UBAYD MALEEK 28

Ranki ya dade Inshallah allergy ne kawai Amma bana saka ran da…

Qin qarasawa yayi tareda dauko zancen itama jekadi kowane lokaci duk zasu farka lafiya Inshallah.

Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta na wasi wasin abinda yace na cewan allergies ne,

Wane irin allergy ne wannan me tsananin azaba.

Daga sama tajisa Yana qara saita murya yace”

Ranki ya dade idan na hali Dan Allah basai ‘yayan MALEEK sunsan meya faruba,kowama Dan Allah kada yasani sai maleek ya tashi anji daga garesa shida jekadin.

To” kawai tace tana kashe wayar cikin ‘yan tunane tunanen dasuke shigarta.

Kasa yin komai na breakfast tayi tabarwa Fana aikin ta wuce daki tashiga wanka tafito lokacin har afia tagama shirinta itama tahau shiri suna gamawa ko breakfast NURU batayiba afia ce kawai tayi suka wuce makaranta.

Tunda suka Isa NURU batada sukuni tunanin halinda yake ciki ya hadu da karatun exams dinta ya hargitsa Mata Kai har wani jiri jirin ciwon Kai takeji   sauqinta dayane daga yau tagama exams dinta hutun gaske zatayi kafin sudawo hutu inshallah sbd tana tsananin buqatar hakan.

****

Qarfe goma Sha ‘daya da mintuna shida maleek ya sauko ahankali yake tafiya cikin nutsuwa da kamewa Yana sanyeda jallabiya milk sai daukan ido takeyi sbd maiqo da laushin yadin jallabiyan.

Mr Omar dayake tsaye tuntuni Yana jiransa a palo yayi saurin sake sauke kansa cikin tsananin biyayya ya sake ja baya maleek ya wuce yabi bayansa cikin tsananin girmamawa yace”

Barka da fitowa MALEEK.

Allah yaqara lafiya da Nisan kwana tareda tabbataccen tsari da kariya.

Fitowa sukai suka nufi gym dinsa har lokacin Mr Omar na bayansa suna shiga a Dan qaramin palon dake ciki maleek ya zauna tareda Dan lumshe idanuwansa dasuke Dan nuna yayi rashin lafiya sbd sunyi haske sosai sun ‘dan fada sai hakan yayi kaman yaqara Masa kyan fuska.

Cikin nutsuwa Mr Omar ya matso daga bayansa yace”

MALEEK garin meriz ne jekadi ta farka tun dazu nayi magana da ita a dakin littafai ta tabbarminda…….shiru yayi tareda sauke Kai.

Dagowa maleek yayi batareda ya kallesaba yace”

Uhum…

Sake gyara tsayuwa mr Omar yayi Yana Dan gyaran murya a raunane yace”

Jinin mushrah ce tayi wannan aikin.

Alokacin ya dago manyan idanuwansa dasuka koma fararensu tas ya dorawa Mr Omar dayayi saurin yin qasa da Kai Yana cewa”

Afuwa MALEEK Amma tabbacen zancen kenan na duba shayin da jekadin ta gabatarmin tareda tabbacin zancenta na cewa tun a gizah taga abin zargi atattare da jinin mushrah din.

Shiru dakin ya dauka tsit na tsawon lokaci maleek baice komaiba 

Mr Omar Kuma jiran damar dazai cigaba da koro bayanin sauran zancen.

Ko motsi maleek yayi Mr Omar yasan manufarsa Dan haka shirun maleek din ya tabbar Masa da abinda zaiyi ya juya a nutse ya fita tsawon mintuna uku saigashi tareda jekadi da itakam ta zurma sosai ba laifi saidai jikinta lafiya kalau takejinsa Mr Omar ya rufe kofar ya qaraso yace”

MALEEK ayanda jekadi tayi bayani Babu sanin mushrah ko wani daga cikin ahalinsu gameda wannan aiki na ‘yar uwarta,

Akwai banbancin halaye da ra’ayoyi me girma a tsakaninsu Wanda Kai tsaye zamuce hassada kokuma rashin wayo yasa wani daga cikin gizah yake amfani da ita batareda tasaniba.

Kallon jekadi maleek yayi cikin nutsuwa da kamewar murya yace”

Inawa jekadi ya jiki tareda barka da arzikin samun lafiya.

Cikin girmamawa me girma tace”

Godiya nake maleek hakama jekadi nayi maka sannu da jiki.

Maleek kaman yanda kasani Babu inda wannan aiki yafito sai a gizah Kuma kamar koyaushe dai zarginmu Yana yawone akan mutane da yawa musamman idan mukai la’akari da bincikenmu damuketa fama a dunkule na rasuwar mahaifinka,

Tsawon shekarun Nan Danayi a delah naqi barowa nayi bin duk wani diddiqin sirri Babu wani alamar acan ko wanenen me wannan garin na meriz yake Amma yau bayan shekaru masu tsayi garin yasake bayyana Wanda hakan na nufin garin meriz a cikin delah gizah yake.

A Daren ranar dazamu zo cikin dare Naga abin zargi a sassan baquwar mushrah Amma sbd na tabbatar nashiga najata da wani zancen Kuma tabbas hancina ya shaqi kusan qamshin meriz Amma sbd tabbatarwa naqi magana sbd tasamu damar zuwa dashi anan mu tabbatar da hujja saidai banyi zaton zatayi tsaurin aikata abinda aka aikota dinba ayimin afuwa MALEEK.

Kuma kaman yanda Mr Omar yafada hassadace me qarfi a tsananin padime da mushrah wadda ta samo asali daga cigaban aure da mushrah tasamu na MALEEK Kuma haryanzu mushrah batasan da wannan halayen na ‘yar uwartaba Dan kuwa ko wannan zuwan nata inada tabbacin Babu alkhairi acikinsa sbd iyayensu takanas kaleeb yayi magana dasu bayan nayi Masa bayanin komai na ranar danaga mutum yafita daga sassanta Dan haka Ina me roqo da neman afuwan maleek akan kada yayi fushi da mushrah akan laifi mafi Muni da jininta ta aikata.

Tsit suka kumayi gabaki dayansu na tsawon lokaci maleek na nazartar abubuwa da dama acikin kansa wainda ba komai bane sai mutuwar mahaifinsa dayayi wato mutuwar azaba yanaji Yana gani duk da Yana yaro qarami lokacin Amma Yana iya tuno azabar dayaga mahaifinsa aciki,

Tun daga lokacin Basu sake ji ko ganin wani Abu daya danganci garin meriz ba sai yau sama da shekaru arbain kenan.

Tabbas zarginsu ya tabbata cewar a gizah kowanene yake Dan haka yanxu Kam aikinsu na gaske zai fara.

Dagowa yayi ya kalli Mr Omar dake jiran umarni ya maida idonuwansa kan jekadi Kai tsaye cikin kamewa yace”

Baza’a bari kowa yasan da zancenba ciki kuwa harda ita datayi aikin ki maidaita gizah idan tanacan ne za’a San waye shugaban aikin nata sbd na tabbatarda ita kanta nasan wa takewa aikiba sbd al’amarin me girmane bazasuyi saurin bayyanarda kansuba,

Amfanin wannan aikin na meriz da aka sata shine komawata gizah neman magani sbd sunyi tunanin acan ne kawai za’a samu maganin warkar Dani dagacan ne zasu qarasa niyarsu wadda baasantaba.

Gyada Kai jekadi tayi tace”

Kabar komai ahannuna kafin ka iso gizah Inshallah aikin yayi nisa 

Inshallah sai Allah yacika nufin kaleeb Dan kuwa alqawarine sai anciyar da dabbobin gizah Naman duk Wanda ko da ido yataba ganin garin meriz bare ya taba.

Mr Omar ne ya matso yace”

Jekadi sai magana ta gaba itace umarnin maleek ne kada mushrah tasan abinda yafaru sai lokaci yayi hakama iyayenta

Duk abinda tayi idan lokaci yayi zatafada musu dakanta aranar qarshe da Babu gyara.

Gyada Kai jekadi tayi tana sake yiwa MALEEK fatar samun lafiya ta miqe ta fice.

Mr Omar kuwa gyara tsayuwa yayi yana sauke Kai yace”

Maleek meye ainihin wannan hukuncin na jinin mushrah da aka sanarwa jekadi.

Jininta ta aikata kuskure babba na cutatar da ‘yar uwarta hassadarta tasa tasaka kanta cikin masifarda tun kafin mahaifinta yazama saurayi bare yayi auren haihuwarta.

Wayar kaleeb ya karba da Mr Omar ya miqo Masa bayan yagama yimasa bayanin komai dasuke ciki suka fara magana kowanne cikin kalar nasa ikon da kamewa ta sarautar dake jininsu kafin ya ajiye wayar.

Miqewa yayi tareda nufar kofa sai ya dakata ahankali batareda ya juyoba Kai tsaye yace”

Ka bawa jekadi muriz din damuke ajiya sbd bincike abisaga umarnin kaleeb kullum abata drop daya acikin abinsha ahaka har agama gano ainihin shugabanta duk tsanani kada abari asan muriz ake Bata sbd kaucewa basu alamar ansan dasu.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button