UBAYD MALEEK 34

Hakan data fada yasa NURU kallonta gabaki daya saidai har lokacin Bata ce komaiba kafin ta juya ta dauki kayanta tafara sanyawa lailah taqara harzuka sbd ganin Kamar NURUn ta maidata hauka kawai takeyi saita dauki towel din afia ta riqo hannun NURUn dashi tajawota ta fito da ita dakin tasawa dakin key ta zare ta kalli NURUn tana Dan yamutsa fuska tace”
Next time idan Ina mgn saiki saurareni da kyau,
Kije dakunan dake kusadana Sarah ki dauki daya wannan banason tarkace ko gwamutsetse atareda yarana ciwo zai iya shiga.
Wucewa tayi tabar NURU a tsaye daga ita sai towel tayi shiru batareda tace komaiba har lokacin sai kawai ta juya ta nufi dakin farhat tashige Allah yasa tanada wasu Kaya adakin na farhat saita Sanya duk Dana shan iska ne saita fito taje kicin ta dauko drink da biscuits tadawo daki taci tayi sallah ta haye gadon dakin tana juya wayarta tanason kiran jekadi Amma saita fasa ta ajiye wayar.
Sai yamma afia tadawo ta tararda dokar mum dinta ta girgiza matuqar gaske ta kalli mum din zatayi magana mum din tayi Mata wani kallo tana numa Mata kofa sbd batason dogon zance bare hayaniya.
Koda afia ta fito dakin farhat ta nufa Kai tsaye sbd tasan NURUn na can tana shiga ta taddasu zaune kan kujera suna game da farhat hankalinsu kwance suna dariyarsu.
Wani iri taji na rashin Jin Dadin abinda mum dinta tayi Amma bazata iya take maganartaba sbd duk yanda take kaunar NURU mum dinta mum dintace saita kasa shigowa ta juya zata wuce NURU data lura da ita kalleta tace”
Charger na kawai nake buqata a dakin sai laptop Dina.
Tsayawa afia tayi tareda juyowa ta kalli NURUn taga ba damuwar komai akan fuskarta ta dake itama tace”
Ok zan Aiko mum Sarah takawo miki.”tajuya ta tafi tabar gurin suka cigaba da abinda sukeyi zuciyar NURUn a dake Taki Bari abinda takeji ya rusata.
Koda dare yayi daqyar NURU ta iya rintsawa sbd dokokin lailan sunfara tsauri sbd ko dining din suna Gama cin abinci aka rufesa
Mum Sarah duk hankalinta ya tashi NURUn ta nuna Mata bakomai kadata damu Takoma daki ta kwanta.
Washe gari bayan tafiyar farhat school ma haka tashiga wani sabon cin zarafin ta daure dai Bata cewa komai bare ta tanka qarshe dai futa tayi taje restaurant taci abinci dagacan tace driver ya wuce da ita wani guri acan ta wuni sai qarfe bakwai tadawo gidan tana dawowa ta shige sbd komai na gidan da doka da iko sundawo qarqashin Lailah tadawo da duk qaidojinta da kaf masu aikin suka Santa dasu cikin kwana biyu ta dawo LAILAH MALEEK dinta Dan kuwa tani kowa yasake shiga taitayinsa.
NURU kuwa tsananin yafara Mata yawa Dan kuwa ko ruwan gidan Idan bana toilet ba batada ikon ganinsu bare tabawa Kullum tana daki idan taji yunwa ta fita taje taci abincinta qarshe dai abin duniya ya isheta sbd cin zarafi da ikon lailah yayi yawa Dan yanzu drivernma ta hanashi sake daukan NURU Dan Haka kwana biyu tana daki ga ciwon Mara tun jiya daya sakota gaba sai kawai ta sayi ticket din komawa gizah ta waya.
Tana kwance ciwon mararta yafara tsananta Mata ta tashi zaune riga da wandon baccin safene a jikinta qananu tun na safe Bata tashi tacireba tana dungule cikin gashi yau weekend ne farhat na gida duk taqara hanata sakat da hayaniyarta shiyasa duk Bata cikin nutsuwarta.
Tashi zaune tayi ta kalli farhat tace”
Farhat kije kifadawa mum Sarah takawomin tea me lemon.
Tashi farhat din tayi ta fita da gudu taje tafadawa mum Sarah ta jira Dan agama su taho dashi tana Taya mum Sarah fira.
Mum Sarah duk hankalinta ba kwanceba ta hadawa NURUn tea din tareda sabon cupcakes datayi yau da safen ta hado Mata a qaramin tray ta miqawa farhat din tana cewa”
Farhat ki riqe da kyau kije ki kaiwa aunt dinki kafin mum dinki tafito ko.
Karna farhat tayi ta fito tana tafiya ahankali sbd kada ya zube ta nufi hanyar Palo zuwa dakinta
tana kaiwa tsakiyar Palo sukai kicibis da mum dinta tafito cikin shigar Kuwait gown tana kamshi fuskarta taji kwalliyarta kamar ko yaushe sirrin kyau sai fita yake a fuskar.
Firgici da tsoro yasa farhat sake tray din ya zube Mata gabaki daya a qafa tasaki wani razanannan ihun da duk yasa kowa fitowa musamman NURU data qaraso daqyar da saurinta tayi kan farhat din ta kamota zata duba Lailah ta tareta da hannunta tareda turata baya cikin bacin Rai takalli su mum Sarah tace”
Tashin farko Wanda yayi wannan aikin da Wanda za’a kaiwa nakeson ji.
Tsit sukayi Wanda yasa ranta sake baci ta juyo ta kalli NURU dake kallonta wannan karon cikin qarewar hakurinta.
Tace”
Me kikeyi a dakin dakika fito?
Nace kibar dakin afia shine Kika koma na farhat kina tunanin cutar datasa na koroki daga dakin afia banawa farhat guduntane?
Sarah so nawa zanfada miki dokikina da tsarina acikin gidan Nan?
Kije dakin farhat Dana afia duk wani trash na yarinyar Nan akwasosu yanzu yanzun nan akaisu guestroom.
Dauke wuta dukkaninsu sukayi kowa yakasa motsi afia dataga abin na neman yawa ta matso gurin mum din tace”
Mum Dan Allah ki kyaleta tunda kin hanata zama dakina kince adaina Mata komai ko Bata komai
Mum harfa Edward kin hasa ya dauketa da mota yafita da ita
Mum Dan Allah kadaki kaita guestroom this is too disrespectful Koba komai Matar dad ce……wani lafiyayyan Mari ta saukewa afia dayasa dawowa cikakken hayyacinta na sanin mum dinsu tabbas tasamu matsala kila.
Cikin tsawar lailan tace”
Ki fito da kayanta yanzu Nan nace….
Gyaran murya mr Omar yayi daga bayansu dukkaninsu suka juyo kowa na dauke wutar Shiga firgici musamman afia data juyo gabaki daya gabanta da mugun harbawa
Su mum Sarah kuwa kowa rawar jiki ya dauka suna sauke kawunansu.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_????????????
_Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL_
_Dalaal–MISS XOXO_
_Mabudin zuciya–HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek–MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
********************Suna shigowa gidan farhat tafara tarbonsu da gudu ta fada jikin afia tana Dan bayyanarda tsoronta afili tace”
Afia mum tazo tana ciki tundaxu da kuka fita……
NURU data jefa qafarta Palo ta tsaya cak Jin abinda farhat tafada zuciyarta na dakatawa na ‘yan mintuna kafin ta daga fuska tana kallon cikin palon da Babu kowa ta danne tashigo tareda nufar dakinsu direct tana shiga ta sa sauke ajiyar zuciya ahankali tareda fitarda numfashi ta nufi table din dake
tsakiyar sofas din dakinsu ta ajiye shopping bags din hannunta ta zare qaramin gyalen dake kanta ta cire kayanta ta dauki towel ta nufi toilet tayo wankanta tareda alwala ta fito tashirya cikin riga da wando dogo marasa nauyi tazo ta tayarda sallah har lokacin afia Bata shigo dakinba.Saidata idar da sallah tayi adduointa ta miqe ta kwashi bags din tasaka cikin wardrobe ta dauki hula tasaka akanta ta fice zuwa kitchen neman abincin tana Dan Jin yunwa.