UBAYD MALEEK 33

NURU bayan tayi wanka sunyi breakfast tareda maleek ba sukasan baya gida suna gamawa tadawo Palo ta zauna tana Dan dudduba chats na wayarta bayan tagama waya da abal dinsu akan har lokacin su padima Bata isoba dayake tayi waya da jekadi akan sun Isa lafiya saita fada Masa sun Isa suna gizah padiman zata dawo idan suka huta a gizah aka sallameta da Haka suka bar zancen padiman suka danyi fira tsakaninta dasu aka Bata meryam sukai fira kafin ta kashe tashiga chats din.

Doorbell ne yayi qara tanaji ta Dan dago ta kalli kofar kafin taci gaba da chats dinta mum Sarah tazo ta bude 

Mr Omar ne mum Sarah tabashi hanya ya shigo ya nufo gurin NURUn cikin girmamawa ya tsaya tareda Dan dagowa yace”

Maleek daga office zamuyi tafiyan kwana biyu zuwa Los Angeles.

Dagowa tayi ta kallesa batareda ta iya cewa komaiba harsaida yakuma maimaita Mata kafin ta gyada Kai ahankali tace”

Allah yakai lafiya adawo lfy.

Idan kaje ka sanar zamuje saloon tareda afia.

Kamar wani munafuki Mr Omar din ya boye Dan guntun murmushinsa yayi gyaran murya yace”

Duk inda Zaki anbaki dama Banda zuwa asibiti.

Kallon Mr Omar din tayi fuskarta na sauyawa ga tarin mamakin shine yake Bata damar fitar ne kokuwa

ganin hakan yayi saurin seta murya yace’

Saqo ne daga maleek ranki ya dade.

Shiru tayi kafin ta gyada Kai tace”

Nagode shikenan Allah ya tsare.

Juyawa yayi ya fice mum Sarah tabisa ta rufe kofar Takoma kitchen gurin aikin dasukeyi.

Kasa chat dinma tayi ta ajiye wayar gabaki daya tareda Miqewa ta koma daki ta kwanta.

Baccin Rana tayi sai bayan dawowar farhat da dadewa ta farka ta tashi tayo alwala tafarayin sallah tukuna ta fito taci abinci kadan tadawo gurin Islamic class da ake zuwa anayiwa farhat din kullum ta zauna sunayi da ita.

Sai dare dasuka kwanta NURU tasamu tayi bacci daqyar sbd ‘yar damuwar datakeji hakanan kawai.

Washe gari fes ta tashi ranta ba damuwar komai sukai duk abinda zasuyi guraren karfe biyu suka fice zuwa inda zasuje Amma driver ne yake jansu.

Gurin shopping kayan make-ups da turaruka ta dauko ita saida sukaje bangaren kayan bacci suka daddauka set kaman yanda yawanci suka Saba me guda uku suda farhat saidai NURUn taqara da wasu wainda itama daqyar ta iya daurewa ta daukesu agaban afia din wadda takusa suman tsaye sbd mamaki da firgici Amma ta danne Bata nunawa NURUn ba sbd Bata tabbarda mezayi da irin wainnan sexy kayan baccinba wainda kwata kwata basa sakasu.

Daganan saloon suka tsaya acan suka Dade sai yamma lis suka dawo gida NURU na waya da abal dinsu cewan shi ko numbern padima baya samu tace Masa yabari zatakira jekadi taji meya Hana padiman komawa haryanxu.

##MAMUH#

**********

Ruwa farhat ta dauka a cup takai bakin NURUn cikin kulawa tana cewa”

Sorry Aunt.

Karban ruwan tayi takai bakinta Tasha bada yawaba ta ajiye cup din tana daukan Tissue ta goge Baki.

Kasa hakuri afia tayi sbd girman mamakinta ta kalli NURUn cikin son tabbatarwa da alamar tambayarta afili tace”

NURU menene matsalar?

Ina fatan dai ba maganata bane?

Kallonta NURU tayi tana ajiye Tissue din hannunta ta miqe tsaye idanuwanta kan afian cikin nutsuwarta tace”

Matsalar shine sarqewa nayi inacin abinci kila yawucin ba daidaiba.

Maganarki Kuma afia gabaki daya hankalina bayakai sbd ba hurumina bane Banda ikon saka kaina acikin maganarki da dad dinki.

Juyawa tayi tabar dining din ta nufi daki tashige tana Dan bubbuga kirjinta Dan har lokacin zafi yake Mata na sarkewarne koma na wani abin ne dabam batasaijin dadinsa.

Afia bayan tafiyan NURU sai alokacin yanda dad ya wuce Bai nuna yaji abin data fadaba kila baiji din bane Amma Kuma tanada shakka akan hakan Dan kuwa idan har yajita shareta yayi to tabbas zancen bamai karbuwa bane agaresa kenan sbd duk abinda yayiwa hakan Yana nufin Kar akuma kawo Masa maganar.

Jin tayi fargaba tashigeta sbd Koba komai yayi Mata gargadin sake tada maganar mum dinta cikin gidan Dan haka itadai bazata iya wannan tashin hankalinba kome mum zatayi bazata sake yiwa dad maganar ba.

Miqewa tayi tabar dining din ta nufi dakinsu Dan Kiran mum din saigashi tana shiga ta tadda NURUn kwance kan gado idanuwanta a lumshe sai takasa Kiran mum din tabari saita samu lokacinda Babu kowa akusa.

Qarasa shigowa tayi ta zauna kan sofa tana sake kallon NURU datayi shiru har lokacin idanuwanta a rufe ta nemi guri ta zauna tana tsirarwa kanta wani aikin da wayarta ranta dun a jagule.

NURU najinta Amma Bata bude idanuwanta ba saima numfashi data sauke tasake saukewa ahankali tana son bacci ya dauketa ko zata samu sararin Shan iska acikin kanta itama.

Da daddare bayan sungama cin abinci batareda MALEEK ba sbd har lokacin Bai dawoba kila basudai saniba suka koma daki afia tafara wanka tafito kafin ita dai Saida tayi sallar isha kafin tayi wankan tana fitowa ta Sanya riga da wando na bacci ta shafa body mist kawai ta fice zuwa dakin afia tana sake daurin gashinta dan Tasha iska gurin bacci.

Tana shiga ta taimakawa farhat tayi Shirin bacci suka kwanta bayan ta rage musu hasken wuta suna game a iPad sun Dade sunayi kafin bacci ya daukesu su duka.

Qarfe daya da mintuna goma Sha uku ya Murda kofar dakin ahankali cikin nutsuwa yashigo Dan duba farhat din sbd tafiya zaiyi gobe Kuma itace ba lafiyayya ba shiyasa yafi bada kulawa akanta.

Tunda ya bude yashigo yasan itama tana dakin sbd yaji qamshin _night alien,acqua di Parma_

Qarasowa yayi gadon ya tsaya akansu tareda zaunawa ahankali bakin gadon Yana kallon fuskarta kasancewar itace Baki farhat na kurya.

iPad din hannunta yazame ahankali tareda ajiyewa gefe ya janyo bargo ya gyara musu lullubinsu har zuwa kurji.

Fuskarta data juyo gefensa ya kalla zuwa wuyanta dake bayyane ya feso Masa kamshinta direct cikin hancinsa  sai dumin numfashinta dake sauka ai tsaye kan hannunsa ya rintse ido ya bude ahankali sukai ido biyu da ita qamshinsa daya cika hancinta ya farkar da ita saidai Bata motsaba idanuwan kawai ta zuba Masa.

Kallonta yake ta lumshe ido tasake budewa cikin yanayi na daukan hankali sbd bacci baccin dabai saketaba duka.

Hakan datayi yasashi hadiye wani Abu dayasa maqoshinsa yin sama yadawo qasa tana gani sai hakan yasata Jin tsananin kunya baccinta na sakinta gabaki daya ta motsa ahankali zata juya ya Dora hannunsa cikin wuyanta tareda tallafo fuskarta daf da tasa tayi saurin lumshe ido daga kallonsa numfashinta na sauyawa ta matso da kirjinta ya mannu da nasa sosai take ya sake zuba Mata idanuwansa yanakai dayan hannunsa cikin rigarta ya shafi cikinta dayasata dauke wuta take tana qanqamesa tareda sake mannuwa dashi.

Bude idanuwanta tayi ahankali har lokacin fararen idanuwansa na zube akanta fuskarsu na Dab data juna sosai Dan dogayen hancinsu gugar juna sukeyi duk numfashinsa daya da qamshin spraymintt na Baki take shaqa Ahankali ta bakinsu sukazo daf da juna har lokacin cikin idonta yake kallo idanuwansa na sake rurrusa kuzarin jikinta ta sake Masa gabaki daya cikin jikinsa tana matse dashi.

Kallon bakinsa dake daf da nata tayi sbd lips din kusan suna gugar juna ta lumshe ido tana tunowa a dakin farhat ne Kuma farhat na tashin dare Shan ruwa Dan haka zata iya tashi kowane lokaci Dan haka ta dago idanuwanta ta kallesa ta motsa zata bude Baki tayi magana bakinsu ya hade saijin farhat tayi tana Kiran sunanta cikin bacci.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button