UBAYD MALEEK 28

Cikin jinjina Kai Mr Omar yace”
Yanda kaleeb yace shine daidai.
Fitowa sukayi suka nufo ciki Koda suka shigo direct sama maleek ya wuce kasancewar NURU batanan hakama afia yasa jekadi da kanta ta tsare kitchen harsaida Fana tayiwa maleek din breakfast aka jere Masa Mr Omar Kuma na daga bakin kofar Palo shima ya kafa ya tsare.
Padima datake jiran Jin mugun labari na kuka ya faru agidan taji Babu komai batajin motsin kowa alamun lafiya Amma duk da hakan qin fitowa tayi tanajin hankalinta Sam be kwantaba gabaki daya gizah takeson komawa ta karbi dukiyarta da tukuicinta na aikin da aka sakata da dasa tata cin sabuwar duniyar.
Sai yamma sosai su NURU suka dawo cikin farin ciki da walwala suke duk su dukan sbd Gama exams dasukai.
Wanka nuru tafarayi ta Sanya blue pencil jeans da farar _Gaultier_ top me hannun shimi ta fito a kicinma taci abinci tanason mgn da jekadi Amma Sam jekadin taqi Bata dama qarshema ce Mata tayi allergy ne Kamar yanda Mr Omar yafada Mata.
Padima Saida NURU tadawo tafito suna fira sama sama Dan takasa sakewa Kai tsaye tacewa NURU gida zata koma.
Da mamaki NURU ta kalleta zatayi mgn jekadi ta qaraso cikin girmamawa ta kalli NURUn tace”
An kammala maganin maleek.
Da wani irin farin ciki me tsanani data danne padima ta juyo ta kalli jekadin tanajin dukkanin damuwarta ta yaye kenan yasha tea din boyewa suke baida lafiya kenan.
Miqewa NURU tayi tabar gurin tana cewa”
Padima Ina zuwa.
Murmushi me Fadi jekadi tasakarwa padime tana cewa”
Ki huta lafiya jinin mushrah.
Cikin farin ciki padime tace”
Yawwa.
Dama tanason sanin halinda yake ciki duk da tasan yanzu ko kallo bazata samu daga maleek dinba Amma tanason tabbatarwada yasamu lafiyar Dan haka ta dauki tray din ta fito kenan ta hadu da farhat tana cewa”
Aunt NURU abincin daddy ne wanna?
Gyada Mata Kai kawai NURU tayi tana cewa’
Bari na aje anan ki jirani na sanyo jallabiya saimu Kai Masa.
Jekadi dake fitowa daga kicin ta matso gaban NURUn a natse tace”
Abincin maleek ba’a barinsa ako Ina shiyasa ko jiya yasamu allergy.
Kallon kanta tayi taga shigar Sam Bata daceba da zuwa gurinsa zatai magana jekadi ta sauke Kai tana cewa”
Afito lafiya.
Numfashi me sanyi ta sauke tareda daukan tray din tana satar kallon hanyar dakunansu tafara hawa saman sbd kada afia ta fito.
Tana shiga palon farko ta tsaya kofar palonsa na kurya tana sauke ajiyar zuciya sbd gabanta dake faduwa ta kalli farhat data bude kofar Kai tsaye ta shige tayi gurinsa da gudu Yana zaune kan royal kushin yayi crossing fararen qafafuwansa da Babu takalmi sai daukan ido suke kaman baya taka kasa dasu.
Shigowa tayi qafafunta na Dan rawa ta qaraso ta ajiye tray din kan table tana dagowa maleek dinma na waiwayowa yayi Mata kallo daya ya juya sbd kayan dake jikinta.
##MAMUH#