UBAYD MALEEK 42

Ta bangaren iyayensu nu NURUn kuwa Abu Kamar hadin Baki Koda gari ya waye labarin ya baza duniya babusu Babu Wanda yasan Ina suka bace bat a dare daya ga
‘yan kawo rahoto da ‘yan jaridu daketa yawon gidansu sunason ganawa dasu akan al’amarin Amma babusu sai hakan yaqarawa tashin al’amarin girma sbd take aka
fara kokarin Bata sunan MALEEK da cewar shine ya batarda iyayenta Dan boye laifin tsohuwar matarsa da jekadinsa.
Headquarter dasuka Isa wasu sabbin rubuce rubucen report aka shigar musamman akan ta Yaya ‘yan jaridu sukasan macece aka kashe Kuma Yar uwar matarsa sbd
Babu Wanda yasan gawar waye dagashi sai mr Omar ko jamian tsaro Kai tsaye ya hanasu duba gawar aka barta akan se Yan asibiti sungama nasu aikin tukuna
Kuma ‘yan asibitin ma mutum biyune Kuma a asibitinda Babu Wanda yasan da ita aka aikasu to tayaya zancen yafita zuwaga ‘yan media.
Suna dawowa gida ya shige sashensa ya zauna tareda sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rufe idanu ya bude ya kalli gefenda Mr Omar yake tsaye Kai tsaye
yace”
Kayi komai kaje da kanka ka taho dasu at any cost kada wannan labarin ya samesu harsai sun iso.
Dan dagowa Mr Omar yayi ya kalli MALEEK yace”
MALEEK anan din aikin Nan barinsa nada hadari.
Kaje komai Yana yanda ake son shi.
Angama Inshallah maleek.
Ficewa yayi Kai tsaye yakira Yana booking tickets Allah ya taimakesa washe gari da asuba jirjgin zai tafi Dan Haka Kai tsaye ya wuce ba wani delay.
Sai tsakiyar dare sosai ya Isa gidan Bai samu shigaba ta waya ya sanarda mum Sarah ta sanarda NURU da afia su shirya gizah zasu.
Da mamaki suka kalli juna lokacinsa mum Sarah ta sanar dasu saqon
NURU ta kalli wayarta da jiya ta wayi gari taganta a farfashe ta waiwaya ta kalli afia da tata ma tafi ta NURUn tashi aiki cikin sanyin murya tace”
Kina tunanin lafiya komai yake?
Sauke ajiyar zuciya afia tayi tana Dan duba agogo tace”
Inshallah lafiya.”tafada hakan ne Dan bawa kanta qwarin gwiwa da bama NURUn positive answer Amma tun jiya takejin kanta cikin tsananin damuwa musamman
dataga miscalls na mum dinta data kirata Bata kusa wayar na silent tunda ta karanta massage dinta taji tana kewar soyayyar uwa saidai Kuma zuciyarta na
tunatarda da ita amfani mum dinta keson Yi da ita kawai tunda take nemanta.
Babu wani dogon musu sukahau shiru tsaf suka shirya hankulansu a tashe Babu me nutsuwa daurewa kawai kowannensu keyi Dan qarfafa Dan uwansa.
Sai washe gari da asubar fari jirginsu ya daga suka wuce Basu isaba sai cikin tsakar dare har lokacin ‘yan jerida na daddabe boye a wajen masarautar gizah
suna jiran rahoto
Dayake Mr Omar yasani saida sukazo gate din Yan jaridar na tasowa yace driver yayi cikinsu da mota duk da hakan sama sama afia taji dayan na jeho tambayar
data sakata kallon waje da sauri inda Yan jaridar ke kokarin biyo motar askarawan securities din makeken gate din shiga masarautar suka taresu da sauri suka
koma maboyarsu suna jiran sa’a.
Afia jitayi tana gigicewa da abinda kunnuwanta suka ji cewar
Tsohuwar matar maleek tayi kisa
Kenan shine dalilin daukosu da gaggawa ba shiri?
Rawa jikinta yafarayi ta dago idanuwanta nacikowa da hawayen tashin hankali ta bude Baki zatayi magana daidai tsayawan motar bakin sashensu a fixge tasamu
damar fizgo maganar daqyar ta bakinta tace”
Mum tayi kisa?????
Da sauri NURU ta waiwayo ta kalleta gabanta na mummunan faduwa
Saidai ganin afian na kallon Mr Omar da idanuwanta da take sukai jajir yasa NURUn juyowa tana kallonsa da jiran amsarsa Dan kuwa take jikin NURUn yaso fin
na afia daukan rawa Dan kuwa a yanda tasan lailah kila maleek ne kawai Wanda zata iya kashewa sbd kishi da baqin cikin abinda yayi Mata batasan lokacinda
bakinta Yana rawaba ta furta”
Wa aka kashen???
Sauke Kai Mr Omar yayi cikin tsananin jimami da kasa fadar komai akan tambayoyinsu Wanda yasakasu tabbatarda maganar kenan Haka take abindaya faru kenan.
Take hawayen afia suka balle duk inda hankalinta yake Yana tsananin tashi
Mr Omar yayi saurin fitowa ya budewa afia kofa suka fito har NURUn tsabar rudewa ta manta da sashenta za’a qarasa da ita.
Afia tayi ciki da sauri ko gabanta Bata gani sbd tashin hankali wani takeson tambaya taji shin da gaskene kokuwa gizo maganar tayi Mata,
NURU kuwa sagewa dukkanin kafafuwanta sukai ta nufo cikin tana daga kafa daqyar farhat datai bacci saidai bayinda suke shigarda kayansu afian suka shigo da
ita
Tana shigowa palon daidai lokacinda baiwar da afia ta dakawa tsawa tana cewa”
Ki fadamun abinda ke faruwa a cikin delah gizah nace..””taqarasa fada cikin tsananin karajin daya tsorata baiwar a firgice tace”
Kisa akayi a…a..sassan MALEEK.
Innalillahi’wainna ilaihirrajiun” shine abinda afia tafara maimaitawa cikin tsananin fita hayyacinta tana girgiza Kai da sauri da sauri.
NURU kuwa Jin sunan maleek a maganar yasa jiri dibarta Saida mutum biyu sukai saurin tarota dama Mr Omar yasakasu kiranta Dan qarasawa da ita Bata masaukin
suka fito da ita ko ganin gabanta batayi sosai kokai dake aiki jikinta ya tsaya harta shiga mota aka ja Bata saniba,
Suna Isa bakin masaukinta mr Omar ya bude Mata kofar Motar
gabaki daya Bata lurada wani sashene aka kawota dabam ba asalin nataba Dan tafiyar kawai takeyi batasan inda take jefa qafa Haka Mr Omar ke bude Mata
kofofin palukan dasuke wucewa har zuwa na karshe daya bude ya dakata ta shige ya janyo kofar ya juya ya koma Yana ficewa daga sassan gabaki daya.
Hankalinta baya jikinta saidata takunta yafara nisa cikin palon taji iskar numfashinta ya sauya da qamshin dayake shiga hancinta ta dakata ahankali tareda
dagowa ta kalli inda take tana waiwayawa gefen damarta numfashinta saidaya kusa daukewa sbd bazatan yanayin datashiga ganinsa zaune kan kujera sanyeda
jallabiya brown fuskarsa na fidda wani irin zatin kwarjini Yana kallonta da fararen idanuwansa dake zube tas akanta…ta rufe ido ahankali ta bude ta
tabbatarda shi dinne
Zuciyarta da gangar jikinta sunkasa hakura ta nufesa da wani irin gudu dake bayyanarda dukkanin sirrin zuciyarta akansa idanuwanta na cikowa da hawaye,
Yana ganin hakan ya miqe tsaye ahankali daidai isowarta ta fada jikinsa yayi sama da ita kamar yarinya qarama Yana kallon idanuwanta da hawayenta suka
tsinke take suna gudu kan fuskarta ya sauketa tareda matseta jikinsa ahankali Yana kallon kyakkyawar fuskarta da fararen idanuwanta dake fidda hawaye sosai
Ya dauke gira daya Yana sake boyayyan murmushi tareda kamo fuskarta da tafin hannuwansa biyu Yana kallon cikin idanuwanta data dago ahankali tana kallonsa
itama har lokacin idanuwanta hawayen sun kasa tsayuwa
Ahankali ya matso da fuskarsa dab da tata yakai bakinsa kan kunnenta Saida ya sauke wani numfashin daya sanyata dauke wuta cikin sirrantacciyar muryar da
Bata taba jiba a hankali yace”
Kukan menene wannan??
Rintse idanuwa tayi da qarfi tana sake qanqamesa kirjinta na mannuwa da nashi yayi baya Ahankali Yana dafe kan kujerar dake bayansu Yana riko numfashinsa
dake neman sauyawa ya lumshe ido tareda budewa ya kallon idanuwanta zuwa hancinta dayayi ja sbd kukan datake
Ya zura hannunsa daya zuwa bayanta ya riqo qugunta Yana sake Kai bakinsa kan kunnenta can qasa yace”
Kina tsoron mutuwana ne??….