UBAYD MALEEK 41

Faduwar da jekadi tayi ganin lailan ta nufi cikin da gudu yasata miqewa da sauri tana Kiran sunanta saidai kafin tayi wani yunkuri wani mummunan duka ya sauka akanta me tsananin azaba take ta sulale agurin ta zube a some jini na fita ta goshinta batareda taga Wanda yayi Mata dukan ba.
Lailah kuwa ganin mace a kwance cikin dakin cikin wani yanayi na Kamar majinyaci yasata takowa ahankali zuciyarta na harbawa cikin tsananin mamaki da tsoro ta iso har gabanta zata Kai hannu ta tabata padiman ta bude idanuwa ahankali baccin daya fara daukanta na sakinta ta zubawa lailah idanuwanta ahankali tana kallonta da mamaki Jin motsi abakin kofar shigowan yasa padima kallon bayan lailah mamakin ganinsa nasata kaikata Kai tana kallonsa dakyau ahankali ta bude Baki tace”
AMED????
Da sauri lailah ta juya zata waiwaya wani mugun duka ya sauka a tsakiyar kanta batareda ta waiwayo ba ta yanke jiki ta Fadi agurin sama sama tanajin padiman nasake maimaita amed har idanuwanta suka rufe numfashinta na daukewa.
******
Ruwan sanyin dake sauka kan fuskarta zuwa jikinta masu tsananin sanyi ya sanyata fara numfasawa tana motsa idanuwanta dasukai tsananin nauyi tafara budesu ahankali ahankali tana rufewa tana budewa sbd hasken dayayi Mata yawa harta budesu duka suka sauka kan mutanen dake zagaye da ita tafara Binsu da ido daya bayan daya kafin ta tsayar dasu akan fuskar maleek da yayi Mata kallo daya ya dauke Kai
Ta juyar da kanta gefe taga manyan jami’an tsaro tsatsaye agurin take ta zabura da sauri tana miqewa zaune tana sake kallon mutanen dake gurin ga qarin mamaki da firgicin ganin safiyace tas idanuwanta suka sauka kan mutum kwance miqe sambal anrufesa da farin kyalle har fuska Wanda ke nuni da gawar mutum ce,ta hadiye wani mugun yawu daga bakinta daya bushe kyam Nan take tana miqewa tsaye kanta na sarawa ta dafe kan tana Jin wani tashin hankali na shigarta sbd jekadi tasan tabari agurin jiyan da daddare bayan ta tureta, wani sabon tashin hankali da faduwar gaba me qarfi tashiga kardai wani Abu yasamu jekadi Dan dukan da turewar datai mata???
waiwaye waiwaye tafara tana neman rikicewa jikinta take yafara rawar tashin hankalinda Bata saka Masa ranaba ta nufi maleek da sauri tanajin ma ta wartsake daga ciwon da kanta keyi me tsanani ko gabanta Bata gani saidata Isa gaban maleek zatayi mgna idanuwanta suka sauka gefensa daya da jekadi ke tsaye sunkuye da Kai goshinta duk jini daga gani itama tana cikin tsananin tashin hankali
A haukace lailah ta waiwaya ta kalli gawar dake rufe agurin taji qafafunta na sagewa tayi baya zata Fadi macen dake sanye cikin uniform na hukumar qasar ta tareta tana riqeta dakyau da alamar dama ita ake jira.
Ta fizgo da qarfi tana kallon maleek bakinta na rawa cikin tsananin tashin hankali tace”
Wanene???
Me yake faruwa anan?
Kallo daya yayi Mata ya juya yana sauke siririn numfashi sbd gabaki daya al’amarin ya sauya acikin qanqanin lokacinda basuyi zatoba.
Kallon gawar padima yayi akaro na hudu Yana tunanin yanda ‘yar uwarta zata iya handling wannan mummunan al’amarin Sam an shammacesa a guri mafi mufi Dan kuwa yanzu acikin jekadi da lailah baisan wazai fara wankewaba duk da dukkanin shedu lailah suka nuna ita tayi kisan sbd baro baro jakadi ta fada cewar lailah ce tazo ta bugeta ta Suma itama lailan ta nuna hakan ta Yaya za’a fitarda lailah daga wannan ta bangare daya ta Yaya NURU zataji wannan mummunan labarin?
[ad_2]