UBAYD MALEEK 33

Wani irin mummunan sanyi jikinta yayi takasa dagowa ta kallesa hakama takasa fitowa daga jikinsa tanaji ya zameta tareda Miqewa ya fice batareda ya waiwayo ba tabi bayansa da kallo jikinta na sake mutuwa Dan bama zata iya tashiba yanzu daukowa farhat din ruwa kafafunta bazasu iya daukanta ba.
Tana kokarin tashi taji bude kofar dakin tana dagowa Yana aje Mata ruwan roba biyu agabanta ya juya ya fice mamaki na shirin shideta ta kalli ruwan da sauri tadago tasake kallon kofar daya fice mamakinta na sake ninninkuwa.
Da sauri ta dauki ruwan ta Dora kan jikinta saiga wani siririn murmushi ya sauka kan innocent face dinta tana waiwayawa ta kalli farhat da batama farka ba har lokacin wato dazun motsawane kawai tayi cikin bacci takira sunanta.
Bude ruwan tayi ta ‘dan Sha daya ta rufe ta ajiye har lokacin Dan boyayyan murmushinta Yana kan fuskarta ta zame ta kwanta tana lullubewa tareda rufe idanuwanta.
Washe gari sai 9 ta fito tana Yar miqa sbd tayi bacci me nutsuwa da qarfi ta nufi dakinsu ta shige Kai tsaye ta nufi toilet sai datayo brush tafito tazo gurin afia suna gaisawa tace”
Afia yaushe zakije siyayya akwai abubuwan danake buqata infact inason zuwa saloon yaushe zamuje?
Nima inason gyara kaina da qafafuna siyayya Kuma zanmana online shopping.
No banason online akwai abinda nakeso naje da kaina na siya dole sainaje da kaina.
Me kike buqatane?”afia ta fada tana zare dogon wandon baccinta Dan tubewa tashiga wanka.
Nighties Dina sun tsufa ina buqatan wasu and makeup stuff dai sai perfume danakeson sauya brand.
Ok Nima dai kusan duk buqatar dayace why not muje anjima.
No kikuma dai gobe ba.
Alright shikenan”afia tace tana qarasa cire kayanta ta nufi toilet tashige.
Bayan shigarta toilet din kenan wayarta tayi ringing NURU dake kusa ta dauki wayar zata daga tana dubawa taga sunan MUM baro baro akan wayar ta ajiye batareda ta daga din ba qarshema ta miqe ta fara gyara musu dakin tana kallo lailan nata Kira kusan ko bakwai kafin ta hkr zuciyarta na can na tafarfasa.
Wurgi da wayarta lailah tayi tana miqewa tsaye daga zaunen datake cikin bedroom dinta na qaton gidanta dake LA wanda zata Bari sbd hardashi duk ta rasa batason kowa ko duniya tafara sanin halinda take ciki shiyasa takeson lallabawa takomawa MALEEK batareda koshi yasan hakanba sbd mutane shegu sun nuna Mata wani abin Saida connection da zamanka wani sananne akeyi dakai,
Da farko farkon fitowarta kowa son huldar aiki yake da ita sbd zamanta da saninta Matar MALEEK UBAYD Amma tunda aka fara sanin sun rabu duk manya manyan mutanen datake taredasu sun janye sun nuna Mata sbd maleek ne wani abin shiyasa Dole yanzu Takoma Masa tunda dashi zata cigaba da amfana hartayi sunan da matsayin datake so Amma gashi wannan shashashar Yar tata da batada wayo tana Mata shirme sai ansan metake ciki gashi gidanta ma data saka acikin dukiyar Dan investment data shiga yashige ciki gashi bazata taba iya tambayar kowa kudi ba ayanzu sbd ba girmanta bane bazata taba Bari kowa yasaniba bare raini yashigo tana matsayin Matar maleek guda.
NURU bayan tayi wanka sunyi breakfast tareda maleek ba sukasan baya gida suna gamawa tadawo Palo ta zauna tana Dan dudduba chats na wayarta bayan tagama waya da abal dinsu akan har lokacin su padima Bata isoba dayake tayi waya da jekadi akan sun Isa lafiya saita fada Masa sun Isa suna gizah padiman zata dawo idan suka huta a gizah aka sallameta da Haka suka bar zancen padiman suka danyi fira tsakaninta dasu aka Bata meryam sukai fira kafin ta kashe tashiga chats din.
Doorbell ne yayi qara tanaji ta Dan dago ta kalli kofar kafin taci gaba da chats dinta mum Sarah tazo ta budeĀ
Mr Omar ne mum Sarah tabashi hanya ya shigo ya nufo gurin NURUn cikin girmamawa ya tsaya tareda Dan dagowa yace”
Maleek daga office zamuyi tafiyan kwana biyu zuwa Los Angeles.
Dagowa tayi ta kallesa batareda ta iya cewa komaiba harsaida yakuma maimaita Mata kafin ta gyada Kai ahankali tace”
Allah yakai lafiya adawo lfy.
Idan kaje ka sanar zamuje saloon tareda afia.
Kamar wani munafuki Mr Omar din ya boye Dan guntun murmushinsa yayi gyaran murya yace”
Duk inda Zaki anbaki dama Banda zuwa asibiti.
Kallon Mr Omar din tayi fuskarta na sauyawa ga tarin mamakin shine yake Bata damar fitar ne kokuwa
ganin hakan yayi saurin seta murya yace’
Saqo ne daga maleek ranki ya dade.
Shiru tayi kafin ta gyada Kai tace”
Nagode shikenan Allah ya tsare.
Juyawa yayi ya fice mum Sarah tabisa ta rufe kofar Takoma kitchen gurin aikin dasukeyi.
Kasa chat dinma tayi ta ajiye wayar gabaki daya tareda Miqewa ta koma daki ta kwanta.
Baccin Rana tayi sai bayan dawowar farhat da dadewa ta farka ta tashi tayo alwala tafarayin sallah tukuna ta fito taci abinci kadan tadawo gurin Islamic class da ake zuwa anayiwa farhat din kullum ta zauna sunayi da ita.
Sai dare dasuka kwanta NURU tasamu tayi bacci daqyar sbd ‘yar damuwar datakeji hakanan kawai.
Washe gari fes ta tashi ranta ba damuwar komai sukai duk abinda zasuyi guraren karfe biyu suka fice zuwa inda zasuje Amma driver ne yake jansu.
Gurin shopping kayan make-ups da turaruka ta dauko ita saida sukaje bangaren kayan bacci suka daddauka set kaman yanda yawanci suka Saba me guda uku suda farhat saidai NURUn taqara da wasu wainda itama daqyar ta iya daurewa ta daukesu agaban afia din wadda takusa suman tsaye sbd mamaki da firgici Amma ta danne Bata nunawa NURUn ba sbd Bata tabbarda mezayi da irin wainnan sexy kayan baccinba wainda kwata kwata basa sakasu.
Daganan saloon suka tsaya acan suka Dade sai yamma lis suka dawo gida NURU na waya da abal dinsu cewan shi ko numbern padima baya samu tace Masa yabari zatakira jekadi taji meya Hana padiman komawa haryanxu.
##MAMUH#