali tare da d’an ɗingisa ƙafar tasa ya nufi bakin kekyawan gate ɗin.
Kan yatsarsa manuniya yasa ya ɗan ƙonƙosa jikin ƙofar.
Da sauri wani kekyawan buzu dake zaune bakin ƙofar ya miƙe tsaye, tare da zuwa ya ɗan tura wani abu, kana ya leƙa da ido ɗaya.
Da sauri ya meda abin ya rufe tare da sakin murmushi cikin tsananin jin daɗi ya ja ƙofar ya buɗe yana mai cewa.
“Masha Allah, Dr. ya dawo”.
Da sauri wani kekyawan matashi dake fitowa daga can cikin gidan cikin ya nufi baki gate ɗin cike da farin ciki.
Yana cewa.
“Alhamdulillah, Abba! Abba!!! Mamy ga Hamma Rayyern ya iso”.
Ya ƙare mgnar yana mai rungume Dr Rayyern da ya shigo.
Yayinda wasu mutanen suka taso da sauri suka iso garesu.
“Dakta Barka da isowa lfy”.
Shine abinda suke haɗa baki wurin faɗa da alamun shaƙuwa da so.
Duk da alamun akwai driver’ a ciki da kuma mai bawa fulawa ruwa sai kuma mai wankinsu da guga,
Sai Baba Mauɗo wannan buzun da alamun mai gadinsu ne, shi.
Wani ɗan guntun murmushi yayi tare dasa hannunshi ya shafa kan wannan kekyawan matashi daya amshi takardun hannunshi yace.
“I miss you so much my Ramadan”.
Kana ya bawa Baba Mauɗo hannu cikin kulawa da girmamawa tare dasu Ari sukayi musabaha.
Anutse yayi gaba Ramadan na biye dashi a baya.
Yayinda Su kuma suka koma wurin aikinsu, suna me farin cikin dawowar Dakta wanda yayi kusan mako huɗu baya nan.
Suna ratsa farfajiyar gidan da a ƙalla zai ɗauki motoci 7 zuwa 9 kuma ko wacce bazata matsi ko gogi ƴar uwarta ba.
Gaba ɗaya gidan zagaye yake da dogayen bishiyoyin na mijin gwanda, sai sirran Ayaba dake ƙasansu a jere da ƴan guntayen dabino.
Kana daga can baya kuma wani ɗan ma dai-dai-cin Garden ne mai masifar kyau, wanda yake cike da itatuwa da tsirrai masu sanyi da ƙamshi.
Kana daga farfajiyar gidan akwai wani baranda mai kyau da faɗi, wanda yake da steps.
Ata ƙasanshi gefen bishiyoyin an jera fararen kujerun silver hakama a ciki.
Kana tura ƙofar zaka riski wani hamshaƙin falo mai ɗan karen girma, Dan fadi da girmawa kuwa AC ma biyu ne aciki.
Ta gefen hagun falon gab da bakin ƙofar shigowa kuwa, wani ɗan madaidacin Bathroom ne.
Sai kuma gefen hagu, wani corridor ne mai fadi.
Kana shiga wurin zaka ga steps ɗin hawa sama masu faɗi.
Can gefen Bathroom din kuma ta gaba, wani kekkyawan Dinning area ne mai dauke da table mai kujeru takwas, sai wani Fridge mai suffar show glass Wanda ke cike maƙil da kayan sha.
Sai gefenshi kaɗan washing hand baby ne.
Kana ta kanshi ƙofar kitchine ne mai girma, wanda yake ƙawace da Kitchen cabinets and drawers masu masifar kyau, komai na ciki blue color and white ne.
Daga cikin kitchen din kuma ƙofar store ne.
Daga cikin store kuma akwai ƙofar baya, inda wasu igiyoyin shanya ke jere da kuma inda suke ajiye kamarsu dankali, doya, al’basa, da dai ire irensu.
Daga Kitchine din kuwa akwai wata ƙofar da zata ratsa ta cikin wani corridor, mai ɗauke da ɗan madaidacin falo mai 3 Bedroom,s and bathrooms. Sai ɗan Dinning area ƙarami.
Can gefen dama kuwa inda benen yake, kana hawa sama kan steps din, kana iya hango cikin falon ƙasa.
Tafiya kaɗan zakayi ka riski wani babban falo mai masifar kyau da tsaruwa.
Can gefe kuma wani kekkyawan Dinning table ne shirye cikin Dinning area mai sarƙafe da labule mai zirin-zirin igiyoyin dake sarƙafe da duwatsu masu daraja sheƙin Diamond.
Kana sai wani Fridge shima kamar show glass kana gefenshi kuma Show glass ɗinne mai shirye da cups, plates, spoons, mug’s da dai sauransu.
Sai Kitchen dake gefe da store kamar na falon ƙasa.
Kana sai Bedroom guda biyu, wanda basa kusa da juna dan a tsakanin su Dinning area da kitchen da store suke.
Akwai wata baranda mai kyau ta bayan ɗaya Bedroom ɗin inda nanne ɗakin Dr.Rayyern ɗayan kuma na Ramadan.
Ƙasan benen kuma akwai wata ƙofar wanda kana shiga zaka samu wani side ne kuma irin na saman sak, koman su iri ɗaya.
Sai can gefen kitchin ɗin falon ƙasan kuma akwai wani kofa wanda room and parlour ne mai kyau da Bathroom a ciki.
Daga gefe kuma can akwai ɗaki ɗaya inda masu aiki zata iya zama, amman bbu mai aikin a gidan.
Can waje kuma akwai BQ, Boys Quaters.
Gefen BQ ɗin kuma wani part ne mai kyau matsakaici a rufe yake su kansu Dr Rayyern da Ramadan Basu san menene a cikin wannan Part ɗin ba.
Tsarin gidan dai masha ALLAH.
Bisa wannan babban baranda mai steps biyar zuwa shida suka hau. Kana suka buɗe kofar babban falon.
Ramadan na mai kiran Abba! Abba!! Yana buɗe kofar suka hango Abba da Mamy, suna sauƙowa daga steps ɗin Dinning area, Wanda ta nan zasu fito side ɗinsu.
Wani kyakkyawan mutum ne mai matsakaicin shekaru, mai jini a jiki da tarin cikar haiba da kamala.
Ganin Rayyern dinne kuma yasa shi sakin wani irin yalwataccen murmushi, tare da buɗe hannayenshi dake cikin gariyar jikinsa.
Da sauri Dr Rayyern ya ƙarasa gabansa.
Rungumeshi yayi tsam a jikinsa tare da sauƙe ajiyan zuciya.
Mamy kuwa gefe ta zauna bisa kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, cikin haiba da tarin son ɗan nata tace.
“Babana wato Abba kawai kayi missing ko”.
Da sauri ya saki Abba yana murmushi mai cike da farin cikin ganinsu yace.
“Na isa Mamy, bakiji me bahaushe yace ba.”
Da sauri tace.
“Me yace”.
Ta ƙare mgnar tana yiwa Abba kallon tsokana.
Matsowa yayi kusa da ita, hannunta ya kamo ya ɗaura tsakiyar kanshi tare da yin ƙasa da murya yace.
“Uwa mafi uba koda uban sarki ne”.
Dariya mai cike da so tayi mishi.
Abba kuwa gefenta ya zauna tare da tsareshi da ido.
Ƙeyarshi ya ɗan sosa cikin sanyi yace.
“Abba bani ne na faɗa bafa, Malam bahaushe ne ya faɗa”.
Ramadan ne yayi murmushi yana mai jin daɗin, yaga Hamman nashi yana gaban iyayensu, dan nanne kaɗai zakaga fara’arsa ka kuma ji yayi doguwar mgn Especially in da Abba ne.
A hankali ya zauna gaban Abban nasu, tare da miƙar da ƙafarsa dake masifar mishi zogi.
Ita kuwa Mamy Dinning area ta nufa.
Plate ta ɗauƙa cikin show glass din, kana ta buɗe Fridge.
Chocolates da sweet ta cika cikin plate ɗin.
Kana ɗayan kuma tasa Apple da inibi. sai kuma goran ruwa da cup a ɗaya ta shiryasu, bisa tray’n kana ta nufo falon.
Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi, tare da zubawa ƙafarsa ido cikin mmki yace.
“Innalillahi Hamma Rayyern meya samu ƙafarka?”
A hankali ya miƙar da ƙafar tare da motsa ta.
Da sauri Mamy ta ƙasaro, Abba kuwa sunkuyowa yayi ya kama ƙafar cikin tashin hankali, ganin yadda yatsar ta haye ta kumbura ga jini har yanzu zuba yakeyi.
“Rayyern, meya sameka? Meya faru?”.
Yayi tambayar a rikice.
Kanshi ya ɗan sunkuyar ya kalli ƙafar tasa, kana a hankali yace.
“Wata mahaukaciya ce ta takani”.
Yayi mgnar cikin salonsa na rashin iya ƙarya.
“Wacece ita a ina kuka haɗu?”.
Abba ya kuma tambaya.
“Ban santaba, just kawai dai I know mental problem ce, kuma a Airport muka hadu.”
Ya bashi amsa, adan takai ce yana mai cije labb’ansa, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar kafar tanayi mishi zafi sosae.
Ramadan kuwa da sauri ya miƙe, ɗakinsa ya haura da sassarfa, dan ƙaramin akwatin taimakon gaggawa na likitoci ya ɗauko.
Yana sauƙowa ya zauna daɓas a gaban Dr.Rayyern ɗin, kamo ƙafar yayi tare da fara bashi taimakon gaggawa dan jinin ya tsaya.
Cikin mmki Ramadan yace.
“Sorry Hamma har nail dinka ya fashe, amma Mahaukaciya a airport how? then why akabarta ta shiga airport din?”