UBAYD MALEEK 40

Ayi aike gurin tsohuwar matar maleek lailah cewa nabata damar zuwa muyi mgn.

Allah yaqara ma girma da lafiya.”yakoob din yafada Yana yin baya baya ya juya ya fice.

Ta bangaren lailah kuwa yau ta samu damar Isa gurin hutawar neges Dan maganar aurenta da maleek data kawota har cikin palon akai Mata iso ta qaraso gabansa ta gaidashi cikin girmamawa kafin ta zauna cikin tata isar ta zamtowarta Matar asalin me mulkin
Take aka fara shigo da kayan marmari dasu Zuma da kayayyakin tabawa aka cike gurin tsab ta dago ta kalli kayan tareda dauke Kai sbd hakan tamkar cin fuskane ga maleek ace macen dake matsayin matarsa tana zaune gaban wani Wanda ba maleek ba har akawo Mata abinsha Dana ci Ana nufin taci gabansa wannan rashin darajar yayi yawa tana matsayin Matar maleek guda.

Numfashi ta sauke tareda waiwayowa ta kallesa Kai tsaye cikin tausasa harshe tace”

Allah ya taimaki neges me gizah ta yanxu ina maka barka da hutawa tareda barka da ganin wannan lokacin.

Kallonta yayi daka zaman hakimcen dayake ya Dan saki fuska wani murmushin dattijantaka na sauka kan fuskarsa yace”

Neges ya amsa Kuma Yana biki barka da fitowa medakin maleek na gizah.

Lailah tunda tashigo cikin zuriarsu take tsaye a wuyansa sbd mace ce me tsananin son mulki da Isa tareda kwadayin komai yazama Yana qarqashinta da ikonta Dan kuwa Jin take kamarma itace maleek din sbd sosai ikonta da gadararta ke bayyanarda mijintane me kujerar sosai take shigar Masa hanci Yana dannewa sbd taku da zamanta sirikarsa amma zai Bata darasi daidai da ajinta sbd ita takawo kanta gurinsa yanzu neman mafitar matsalarta da maleek.

Cikin nutsuwa da kulawa ya Dan juyo da Kai a kame yace”

Abu dayane akan matsalar aurenku da maleek shine karkata da hankalinsa yayi ta wani bangaren
Ma’ana wani Abu daya rinjayi tunaninsa akan iyalinsa.

Dagowa tayi cikin mamaki tace”

Akwai abinda ya rinjayesa kuwa bayan wannan auren da yayine…

Wani murmushin yakuma saki Yana cewa”

Mace bazata juyarda maleek ba ko wacece kuwa nafi sakaran wani Abu daban Wanda Banda sani akai Amma Dole saikin Saka ido kin bincika kin gano kafin asan inda gyaran zai faro.

Shiru tayi tana nazarin zancensa sbd Bai wani shigetaba zancen Dan kuwa duk me lafiya ya kalli al’amarin dakyau zai fahimci cewan Babu wani dalilin sauyawar maleek zallar halinsane rashin daukan reni ko kadan sai aure daya qara take hasaso wani abun daban Amma tunda yafadi hakan zata bincika tagani Dan a shirye take da maganin dukkanin abinda zai shata Mata layi da zamowa Matar maleek.

Batareda ya kalleta ba yasake Dora Mata tunanin bibiyar daddaqin abinda maleek ke tunani ta hanyar bibiyar jekadi sbd itace mafi amintar maleek a duk gizah da rayuwarsu bayan kaleeb da Mr Omar ko mahaifiyarsa Anneti batasan sirrinsaba sai wainnan mutanen uku.

Da wannan tunanin sosai lailah tasakawa jekadi ayar tambaya Dama tajima da sanin jekadi maqiyiyarta ce ba kauna atsakaninsu munafukartace kodan yanda tasamu cikakken bayanin jekadi itace tsaye akan komai na NURU a rayuwar maleek Dan Haka ta kanta zata fara saita rusa yardar dake tsakaninsu da maleek bayan tasan menene matsalar tukuna.

Bayan tabaro can sassan Anneti ta nufa akaiwa Anneti shelar isowarta tashigo cikin shigar alfarmarta kamar koyaushe ta zauna ta gaida Annetin Kamar dai yanda suka Saba cikin yanayi na Ni Matar neges nikuma Matar MALEEK Babu wata qarin Hira akai sbd Lailah har cikin ranta duk tsanarsu da qiyayyarsu takeji sbd sune munafukanta dasuka tsayawa NURU akan auren MALEEK Dan Haka Bata wani tsayaba ta wuce tabar Anneti da bin bayanta da kallon mamakinda baigama sakintaba saidai bazatani takan zancen lailah ba zata jira maleek yazo tana buqatan bayanin dawowan lailan.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button