TUBALI Page 21 to 30

“Uhmmm” yace dan azaban zafin da yakeji.
Da sauri suka ɗago kansu baki ɗayansu.
Shi Dr.Rayyern TV dake like jikin ginin ya zubawa idanu.
Tamkar zai mannasu jikin fuskar kekyawan Dattijon nan Malam Mai-nasara da aka hasko a tashar Sunnah TV.
Ahankali ya janye ƙafarsa daga riƙon da Ramadan yayi mishi.
Tare da juyawa ya maida hankalinshi ga TV, yayinda shima Ramadan hakan yayi.
Abba da Mamy kuwa idanu suka zubawa Rayyern ɗin.
Wani irin kallo Abba yakeyi mishi mai cike da ma’anoni.
Cikin haɗe fuska yace.
“Kai Ramadan tashi ka kashe tv’n nan”.
Juyawa sukayi baki ɗayansu suna kallonshi.
Fuskarshi dake haɗe ne yasa Rayyern yin ƙasa da kanshi, cikin sassayan sauti murya can ƙasa yace.
“Please Abba kayi haƙuri wa’azinshi nada daɗi”.
Cikin tsawa yace.
“Ramadan kashe min TV nan”.
Da sauri Ramadan ya miƙe jiki na rawa ya kashe TV’n.
Shi kuwa Rayyern cikin wani irin rauni da biyayya, ga mahaifin nashi da bin umarnin shi da neman izininshi yace.
“Abba kayi haƙuri”.
Fuska a haɗe yace.
“Ramadan zokayi mishi aikin daya dace.
To yace kana yazo ya wonke mishi yatsar yayi mishi dreesing ɗin wurin da duk abinda ya kamata.
Yana gamawa magriba nayi.
Dole suka miƙe sukayi al’wala kana suka nufi masallaci.
Jannart kuwa.
A hankali ta kutsa kanta cikin falon nasu.
Tazo tsakiyar falon kekan tayi kiciɓis da…!
In sha Allah zuwa dare in na samu caji zakuga PAGE 6.
Littafin TUBALI na kuɗine .
By
*GARKUWAR FULANI*????????????????????????????????????????????
*TUBALI*
PAGE 6
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*FREE PAGE ne*
*Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki darinki biyar kacal in saki a ƙaramin group wanda bonus ne ga dana na, dan in na gama ya zama Complete 1k ne, saukine yanzu ga Masoyana, asalin kuɗi nai 1k ne, Special Group kuma su post nasu zaifi yawa. 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276. Kada ki bari garabasar ta wuceki, kice sai an gama, Hajia in kuma kinada zakuwa da turo 1k a saukake cikin makonni bibbiyu zamuke gama part-part*
Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki???????????? da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba’a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci????iya kudinka iya shagalinka????kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR)
Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza.
kada kubari abaku labari???? munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai???? da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR ????????????da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki.
Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm????????????????️????????
Da Yah Junaid, wani irin masifeffen tsorone ya rufeta wanda yasa ta fara ja da baya.
“Dan ubanki sai yanzu kika dawo? Ina kikaje kika tsaya? Tukun nama ƙarfe nawa ne ƙa’idar tashi aikinki?”
Ƙara matsota yayi tare da buga mata tsawa.
“Shegiya ƴar iska badake nake mgn bane kina jina kinyi shiruba”.
Cikin rawan murya tace.
“Uh uhm dama gidan Baba Kabir nake”.
Ta ƙare mgnar tana komawa gefen Mom da yanzu ta iso.
Cikin haɗe fuska tace.
“Yarinyar nanfa ba isasshen lfy ne da itaba”.
Juya kai yayi ya watsa mata wani irin masifeffen kallo tare da cewa.
“Toh uwar shisshigi”.
A hatsale Mom tace.
“Toh ubana, anyi Shisshigin aikin banza”.
Ta ƙare mgnar da kama hannun Jannart sukayi ciki.
Shi kuwa kwaffa yayi tare da bin bayan Abdul da yazo ya wuce su, bai ce musu ko ƙalaba.
Riyyam-nsra ne kwance bisa tattausan gadon ɗakin hotel ɗin daya kama.
Tuni yasa sim card ɗin sa na Mtn har ya zauna ras a wayar.
Kana yasa katin daya saya tun wurin sayan layin.
Mgn yakeyi da Mammy.
Yana mata bayanin haɗuwarsa da mutumin nan da suke kama.
Harma da haɗuwarsu da su Salman, kana ya ƙara da cewa.
“Mammy al’ummar Nigeria suna da kirki, suna da mutunci da mutunta baƙo, naga karamcinsu tun a cikin jirgi.
Mammy ina son su ina son ƙasar.”
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Yesssss! Riyyam akwai masu kirki, da amana da kawaici.
Amman kuma akwai maha’inta azzalumai macuta, ka kula da kanka kayi taka tsantsan.”
Cikin gamsuwa yace.
“Toh Mammy in sha Allah zan kula”.
Daga nan ta bawa Zayton sukayi ta hira yana mai gaya mata yadda ƙasar take.
Zaune suke a falon gidan Dr Lukman.
Cikin tawagarsu ta gamayyar kamfanonin jihar da kuma likitoci.
Dr Lukman keyi musu bayanin cewa.
“Dr Rayyern Mai-nasara ya dawo a yammacin yau, kuma Alhamdulillah dama akwai taron da gwamnatin jiha zatayi damu likitoci a gobe da safe, shine babban dalilin dawowarsa.
Toh muna tashi a taron zanyi ƙoƙarin tahowa dashi campany’n Alhaji Idi Sale Dakata, muyi taron jan ra’ayin nashi a can”.
Cikin gamsuwa sukace eh hakan yayi.
Kana sukaci gaba da tattaunawar.
Ab’angaren Dr Rayyern Mai-nasara kuwa, kusan atare suka shigo cikin gidan shida Abba da kuma Ramadan, wanda yanzunne dawowansu daga masallaci, domin koda suka yi sallah’n magriba basu fito daga cikin masallacin ba, har saida aka sallame salla’n Isha.
Kaitsaye cikin babban falon gidan suka nufa, Yayinda zuciyar kowannensu ke cike da sanyi da kuma salama, musamman ga yanda iska mai dadi ke kad’awa tana ratsa kowani hudan gashi na jikin d’an Adam mai rai.
Haka suka shigo falon Abba na gaba, sai Rayyern dake take masa baya, wanda yayi na k’arshen shigowa kuwa shine Ramadan, wanda yake d’an shafa screen d’in wayar dake rike a hannunsa.
Ganin shigowarsu ne kuma yasa Mamy dake, tsaye agaban had’add’en dining table d’insu wanda aka k’awatasa da wasu fitinannun royal chairs, ta saki sassanyar murmushin dake bayyana tsananin k’aunarta ga ahalin nata, murya asake tace.
“Masha Allah! Our dinner is ready.”
Jin hakan da sukayi dinne kuma yasa kasu sakin murmushi, tare da wuce wa dining area din kai tsaye.
Ramadan kuwa kulolin da Mamy ta miƙo kishi ya amsa dasu plate and spoos da gorunan ruwa mai sanyi.
Kana ya juya ya fita, dan kaiwa su Baba Mauɗo nasu abincin cikin kamala da mutuntaka ya kai musu kana ya dawo.
Shikuwa Rayyern da tun fitowarsu daga masallaci, yake tasbihi acikin zuciyarsa, kaitsaye gaban had’add’en fridge’n mai kaman show glass d’in dake dining area din ya nufa, yana isa kuwa ya bud’e murfin fridge’n, tare da d’ansa kansa ya zaro babban ledan chocolate na diary milk , wanda ya d’au sanyi sosai.
Maida murfin fridge’n yayi ya rufe, tare da juyowa ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun dining table d’in, wanda aka cika saman babban table d’in, da kayan cima kala kala, more especially fruits.
Ahankali ya b’are ledan, tare da kai chocolate d’in bakinsa.
Fitinannun idanunsa masu d’auke da long eye lashes ya lumshe, adaidai lokacin da yaji d’and’ano da kuma zak’in chocolate din ya mamaye harshen sa, wanda hakan yasa shi sake tura chocolate din abakinsa, tare da soma taunawa ahankali, yana maijin wani irin sanyi aransa, Tabbas aduk sanda yake cin abunda yakeso, yakanji wani irin gamsuwa na musamman, musamman madai duk wani abu mai zak’i, kwarai yanason zak’i sosai da sosai.


