UBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK 42

Wani sirirn kuka ta fashe dashi Jin abindaya fada sbd har lokacin Bata gama fitowa da mummunan tashin hankalin tunanin rasashiba 

Ya kamo hannunta suka zauna Yana kallon fuskarta tareda tallafo fuskar da hannuwansa Yana cikin yanayi na kulawa yace”

Ok shikenan ya Isa haka,

Ban mutu ba,Babu abindaya sameni ok?.

Rungume kanta yayi Yana shafa bayanta ahankali Yana zuwa kanta hartagama kukan tafara sauke ajiyar zuciya sai alokacin shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya 

tareda lumshe fararen idanuwansa yanajin nutsuwa na shigarsa sbd kukan nata ya wargaza duk wata nustuwarsa dama tunanin komai.

Saidaya tabbatarda tadawo hayyacinta tagama samun nutsuwa ya dagota ya kalli fuskarta datai qasa da ita sai alokacin takejin kunyar kanta ta Dan juyar dakai 

tana Jin sanyi da nutsuwa na dawo Mata.

Hannunta cikin nashi suka nufi bedroom dinsa da komai ya nuna yakuma bayyanarda Nan din ne asalin turakar sarki Dan kuwa duk wani Abu dake tsare a dakin me 

adon zaibane(golden) sai makeken gadonsa dako rabinsa ya ishesu su biyun hadda saurama

Sai wasu dogayen labulayen windunansa dasukafi Kama da kofofi sbd girmansu ta waiwaya inda madubinsa yake ya cinye kusan Rabin bangon gefen dayake ta tsaya 

gaban madubin tana kallon kanta cikin nutsuwa da nazartar rayuwa sbd wato Babu Wanda yasan me ubangiji ya tanadarwa rayuwarsa agaba.

Ta cikin madubin suka kalli juna ta sauke kanta ahankali tana juyawa daga kallon madubin ta taka ahankali tabar gabansa ya riqo hannunta Yana dawowa da ita 

baya gabansa wannan karon kallo daya yayi Mata ya dauke Kai sbd kokarinsa kada ya tashi a banza Dan kallonta kawai na canja Masa tsarukansa da dama.

Zamewa tayi ahankali tareda nufar toilet dinsa tashige ta rufo kofa tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi tana rufe ido cikin sanyi tace”

NURU why did you loose your control¿

Ta Jima ahaka tana sauke numfashi harsaida tadawo nutsuwarta gabaki dayanta kafin ta zare kayanta ahankali ta daure gashinta tsakiya ta yanda bazai jiqeba 

tayo wanka ta janyo towel dinsa blue ta dauro ta fito.

Kwance tasamesa a tsakiyar gadon takasa kallon gefen ta nufi madubinsa turare kawai tashafa ta juyo tarasa abinyi sbd sallah takeson Yi 

Dole doguwar rigarta ta Dora kan towel din tayi sallolinta tana idarwa ta miqe ta zare rigar ta waiwaya takallesa a sace taga kaman yayi bacci saita sulalo 

ahankali ta hau gadon ta kwanta gefensa tana fuskantarsa ta zubawa kyakkyawar fuskarsa idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya a boye, ta gangaro da idanuwanta 

kan dogon hancinsa da duk farhat shi ta dauko

Ta lumshe idanuwanta lokacinda taji hannunsa na sauka jikinta ahankali ta cikin bargon dasuke rufe dashi 

Daga hakan Bai qare komaiba sukai bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button