UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 42

 ******************Kasa hakuri lailah tayi cikin sabuwar qaramar haukar dake Shirin kamata agurin take tafara kwacewa tana kallon maleek da sauran mutanen dake gurin cikin 

tsananin ihun dukkanin jikinta na rawa take cewa”

Meyasa zaku tafi Dani?

Bani nakashetaba wlh,

Dan Allah ki tsaya nayi muku bayanin abinda yafaru wlh tallahi bani bace

Dan girman Allah maleek kace su barni kasan bazan taba iya aikata wannan mummunan abin ba 

Ba halina bane,

Dan Allah ki sakeni wallahi bani bace ku tambayi jekadi Dan Allah maleek karka Bari su tafi Dani….

Tana ihun tashin hankali dukkanin jikinta Babu inda baya wani irin mazarin tashin hankali da ficewa hayyaci musamman data tabbatarda tabbas kisa akai Kuma 

itace ake nufin tayi kisar kenan kasheta za’ayi itama tabar duniya da ‘yayanta

Tunanin hakan ke saka haukatarda kwanyarta tafara fizgewa tana kokarin zuwa gurin maleek dake tsaye batareda ya dago ya kalletaba sbd kunyar hakan da baqin 

cikin hakan dake cinsa koba komai ita din uwar ‘yayansace matarsa ta farko wadda koman lalacewarta za’a kirata da matarsa ta farko har qarshen rayuwarsu.

Dayake har bakin kofar sassansa qatuwar baqar motar jami’an tsaron take suna Isa aka sanyata aka rufe tana wani irin kuka da neman ceto daga maleek tana 

rantsuwar ba ita din bace har muryarta tafara dishewa musamman daya zamto kallon karshene takewa koina Dan tasan hukun kisarta bazai dauki delay ba tunda 

komai a bayyane yake tasake sakin wani mahaukacin kuka tana buga kanta da tint windon motar da qarfi tana kuka tana Kiran sunan maleek cikin dukkanin bada 

imaninta ga shikadaine zai iya cetonta 

Haka aka janyo jekadi itama aka saka cikin motar aka rufe Kafin

Ja motar suka wuce sai alokacin maleek ya dago ya kalli Mr Omar dake tsaye a gefe tsaye kansa sunkuye cikin yanayi na tsananin jimami idanuwansa suka kada 

sukai jajir ya dago Yana kallo ‘yan motar asibitin dasuka Kira suka matso Dan daukar gawar su wuce da ita saiga shelar sanrwar tahowar NEGES da kansa zuwa 

sassan Dan tuni abinda yafaru ya karade gizah saidai Babu Wanda yasamu iko ko damar shigowa sassan hakama Babu Wanda yasamu masaniyar shin wanene aka kashen 

 daga jami’an tsaron da Mr Omar yakira sai motar asibitin da jami’an tsaron sukazo dasu Dan daukan gawar sai Anneti data iso sassan cikin tsananin tashin 

hankali tana zubda hawayen ganin wannan mummunar qaddararriyar ranar ace kisa acikin gizah Kuma daga sassan maleek qari da Dadi tsohuwar matarsa da 

jekadinsace cikinsu daya ya aikata wannan mummunan Abu me duniya zatayiwa MALEEK kallo?

Gashi Anki bude gawar bare asan wanene aka kashen.

Neges na zuwa cikin tsananin jimami da tashin hankalin wannan mummunan al’amarin ya kalli MALEEK Yana bayyanarda damuwarsa da rashin Jin dadinsa akan 

al’amarin yace”

Ina me jajanta maka wannan al’amari 

Saidai nayi maka alqawarin hukunta duk Wanda aka tabbatarda shine yayi kisan a tsakaninsu biyun Dan kuwa wannan al’amari babbane dazai iya tana darajarmu 

gabaki daya da ikonmu Dan Haka komai zai tafi abisaga adalci da doka wannan alqawarinane.

Sai alokacin maleek ya dago ya kallesa da idanuwansa dake bayyanarda zallar bacin Rai da wani irin zafi na iko da mulki dake yawo jininsa ahankali ya bude 

Baki cikin kamewa yace”

Godiya maleek yake Kuma Ina fatar zaka tuna wannan alqawarin naka Dan cikakkene jinin delas basa alwawarinda basa cikawa Ni nayi maka alqawarin tayaka cika 

wannan alqawarin za’a tafiyar da komai bisaga adalci da doka.

Jinjina Kai neges yayi Yana danne abinda yakeji gameda maleek din ya sassauta kallonsa zuwaga gawar da aka dauka za’a shigar ambulance ya waiwaya ya kalli 

yakoob Yana cewa”

A tabbatarda gawar kafin su tafi da ita.

Matsowa Mr Omar yayi Ya tarewa yakoob hanzari Yana sauke Kai cikin tsananin girmamawa ga neges Yana sassauta harshe da cewa”

Allah yaqarawa neges girma 

Ina neman afuwar rashin barin abude gawa irin wannan agabanka sbd darajarka fifitacciyace dabazai yiyu irin wannan abudeta a gabanka sbd dukkanin suturarta 

a yage take Wanda ya nuna alamar Tasha dama da makashinta kafin samun nasararsa 

Ni zanyi shedar tabbarda gawar aduk  lokacinda buqatan hakan ta taso agurin Sharia.

Cikin jinjinawa yace”

Shikenan hakan yayi Allah ya kyauta Amma duk da hakan Ana buqatan tabbarwan.

Matsawa mr Omar yayi tareda bawa yakoob hanya ya wuce Dan ya tabbatar din saidai Yana Kai hannun zai bude jami’an tsaron dasuke jiran ambulance su tafi tare 

suka dakatar dashi cikin yanayi na dokar aikinsu da girmamawa ga neges shugaban yace”

Allah yaqarawa neges girma Babu Wanda zai sake taba gawar Nan ayanxu sbd Babu abinda mukai bincike akansa zamuje da gawar lab muduba komai ayi aune aune 

daga lokacin ne bayan angama komai zamu bayar da gawar ayi Mata janaixa daganan ne kowa zai iya tabawa Amma yanxu muna bawa neges matuqar hkr 

Saidai idan hankalinka yafi kwanciya da kwakwariyar shedane zamu iya cewa tunda maleek yagani hakan zai gamsar da Kai.

Numfashi boyayye neges yasake Yana jinjina Kai tareda kallon maleek cikin yanayi na kulawa da damuwa yace”

Duk yanda za’a ayi kada abari media suji wannan mumman labarin ayi komai a sirrance tunda hukumarma a sirrance suka shigo suka fice.

Motar asibitin tafara wucewa daukeda gawar kafin akabar jamian tsaro uku da sauran securities din maleek a bakin sassan na maleek sbd shima Yana cikin 

wainda hukumar zata tsare sbd komai a qarqashin bangarensa yafaru Dan Haka an saka tsaro a sassansa babu inda zashi zai zauna aciki bame Shiga sai mr Omar 

kawai aka bawa dama shima abincin kawai zai ringa shiga dashi yafito sai zuwa headquarter aduk lokacinda aka buqaci ganinsa harsai antabbatarda cikin su 

biyun lailah ce ko jekadin ce tayi kisan.

Da hakan zancen yasake qamari hankalin jama’ar gizah yayi mumman tashi musamman Anneti tana tsananin buqatan ganinsa saidai ba dama Haka Takoma sashenta 

cikin tsananin tashin hankali da damuwa tana daga hankalinta da rokon Allah sassaucin wannan mummunan masifar har lailah take roqawa sassauci sbd ita uwace 

tasan wannan Abu wani babban al’amarine daga ubangiji kowa na neman doki daga garesa Dan Haka kowa zata rokar Masa.

Ta bangaren Mr Omar Yana fitowa gizah tareda maleek cikin sirrantacciyar mota sai motar jamian tsaro da securities dinsa fitowarsu gizah kenan ga tarin 

dibbin mamakinsu ‘yan media ne birjik suka yo kansu tareda zagaye motocinsu suna jeho tambayoyin dasuka kusan hargitsa tunaninsu su dukan Dan kuwa bayani ne 

akan cewa”

Shin me maleek zai iya cewa akan tsohuwar matarsa da jekadinsa dasuka taru suka kashe ‘yar uwar matarsa?????

Tsit sukayi dukkaninsu Mr Omar na dagowa ya kallesu kafin ya ‘dan waiwayo ya kalli MALEEK dake duba wayarsa hankalinsa kwance ya girgizawa Mr Omar din Kai 

take Mr Omar yabawa motar wuta sukai cikinsu da gudu sukaita kansu suna tsananta wutar al’amarin a social media da cewar tsohuwar matar UBAYD MALEEK M 

KALEEB tayi hadin gwiwa da jekadinsa gurin kashe yayar matarsa a Daren jiya.

Ganin yanda abin ke ruruwa Kamar wutar daji yasanya Mr Omar Kiran mum Sarah da gaggawa ya Bata umarnin duk wani Abu daya shafi kallon news ko wayoyin NURU 

da afia duk ta lalata kada tabari su samu news na abinda yake faruwa.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button