MUTUM DA DUNIYARSA 10

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._*
*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[10…]_*
…………..Baje suke a falo su Kalil Na homework, yayinda Abba ke kallon labarai, hajia Hindu kam Ana zaune gefe ankashe kan d’auri Ana latsa waya da d’ora lemo.
“Lah Abba wannan tana Kama da Jiddahn gidan Umman gwammaja”. Hussain yafad’a idonsa a TV shima.
Ware ido sosai Abba ya kumayi, itama hajia hindu dasu kalifa duk suka kalli TV.
Wata Y’ar zabura Abba yayi dan mamaki, tabbas wannan Jiddah ce y’arsa, wato dayace kartaje saida taje kenan?. Baikai k’arshen tunaninsaba aka wuce rahoton taron dasu Jiddah sukayi.
Hajia Hindu cikin ta6e baki tace, “Itace kuwa Hussain, anje nunamana su masu addinine ko, ai tsoron ALLAH a zuci yake dai”.
Dariya Kalifa yay suna tafawa da Hassan tareda fad’in “Tab d’i, su ustaziya kenan”.
Dariya duk yaran sukayi har hajia Hindu, amma banda Abba da Munner dayay barci. Abba kam ransane a 6ace wai jiddah batabi Umarninsa ba, da ace dare baiyiba da yanzu sai yaje ya saukema Umma ta cikinsa kafin jiddah ta dawo yaci Ubanta.
Humm????????♀????.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Umma dai basusan wainar da ake toyawa ba, dansu ba kayan kallon ke garesuba, sai yau da yamma saiga Sadiq da majeed sunzo gidan (yaran uncle yahaya).
Da fara’a Umma ta taresu, hakama su Jiddah, walida da Sadiq Kansu d’aya, dan shekarun